abari ba dan haka su kawai ma barin NUAB da Yaransa suke so a masarautar ya koma inda ya fito masarautar bata buqatarsa hakama halayensa sun gama bayyanarda babuta yanda zaayi yayi mulkin qasa gabaki daya dan zai iya ringa bayyanarda tsiraicin jikinsa ga duniya ne Bayan yana matsayin sultan dan haka Sam babu ta inda zaa basa mulkin BOYEM.
Shi kansa Wani irin yanayi ne me Zafi da radadin kuruciyarsa dayake taso masa yakeji na haduwan da zaiyi da mutumin dayake matsayin ubansa amma yayi watsi dashi tinda qananun shekaru ya jefa sa duniyar da babu kowa da zai rayu dashi a cikinsa, ya kuma rabasa da mahaifiyarsa batareda tausayin halinda take ciki ba har tsawon shekaru….
Numfashi me dumi ya sauke mara sauti a lokacinda yake tsaye gaban mirror din dayake closet dinsa tukuna Kai tsaye ya wuce bathroom dan wanka,
Mintina ya dauka gurin wankan kafin ya fito daure da towel gashina na tsiyayar da ruwa a hankali.
Wani towel din ya saka a kansa qarami yana goge gashinsa dashi kafin ya iso gaban dresser ya tsaya.
Shirin mintin kusan talatin yayi kafin ya gama ya fito a lokacin 10 na dare tana gap da yi dan haka yana fitowa Kai tsaye bangaren sultan ya nufa cikin nutsuwa da Izzarsa.
Suna isa tin daga nesa masu tsaran kofar suka wangale masa kofar kansu a qasa cikeda girmawa suna masa Barka da zuwa da zallar ladabi.
Shima kadir dayake kofar a tsaye yana gadin isowansa dan tarbansa rissinawa yayi yana masa Barka da zuwa cikin girmamawa me girman gaske kafin ya basa hanya ya wuce shikuma yana gabansa dan yi masa iso har inda sultan yake Zaune cikin palon sa dayake hutawa na alfarma koina qamshinsa da sanyin ac ne ya kame ya riqe.
Su aleey a kofar suka tsaya dukkaninsu a natse sha hayaniya,
Palo biyu suka wuce kafin suka isa asalin palon dayake din yana Zaune cikin shigarsa ta hutawa tamkar ba dattijin daya manyanta sosai ba yana sanye da ash Riga da wando masu kauri da tsadan gaske da sukaiwa jikinsa kyau kwarjinsa ya cike gurin kaman yanda qamshinsa ya cike gurin.
Sako kan NUAB a cikin shigar datake kusan iri daya data sultan nasa qamshin a hankali yana gauraye gurin yana kokarin doke na sultan din sanyin nutsuwa a zuciya,
Dagowa sultan yayi yana Dora fararen idanuwansa akansa yana kallansa cikeda nutsuwa da kaunar da ba damar nunawa sbd wutar dayake gani a idanuwan NUAB din ta fushin da ba yanzu zai sauko ba shima baya buqatan ya sauko din yanzu harsai ya tirsasa karban abinda yakeson ya karba,
Kwarjini da nutsuwan kyan NUAB cike idanuwan sultan sukai kaman yanda nasa kwarjini yake kokarin shiga lafiyayyun idanuwan LEUL me BOYEM daya daukesu daga kallan mahaifin nasa yana isowa cikeda nutsuwa da izza tareda kamewa ya zauna a kujeran dake facing sultan din ya dago fararen idanunwansa ya kallesa yana yaqar wutar datake cin zuciyarsa ya bude Baki a taqaice da kamewa yace
‘Barka da wannan lokaci me BOYEM’
Numfashi me sanyi da dan murmushi sultan ya sake yana sake kafe idanuwansa Akan NUAB din Wanda shima dagowa yayi da idonsa masu razana maza ya bude Baki cikeda nasa mulkin da izaa yace
‘Barka da isowan magajin me boyem LEUL NUAB ALMAZZ,
Batareda bata lokaci ba menene dalilin son ganina??
Qarasa fada yayi yana komawa sultan dinsa sak cikeda ikon mulki ba wata sakin Fuska,
Shima NUAB din baida lokacin batawa a maganar ya dago ya kallesa Kai tsaye yace
‘Zan bar BOYEM a karo na biyu kuma wannan Karan tafiya ta har abada Wadda zanyita ne tareda mahaifiyata wadda banajin tanada Sauran amfani a masarautar…’
Qarasa maganar yayi yana dagowa ya zubawa sultan idanunwansa da suka bayyana da kyau fes Akan fuskar sultan din.
Cup din hot green tea din dayake hannunsa yana hayaqi sultan yayi yana jingina bayansa a natse hankali kwance kafin ya kalli NUAB din dakyau har lokacin hankalinsa kwance ba alamar ko mamaki a tattare dashi,
Bude bakinsa yayi da cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali yace
‘Nine datake a qarqashina zan sanar idan ma batada amfanin amma ba Kai da kake baqo ba a masarautar da rayuwarta ba……
Wani irin kallo NUAB yayi masa maganarsa na sukar zuciyarsa baice komaiba idanunwansa na dan sauyawa.
Cigaba da magana sultan yayi da cewa
‘NUAB ALMAZZ mahaifiyar Ayanah ghaz ta haramta gareka da kowa ma duniya Bayan ni daga ranar data zama wishmah ko yayanta basada iko da ita saini,
Wannan shine abinda Baka gama fahimta ba inaga,
Ayanah ghaz har abada kafarta bazata bar Masarautar BOYEM ba sai ranar da bana raye nabar duniya kenan to daga wannan lokacin ne zaka iya samun ikon mahaifiyarka amma Banda ina raye..
Wani irin motsi jijiyoyin NUAB din sukeyi suna fitowa idanuwansa kuwa ja suke rikidewa sunayi me tsananin gaske ya kafe idanuwansa akan sultan din Wanda yake magana hankali kwance,
Zafi jininsa yafara yi yana tafarfasa da maganar da sultan ke kokarin fada masa na cewa baida ikon mahaifiyarsa har sai ranar da sultan din yabar duniya Bayan shi bazai iya jiran hakan ba kome zai iyayi dan a basa mahaifiyarsa….
Bude Baki s