NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 122 of 146

n yake shirin yi na maida wishmah matsayinta a dare guda batareda tsammanin kowaba, Tayaya macen da suke son ‘dan tawayen ‘danta ya tattarata ya tafi da ita ko su aika masa ita sama zaa ce an maida mata matsayinta dayake tabbatarwa duniya ita din cikakkiyar ikon da mallakar sultan ce. Wani nauyi kirjinta ya ta jefar da wayarta a kujeran dake dakin tana fasa kiran likita ta bude Baki kaman zuciyarta zatai aman wuta tace ‘Yanayin Mamee baa buqatan likita baqin ciki ne da dacin zuciya zata dawo daidai zuwa anjima idan ta samu sassauci’ Tana gama fadar hakan a koma kan kujeran ta zauna tana dafe goshinta dayake mata nauyi sbd ciwon Kai da bacin ran dayake cinta, Shiru sukai dukkaninsu kowa da yanda baqin cikinsa yake cin zuciya da kirjinsa, Meryam da aka aikawa mameen ba lafiya Kai tsaye tana zuwa taji abinda ya faru shiru tayi batareda tace komaiba ta jiya ta koma sbd batada abin fada hakama karfinta da lafiyarta Neman qarewa sukeyi a gurin dawainiya sa dakon baqin ciki da ritirin zuciya kullum Wanda a yanzu kam ta fara gajiya gangar jikinta ta fara gazawa ga daukan wannan baqin cikin da baida ranar qarewa bata fatar ta mutu a cikinsa batareda ta dandana farin ciki da kwanciyan hankalin gidan aure da tara zuria ba. ******Tenya kuwa a tsaye take qyam kan kafafunta tinda wannan sakon ya iso mata Wanda kwakwalwan kanta itama ta kasa dauka sbd babu ta yanda zaayi ace Bayan shekaru masu yawa da yafe wishmah daga zuciya da shimfidarsa rana tsaka dare daya yace ya dawo da ita a Daren da suke kallan Daren karshe na rayuwarsu a masarautar, A Daren da suke jiran gari ya waye masa su bar komai anan suje su shimfida sabuwar rayuwa, Shin sultan ya San da shirin tafiyarsu ne a goben daya yanke wannan hukuncin daya girgiza zukatansu dama duk Wanda zaiji cikakkiyar sanarwar zuwa da safe, A wane Hali NUAB zai tsinci wannan mummunan labarin ga kunnuwa da zuciyarsa sbd hakan da sultan yayi Baro Baro yana nuni da Hana cikar burin NUAB ne yayi ta hanya me sauki se karfi dan kuwa koda NUAB yake ‘danta Wanda yafi kusanci da ikonta Akan kowa zamtowanta wishmah din ubansa kuma maidata cikakken matsayinta ya kere kowace irin dama da ikon da ‘danta yake dashi akanta. Zufa ne a tsiyayo mata ahankali yana gangarowa daga gefen goshinta ta zame ahankali ta zauna gefen sakinah datai mutuwar Zaune itama idanuwanta jajir dan kuwa matiqar wannan mummunan sakon ya isa kunnan NUAB wutar tsanar mahaifinsa datake ransa ce zata sake hauhawa sbd tafiya da mahaifiyarsa bazai taba yiyuwaba gashi a yanzu datake cikin tsananin shauqin danta matiqar ya tafi yabarta batareda ya cika mata alkawarin tafiya da itaba komai zai iya faruwa da ita dan haka akwai tashin hankali a cikin wannan lamarin daya sauka a dare daya tamkar saukar aradu. Kasa isarwa da Ayanah sakon sukai dukkaninsu sbd basusan tayaya kwakwalwanta zata karbi sakon ba hakama basu saniba ko sakon ya isa kunnuwan NUAB shima basusan yaya zai amsa sakonba dan haka tamkar sakon mutuwa sakon ya zamewa kowane ba gangaren harda na maraki wadda itama daga sama taji sakon ya saukar mata kamar tsawa sbd ta Riga ta dauka ta sakawa zuciyarta sultan ya gama da wishmah kenan har karshen rayuwarta, Ko HAILE da zuriarta sun dauka ya gama da ita ya rufe babinta har qarshen rayuwarsa Shiyasa komai Yazo musu a mummunan bazata da gigita. Kowane bangare a cikin bangaren uku na matan nasa tsit ya dauka babu bangaren da ba a cikin dacin zuciya da mutuwar jiki me tsanani suke ba tareda fargaba dan kuwa abu ne dayazo babu shirinda zasu San yaya zasu tarbesa ba. Dare sake nutsuwa yakeyi Wanda ya saka tenya da suke Zaune zasuyi kwanan Zaune miqewa tayi shirin kaiwa sultan ziyara dan isar da rokon alfarmar da zasu buqata. Tareda bayi hudu ta isa bangaren sultan din ta isarwa da kadir roko da sassaucin da wishmah take nema daga sultan Akan zuwanta Ayau Yazo ba shiri sultan yayi mata Afuwan karbanta a gobe ba yau din ba sbd yanzu haka ta jima da bacci sbd yanayin jikinta. Kadir bai jima sosai a ciki ba gurin isar da sakon ya fito da sakon rokonsu ya karbu Ayau sultan ya mata Afuwa zuwa goben ta dawo cikakkiyar macensa wishmah dinsa. Da sanyin jiki tenya tayi godia da girmamawa ta juya ta bar gurin tana komawa bangarensu kowa yayi dakinsa cikin jimamin yanda zasu iya sanar da Ayanah a gobe ta Koma wishmah dinta bazata taba iya bin ‘danta ba sedai shi idan zai zauna Masarautar tareda ita. ********A daidai wannan lokacin NUAB yana tsaye tsakiyar palonsa idanuwansa jajir sunyi Wani irin jan daya saka gabaki daya Yaransa sunkuyar da kansu suna tsaye Jere a kofar palon babu me ikon cewa komai ko tambayar komai sbd fushi da wutar dake ci a idanuwan LEUL dinsu sun tabbatarda mahaifinsa ne kadai a duniyar nan ya isa ya tabasa haka batareda sun shiga ba amma wannan fadan ba gurin shigarsu bane amma dukda mahaifinsa ne yana cewa suyi Wani abin tsaf zasuyi batareda tsayawa komaiba dan haka Ayau da suke ganin fushi da tsananin bacin ran da basu taba ganiba a tattare dashi
🏠