ba yasa sun tabbatarda akwai Sauran Wani abu koma menene a zuciyar NUAB gameda mahaifinsa dan ba dan hakan ba Ayau sultan YASAR bazai kwana da kansa Akan wuyansa ba batareda sun tabbatarda ya samu ganawa da malaikan daukan rai.
Duk wata jijiyar dake jikinsa sun fiffito fuskarsa da kunnuwansa sunyi jajir Wanda ke bayyanarda ba qaramar wuta ce take ci a jini da zuciyarsa ba dan kuwa zuciyarsa gap take da bindiga Akan abinda yake ji,
Duk yanda ya rayu cikin fushi da mahaifinsa Akan abinda yayi na rabasa da uwarsa bai taba dauka zuciyarsa takai maqurar matakin karshe na qinsa da mahaifiyarsa ba da har zai iya basa zabi biyu na abinda yasan babu Wanda zai taba yi a cikin biyu ?
Bazai taba karban mulkin BOYEM ba sbd qiyayyar BOYEM da duk Wanda yake cikinta dake zuciyarsa,
Hakama zabi na biyun bazai taba saka hannun yabar mahaifiyarsa a BOYEM ba bazai taba dawowa ba har karshen rayuwarsa,
Tayaya wannan mutumin zaiyi tinanin yabar mahaifiyarsa anan qasar yabar qasar har abada sbd kawai yana son ya karbi mulkin masarautar da bai taba shaawan zama magajinta bare sarkintaba,Masarautar data wulaqanta mahaifiyarsa,
Masarautar da bata taba daraja mahaifiyarsa ba.
Rintse jajayen idanuwansa yayi yana sake Jin fushin da bai taba Jin irinsa ba yana danne kirjinsa da numfashinsa ya bude bude ido yana dunqule hannuwansa biyu da suke wata irin rawar tsantsar bacin rai da baqin ciki me tsananin gaske.
Tsit bangaren nasa ya dauka harma da zagayensa dan kuwa niimar bangarorin duk Wanda yake jinin masarautar dumi ya dauka me karfin gaske sbd masifar da babu shiri data fadowa kowannensu a Daren.
A bangaren sultan shima a Zaunen kaman yanda duka iyalansa suke ya kwana zuciyarsa cikeda abubuwa daban daban da suke shirye da karban tsanar kowace iri daga NUAB da kowa ma matiqar zai Kai qure lambar fushi da Zafin kan NUAB ya sakasa karban mulkin Masarautar dayake shirye da sauka ako Yaushe dan kawai ya Dora sa akai Wanda saiyayi hakan zai samu nutsuwa da sukunin dabai samu irinsa ba tinda ya hau mulkin.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
59
Koda safiyar garin ta waye kowa dake cikin ahalin da ciwon Kai masu tsanani suka ringa tashi dashi tareda ciwon rai shima me tsananin gaske ga wainda suka samu rintsa wa baccin kenan ga wainda basu rintsa ba kuwa kaman wainda suka kwana gadin gawa haka suka tashi da idanuwa kaman baqin china.
NUAB ALMAZZ da duk Wanda yake bangarensa cikin Yaransa kaf babu Wanda ko gifta masa bacci yayi a ido,
Dan haka Koda ya fito sallar asuba sukai sallah a tare daga nan geamin suka shiga dakin da aka tsara masa dan hakan suka fara geamin har lokacin suna iya ganin fushinsa da bacin ransa bai gama sauka ba dan haka a kiyaye da shirye da kowane shirin suke hakama kaman yanda baice komai gameda tafiyarsu datake a ranarba babu Wanda ya tada maganar sbd a shirye suke da qarasa rayuwarsu anan matiqar baice ga ranar da zaa wuce ba su a inda ya zabi rayuwa acan tasu rayuwar take suma dan haka bangaren tsit yake babu wulgawan kowane bawan da baa nan yake aikin hidimar NUAB ba Wanda ko ruwan shansa basu cika barin kowa na basa ba idan ba su din ba sbd tsaro.
Tenya da Maa sakinah kuwa tinda garin ya waye suke juya yanda zasu isar da sakon sultan ga Ayanah wadda ta tashi da tsananin kulafucin son ganin NUAB sbd tafiyarsa da zaiyi a ranar ya tafi da ita dasu sakinah dan haka Ayau din ma koda bayinta suka gama hada mata ruwan wanka tana tsaye jiran su gama tayi ta shirya dan kuwa haka take Jin tsananin kewan Abaas Wanda a zuciyarta tana barin masarautar take ganin zata hadu dasu.
Karfe tara na safe Ayanah ta gama dukkanin shirinta tana Zaune tana jiran NUAB Wanda ya kasa zuwa inda take dan baisan tayaya zai iya kallanta ba ya sanar mata ya daga tafiyar tasu data saka aranta sosai,
Shi kansa tsoron Wani ciwon ya sameta ko jikinta ya rikice ya saka ya rasa ta yaya zai kalleta,
A Karan farko rayuwarsa da Wani ya sakasa a matsatsen yanayin da komai nasa ya tsaya cak batareda ya kaddamar da danyen hukuncin akansa ba,
Maganar data shafi mahaifiyarsa tafi masa business deal din billions na dollars a rayuwarsa,
Akan lamarin da duk ya shafi mahaifiyarsa baya masa garaje hakanne ya saka sultan yakeson ya quntata masa ta hanyar bullo masa ya nuna masa karfin ikonsa dayake kanta shima.
Karfe sha daya da rabi ya shirya cikin black fendi wears da black geometric shape glasses na tom ford qamshinsa na tashi a hankali ya fito ya tinkari bangaren mahaifiyarsa Aleey na gefensa yana waya a natse shima Akan Wani business dinsu Yaransa biyu ne a bayansa da umbrella sai bayi kusan goma a can Bayan yaran nasa da suke bayin da aikinsu basa Rakiya da tsaro na cikin masarautar Wanda Sarkin bayi ne ya tanadar masa su masu karfin gaske ya aiko a matsayin bayinsa.
Ko kafin ya iso a daidai wannan lokacin Ayanah ta dauko wayarta zata saka