NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 127 of 146

mata da quncin da harsu mutu bazasu manya dashi ba Maa sakinah tace ‘ABAAS GHAZ shine ‘da na karshe a jinin sarautar GHAZ data shafe a duniya gabaki daya yanzu, Shekaru masu yawan gaske ne da bazan tinaba suka Baro mu da asalin ANJOM GHAZ wato garin da mahaifin Abaas yake mulki, Abaas da Ayanah uwa daya uba daye suke tareda yan uwansu biyu da duka iyaye daya ne suka haifesu, AYANAH GHAZ itace babba sai ZUHRAH GHAZ sai NURAT GHAZ kafin ABAAS GHAZ…….. Ahankali tafara basa mummunan labarin rayuwarsu dayake cikeda baqin cikin da bai taba gogewa ba daga zuciyoyinsu,baqin cikin da dashi zasu mutu,baqin cikin da shine ya kawar da lafiyar kwakwalwa da gangar jikin Ayanaah,baqin cikin da shine zai zama abinda zasu mutu dashi,baqin cikin da har zuriar Bayan baya tasu Ayanah zasuyi baqin cikin jinsa har cikin jininsu,baqin cikin da a yanzu shine yake Neman raba Ayanah da rayuwarta…. Wani irin kuka takeyi mara sautin daya saka aleey daukan tissue ya miqa mata idanuwansa jajir hannuwansa na rawa zuciyarsa kaman zata fado hakama hawaye ne masu Zafin gaske suke Neman cikowa idanuwansa yanajin komai cikin zuciya da kirjinsa, Babban abinda yake sake saka jikinsa rawa shine yanda wannan mummunan tarihin zai isa kunnuwan LEUL, Yaya tarihin nan zai isa ga zuciyar datake shirye da mutuwa Akan wadda wannan mummunan tarihin yayi kaca kaca da rayuwarta? Tayaya zuciyarsa zata riski wannan tarihin kaddarar dayake dabaibaiye da rayuwar Amminsa. Numfashi Aleey ya sake saukewa yana kallan Maa yayi mata alkawarin zai Nemo Abaas a cikin qanqanin lokaci insha Allah hakama wannan tarihin LEUL ba a bakin kowa zaiji Saba insha Allah Sai a bakin Abaas da kansa. Ficewa Aleey yayi daga palon yana danna iPad dinsa sbd fara tattara kan bayanan daya riqe tsaf a cikin kansa na tarihin da abubuwan da zasu taimakawa bincikensa. Bedroom dinsa ya isa ya rufe yana Zaunawa kan sofa da table a gabansa ya bude laptop yana fara bi takan qasashen dake zagaye da BOYEM ta kowane bangare gabas yamma kudi da arewa. ******A Daren ko kadan aleey bai rintsa idanuwansa da kwakwalwansa ba saida ya hada wasu irin fitinannun bincike da bayanai har asuba, Sallar asuba yayi ya cigaba da hada kan bayanan sa da zai gabatarwa LEUL kuma yana saka ran ta hakan insha Allah Abaas kaman yana hannunsu ne. Karfe goma na safe NUAB ya fito a shirye cikin brown gucci wears da takarmin berluti brown suma fuskarsa fresh duk da yana cikin tsananin damuwa a kwanakin amma komai nasa yana nan daukan ido da girgiza zuciya yakeyi, Koda ya fito aleey yana tsaye shirye a palon hannunsa dauke da iPad fuskarsa sanye da farin glass da girmamawa ya yi masa Barka da fitowa yana bin bayansa zuwa dining inda aka cikeda tsaf da breakfast dinsa sbd yanzu da Amminsa take kwance ya Dena cin abinci acan. Zaunawa yayi a daidai lokacin shima aleey din ya zauna Bayan yayi serving nasa. Cikin nutsuwa sukai breakfast din suka kammala suka Baro dining din NUAB ya zauna Akan lafiyayyar 2seater Turkish royal cushion dake palon ya dago fararen idanuwansa masu daukan ido ya sauke Akan Aleey Wanda ya sauke ajiyan zuciya a natse ya matso ya bude iPad dinsa ya kamo bayanin dazai masa ya miqa masa a natse da girmamawa kafin ya dan ja baya kadan yana bude laptop din hannunsa daidai lokacinda NUAB ya bude abinda ya gama hada masa yafara bayani da cewa, ‘ANJOM GHAZ shine asalin garin da su Ammi suka fito, Safarar bayi ce ta fiddosu daga can zuwa nan Wanda a yanda Maa tayi bayani babu sunan qasar da suka sani Bayan anfito dasu zuwa nan din BOYEM, Abinda na tattara a bayaninta shine tace qasa goma sha shida aka wuto dasu ta ruwa kafin suka iso BOYEM, A bayanin nata su qasashe shidan nan bawai ta tabbatar bane amma a iya lissafinta tsayuwa goma Sha shida akai dasu Wanda hakan ya tabbatar mun da qasashe ne suke tsayawa kenan dan babu jirgin ruwa me girman da zai ringa tsayawa koina idan ba bodar wata qasar ya isoba, Zoomin map din daya hada yayi yana cigaba da cewa ‘Batasan sunan qasar da suka rabu da Abaas ba amma qasa biyu suka qara tsayawa Bayan rabuwarsu dashi a ta ukun ce suke isa inda aka saida su maana nan BOYEM kenan, A binciken dana tabbatar bisa ga wannan bayanin nata dama hada shima to qasar LARASIA aka siyar da Abaas Wanda idan muka duba qasa biyu ce tsakaninta da BOYEM dan hakan nake da tabbacin larasia dince inda aka siyar dashi.’ Wani bangaren Aleey ya sake zooming yana cigaba da cewa ‘Idan kuma na aka hada lissafin qasa goma sha shida dake akwai daga nan BOYEM ta gabas to Nahiyar qasar BASSHAH kenan idan kuma daga yamma ne qasa sha shida daga nan qasar ALSIYASH kenan, Idan kuma ta kudu ne qasar BUHARAQS kenan Hakama idan ta arewa ne to qasar ANTARIA kenan. Duka duka wannan bayanin dana hada qasashen nan sune inda zaa fara binciken nemansa amma dole duk qasar da zamu tafi Bayan sauka qasar sai an tafi bakin bodar ruwansu tanan ne dole zaa iya gane garuruwa masu kusa da manyan oceans da zaa iya samun tabbacin samun sa.
🏠