NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 121 of 146

ultan yayi yana sake daukan cup dinsa yakai bakinsa ya dago ya kalli kadir dayake tsaye Wanda take ya juya ya dauko wasu takardu a cikin file biyu me kyau da tsari Yazo ya ajiye gaban NUAB kan table din gabansa ya juya ya koma gefe. Sultan ne ya kalli files din kafin ya dago ya kalli NUAB din ya sake sakin nutsatsen murmushi me kyau yace ‘LEUL NUAB ALMAZZ me boyem kanada zabi guda biyu anan Wanda nasan zaka iya sbd mahaifiyarka, Kallan files din NUAB yayi zuciyarsa na Wani irin tafarfasa da kaunar da har jikinsa ya nuna sbd Wani irin ja fuskarsa da hannuwansa sukeyi, ‘Zabi biyu ne a gabanka, Na hannun dama takarda nada sabon sultan dazai mulki BOYEM ne datake dauke da sunanka kanta saka hannu a cikinta gobe zaa fitarwa da Masarauta da duniya ita a matsayin sabon sultan dazai fara mulki a gobe Wanda hakan zai Baka damar samun cikakken iko Akan mahaifiyarka harma da mahaifinka da baka buqata, Ta hannun Hagun kuwa takarda ce da zata fita a gobe itama idan Ka saka mata hannu cewan har abada kabar BOYEM da mahaifiyarka harsai ranar da Allah ya dauki raina…. Zabi na gareka me BOYEM da Moscow. Idan akwai abinda yafi tafarfasan jini shine yake faruwa da NUAB Wanda dukkanin jikinsa ke wata irin rawa koina nasa nayin ja idanuwansa na kafe Akan sultan Wanda shima shi din yake kalla zuciyarsa a shirye da karban duk zabin da NUAB din zaiyi a cikin biyun. Yanda jikin NUAB din ke wata irin rawa da fizgar wutar dake ci a jini da kansa da kirjinsa ya saka yayi shiru batareda yace komaiba kuma bai dauke idanuwansa daga kan sultan dayake wa Wani irin kallan tsanar datafi duk wadda ya taba yi masa a baya ba ta yau din kokarin buga zuciyarsa takeyi dan miqewa yayi ya juya yabar palon idanuwansa kaman zasu fara feshin wuta sbd fushin da bai taba shigaba rayuwarsa. Yana fitowa su aleey suka sha jinin jikinsu taje suka bi bayansa a qame batareda cewa komaiba. NUAB na ficewa sultan shima take ya aika wa tenya sako a cikin Daren cewan Ayi sanarwar a Daren nan ya maida mata matsayinta na komawa zuwa kwana tiraka daga yau dinnan. Sakon na isarwa tenya mummunan shock ta shiga Wanda y sakata mutuwar tsaye, HAILE data fito a Daren itama cikin shirin zuwa tirakar kwana tama fitowa aka Dakatar da ita da sakon hakan Wanda ya sakata mutuwar tsaye kafafunta na kasa daukanta. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 58 Jiri me karfin gaske ne ya dibi HAILE wadda idanuwanta suke kokarin juyewa sbd dishi dishin da suke gani tsabar mummunan bugawan da kirjinta yayi tareda shock na babu tsammani, Fetto ce tayi saurin riqeta cikeda tashin hankalin da baa saka masa rana ba itama dan kuwa kaman kunnuwansu basu ji musu da kyau Dagowa fetto tayi ta kalli jakadiyar sakon wadda ke tsaye da bayi biyu a bayanta kansu a qasa cikeda girmamawa ta zuba musu ido bakinta na nauyin rasa ta inda zata fara jeho tambayar ta bude Baki a dan rikice tace ‘Maimaita sakon’ Cikin girmamawa bayin suka sake zubewa qasa Banda jakadiyar sakon data sauke kanta qasa cikin tsananin girmamawa ta sake maimaita sakon Wanda ya qarasa wargaza kuzarin HAILE ta Nemi zubewa jikin fetto kowace jijiyar jikinta jinin cikinta na katsewa kanta yayi nauyi sbd wata irin sarawa da yayi. Cikin sauri da kokarin sirrinta yanayin Hailen fetto tace masu kawo sakon su wuce ita kuka Kama Hailen tayi suka juya tareda Sauran bayin dake bayansu kowa kafafunsa a nauyaye sbd jinin uwargidansu dake tafarfasa duniyar bangaren tana daukan zafi gabaki dayanta. Suna isa Kai tsaye har bedroom dinta fetto ta kaita ta kwantar tareda fitowa take ta aika bangaren Aslam Akan a kira likita a turo sa queen haile na buqatarsa. Aslam na samun sakon ta fito ta nufo bangaren mahaifiyar tata sbd ganin meya sameta kokuma idan Wani abin ne ya faru dan kuwa tasan tabarta da shirin tafiya gurin sultan. Tana isowa ta tarar da ko magana Mamee din bata iya yi kirjinta ke tsananin ciwo da zafi sosai idanuwanta sunyi jajir ajiyan zuciya kawai takeyi me Zafi da karfi akai akai bakinta baya iya furta komai. Kallan fetto Aslam din tayi ta tambayeta meya samu mameen Bayanin komai fetto tayi mata Wanda ya saka Aslam din juyowa ta kalli mahaifiyarta itama idanuwanta na sauyawa zuciyarta tayi dum tama rasa abin fada sbd alamu na sake tabbatarda masifu da ranakun baqin cikinsu zasu bude su fara ne matiqar NUAB na nan dan kuwa dasu da bokayen su sun tabbatarda shine matsalar datake tsakaninsu da dukkanin Buri,nutsuwa,kwanciyan hankali da farin cikinsu da suke buqatar kawar wa matiqar suna son rayuwa da wainnan abubuwan. Shekara sama da ashirin rabon sultan da Wishmarsa, Ya rufe ya shafe babinta a rayuwarsa da shimfidarsa kaman yanda kowa da Masarautar suka rufe shafinta a cikin matan sultan, Wace masifar ce take Neman kunno Kai da a cikin Daren nan wannan mummunan sakon zai bayyana? Me sulta
🏠