NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 124 of 146

kiran NUAB dabai taba kaiwa wannan lokacin bai taho gareta ba hakama a saninta yace da safe zasu wuce amma gashi har rana tayi babushi Wanda hakan ya saka zuciyarta rasa sukuni hankalinta ya fara tashi da shiga firgici. Tana kokarin saka kiran Sakinah ta kalleta tareda saka hannu ta karbi wayar ta ajiye gefe ta kalleta tareda zama kujeran datake kusa da ita ta sauke Numfashi tana kallanta ta bude Baki zatai magana tenya da itace takeda alhakin isar da sakon ta kalli Ayanah data zuba musu ido zuciyarta na Wani irin nauyi tana jiran Jin abinda zasu fada ta katse sakinah da zubewa gaban Ayanah kanta na yin qasa sbd cike al’adar isar da sakon sultan ga wishimah dinsa ta bude Baki da murya me sauti dake yankar zuciyarta ga abinda zata fada tace ‘Allah ya qara miki lafiya da tsawon rai da zaki sheda aure da mulkin LEUL BOYEM NUAB ALMAZZ me BOYEM da Moscow, Allah ya qara miki girma da daraja wishmah uwar NUAB,Zakin BOYEM,Sarkin BOYEM,diamond din BOYEM, Ina fatan Allah ya bakin karfin zuciyar da zata karbi sako me daraja daga me daraja sultan me wishmah da LEUL NUAB ALMAZZ boyem wato sarki YASAR ALMAZ me boyem, A Daren jiyan sakon me daraja ya iso sultan mai boyem yace a miki albishirin ya maida miki martabarki ta wishimarsa ya maida miki karban kwananki a tirakarsa daga Daren jiyan Wanda Ayau zaki far……… Cikin wani irin sauti da basu taba ji ba a muryar NUAB da basu taba tsammanin ganinsa lokacinba kaman saukar aradu sukaji cikin nutsuwa yace ‘What? Maa? Sakinah ce ta dago jiki a matiqar sanyaye ta kalli kofar idanuwanta na sauyawa sbd Wani dandanon zallar daci da bacin rai tareda baqin ciki me tsananin gaske da suka jiyo a muryansa da idanuwansa dayake zarewa glass, Kafe idanuwansa yayi Akan Maa tenya din wadda ta sunkuyar da kanta zuciyarta na ‘daci itama dan basuyi farin ciki ko kadan da hakan ba amma ba yanda zatai dole ta isar da sakon sultan ga wishmah dinsa a darajance. Ayanah data dauke wuta a Zaune sbd kwakwalwanta data kasa digesting komai zuwa hankalinta dataji yana gushewa ta dago ta zubawa NUAB din idanuwanta dake sauyawa suka ja ahankali tareda tahowan wasu hawaye masu tsananin zafi a cikinsu ta miqe tsaye tana girgizata Kai da sauti me karfi tafara cewa ‘HAYATEEM Karka tafi Ka barni, Bazan iya zama idan Ka tafiba.. Kayi mun alkawarin tafiya dani inda zaka mu rayu acan tare, Sultan zai rabani dakai ne, Bazan iya rayuwa babu kaiba a kusa dani Hayateem, Hayateem kada Ka tafi Ka barni kaima, Baa ya tafi ya barni,Ammah ta tafi,Nurat ta tafi Zuhrah ta tafi Abaas ya tafi kaima zaka tafi Ka barni?? Wata irin rawa da fizga jikinta ya fara yi mai tsanani tana ja baya tana maganar da karfi idanuwana jajir bakinta na wata irin rawa. Mummunan tashi hankalin tenya da sakinah yayi suka miqe tsaye dukkaninsu suna kokarin nufarta tayi baya da karfi tana kafe idanuwanta Akan NUAB tana maganganun dake tada tsigar jikinsa gabaki daya idanunwansa na yin jajir sbd kallanta tana ficewa hayyacinta Akan idanuwansa yana gani mafi muni na rayuwarsa gabaki daya. Riqota yayi da sauri yana son bude Baki yayi magana amma Ayau Rauninsa yana Neman bayyana ‘Ya Ammi’ ya furta da Wani irin mataccen sautin daya saka gashin jikinsu tenya tashi suna dakatawa cak jiki mace. Riqota yayi jikinsa yana kokarin rungumeta amma gabaki daya fita takeyi hayyacinta tana ture sa da karfin gaske tana cewa mutuwa zatayi itama bazata iyaba kowa yabarta itama zata tafi batason zaman duniyar. Yanda taje maganganun koina jikinta yana fizga da jijjiga ya saka abinda yakeji yana tsananta a jininsa tareda Wani irin mutuwar jiki sbd bai taba ganin mahaifiyarsa a wannan yanayin ba dan haka ya rungumota jikinsa da karfi yana rungumeta ta fasa wani irin kuka me tsananin karfin gaske da tsima zuciya Wanda ya saka su Sakina sake shiga mummunan Halin tsoron dawowan tinaninta tin daga lokacinda ta fara ambatar sunayen ahalinta data bata taba ambata ba a lokaci daya tinda memory dinta ya samu matsala. Kukanta ya sakasa bude bakinsa da yayi mummunan nauyi shima nasa jikin kakkarwar yakeyi da sautin daya ratsata yace ‘Ammi bazan taba tafiya koina na Barik ba, Zan rayu guri daya dake kaman yanda nayi miki alkawari, Zan tafi dake insha Allah ko ba yanzu ba…… Rufe idanunwata tayi tana fasa sabon kukan dayake gigita nutsuwa da rikita jinin jikinsa tace ‘Idan Ka tafi mutuwa zanyi bazaka sake ganinaba Hayate….. ‘Ammi babu inda zan tafi na miki wannan alkawarin matiqar ba dake ba to Hayateem yana nan babu inda zai tafi wannan alkawarina ne gareki Ammi…… Girgiza Kai takeyi tana sake rikicewa sbd wannan Alkwarin dayake yana sake haukatar da kwakwalwanta ne sbd haka ya fada a farko zai tafi da ita amma yanzu a karo na biyu zai sake tafiya yabarta kaman yanda kowa ya barta dan haka kwakwalwanta tafara kokarin dawo mata da memories dinta sa suke buga kwakwalwan tata gangar jikinta fa lafiyarta na kasa dauka fizga tafara me tsananin gaske tana Wani irin Ihun da batasan ta
🏠