NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 126 of 146

kan tareda danne wa amma a wasu lokutan sirrin zuciya idanuwa ne suke nunawa. Halinda ya bayyana daga idanuwan sultan dayake Neman tona zuciyarsa ya lalata sanyin zuciyar dasu HAILE ke samu ga wannan ciwon lokacin daya dayake Neman kawar musu da Ayanah a cikin sauki. Duk yanda likitoci ke kokarinsu sunyi sun samu daidaita numfashinta dake samuwa da taimakon oxygen amma bata farfado ba Wanda kuma a abida suka gani ba lallai ta iya farfadowa yanzu ba bare dawowa daidai hakama abu biyune zai faru idan ta farka shine zata iya dawowa daidai harma da tinaninta da memories dinta data rasa hakama zata iya tashi kuma ba lafiya ba ta rasa Sauran hankali da memoryn daya rage mata Wanda zata manya komai hatta dan data Haifa da sultan da duk Wanda ta taba sani a rayuwarta dan haka abinda sukafi buqata a yanzu shine kada ta farka kusa kusa hakan zai bawa qwaqwalwarta daman samun ishashen hutun da batai aikin komaiba dan haka tinaninta da nutsuwarta zata fi Saurin dawowa cif cif insha Allah sabanin ta tashi da wuri hakan zai iya harbawa cikin kwakwalwan ta buga gabaki daya dan haka zasu hada da nasu taimakon dazai saka bazata farfado ba sai Bayan kaman wata daya haka indai so samu ne. Wannan bayanin ya karya tareda jijjiga duk wani kuzari da zuciyar NUAB ALMAZZ yake dashi dan kuwa Amminsa duniyarsa ce idan har zata iya tashi ta manta wanene shi da girman kaunar datake tsakanin jininsa da nata zai iya rasa kansa a wannan duniyar. Gabaki daya duniyar su aleey suma sai data jijjiga da wannan bayanin na likitoci dan haka Kai tsaye Aleey ya buqaci tattaunawa a tsakanin nasu likitocin dake qasashe daban daban dasu Dr Amed Wanda suka tattauna tattaunawa me tsayi kafin suka fahimci komai anan doctors dinsu suka tabbatar musu da bayanin su Dr Amed din haka yake a yanda suka fahimci kowane bayanin yanayinta da results nata. Wannan tabbacin da suka samu daga nasu doctors din ya saka suka shiga sabuwar zazzafan yanayi suna jiran abinda Allah zaiyi a farfado wan nata. Su sakinah da tenya duniyar tayi musu tsananin quncin da babu kowace irin walwala a rayuwarsu dan haka suka duqufa fadawa Allah sbd dawowan hankalinta da tinanin wata sabuwar masifar ce a rayuwarta da kowane irin baqin cikin data dandana zai dawo mata sabo fil. Sultan tsananin tsaro ya qarawa bangaren Ayanah din hakama shima NUAB Zafafan securities dinsa mata sun iso daga Moscow sune ciki da wajen bangaren Wanda a yanzu Bayan tenya da sakinah sai likitanta Dr Amed babu me shiga dakin datake idan ba NUAB din. Sultan bai taba zuwa dubata ba al’adar dake kansa matsayin shugaba dan haka zuciyar NUAB take sake tsananta akansa. A bangare daya kuwa Wani tsananin bincike aleey yakeyi me gigitarwa Akan Neman Abaas Wanda NUAB yayi alkawarin Nemowa kafin watan nan daya da ake saka ran tashin Amminsa ya cika dan kuwa a yadda likitocin sa suka basa tabbacin indai aka samu abinda zuciyarta tafi tsananin so ko maitarsa fiyeda komai a memory dinta na baya aka gabatar mata dashi tana farfadowa to hakan zai iya tabbatarda tsayuwar hankalinta da memories dinta. Hakan ya saka Kai tsaye ya bada umarnin duk inda Abaas yake a duniya yanason aleey ya qure lissafin kwakwalwansa Akan inda zaa fara nemansa. Wannan ya saka qwaqwalwan Aleey budewa da kyau ya nutsu ya buqaci ganawa da Wanda yasan Abaas a duniya Bayan Ammin. Kai tsaye Sakinah ce wadda zata basa bayanan dayake so dan haka a lokacinda ya zauna a palon da zai tattauna da Maa sakina dagowa yayi a natse ya kalleta da idanuwansa masu sirkin blue blue na asalin baturen Russia ya bude baki Bayan ya dauki iPad din dake hannunsa dan dauka da tattara duka bayanan da zatai masa ya dago yana nutsar da duka hankalinsa akanta yace ‘Maa’ Kallansa tayi a natse itama batareda ta bude bakiba sbd nauyin da bakin yayi mata na rayuwarsu dake dawo mata, ‘Maa,waye Abaas?? Ina Abaas yake? Bata yayi ko guduwa yayi kokuma korarsa akai? Idan bata yayi daga ina ya bata? Idan guduwa yayi daga ina ne ya gudun? Idan korarsa akai waye ya koresa,me yayi aka koresa? Meye cikakkiyar alaqar Abaas da Ammi? Shekara nawa yanzu da rabuwan Ammi da Abaas?’ Numfashi me nutsuwa ya sauke yana kallan Maa din Wadda idanuwanta sukai jajir ya sake tausasa muryansa yace ‘Maa,Maa duka wannan bayanan shine zai bani daman dawo da Abaas rayuwarku, Da wannan bayanin da zaki mun Maa nayi miki alkawarin Nemo Abaas matiqar yana raye insha Allah dan haka kowane bayaninki Maa ki sani yanada mahimmanci da rawar dazai taka a wannan aikin.’ Numfashi me Zafi da wasu hawaye masu Zafin gaske suka gangarowa Maa sakinah wadda Bayan shekaru masu tarin Yawa Ayau NUAB kila zaiji tarihin mahaifiyarsa da bai taba saniba mai daci da rashin dadin ji. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 61 A hankali cikin tsananin sanyi da mutuwar jikin radadin dayake dawo
🏠