NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 12 of 146

tsira ba hakan kawai ya hakura su tafi kawai dan tseratar da ahalinsu. Tsoronta cirewa yayi tana Jin tsananin buqatan dawowansa su bar garin ta qwace daga riqon da yayanta sukai mata ta fice tareda janyo kofar da sauri ta rufe tana cewa bayin dake ciki tareda su suriqe su karsu Bari kowa ya fito. Kai tsaye Amman na fitowa gidan taga masifar fata saka kafafunta daukan wata irin rawar tsoro da firgici zuciyarta na Neman bugawa da sauri ta dafa bango sbd jirin daya debeta na ganin wuta koina da jini kaman bana mutane ba. Bangon dafa jini ne taji a tafin hannunta da sauri ta janye hannunta jikinta na sake daukan rawa. Juyawa tafara yi kafafunta na Neman kasa daukanta tafara baza ido Tana kwada kiran GHAZ Wanda bazai taba jinta ba koda yana kusa sbd karfi da qarar wuta da Ihun mutane da gurnanin rayukan da basu gama fita kirjin mutane ba, Taku kadan tayi Tana kutsa hanyar da mutane ke fitowa suna gudu baa hayyacinsu ba Ana ture juna, Bata ganin komai sai hayaqi da tsananin hasken wuta dake Kama mutane Tana kashe idanuwanta ga wani irin Zafin azabar da basu taba Ji ba dan haka ja da baya ta fara Tana wani irin Ihun kiran GHAZ. Gadan gadan kusrawa sukayo bangaren suna sarar mutane tako ina Ana gudu da Ihun mafi munin tashin hankali. Bude baki tayi Tana sake yin baya da sauri Tana kokarin ambatar GHAZ data hango yana fitowa gurin da gudun shima dauke da wasu yara qananu guda biyu duka mata Bude bakinta batareda maganarta takai ga fita ba wani irin mashi mai tsinin gaske ya keta wuyanta ya shiga makoshinta ya fita ta baya. Cak GHAZ daya kawo daf da ita ya tsaya yana cin wani irin birki idanuwansa a kafe sbd mummunan tashin hankali da firgici mafi munin rayuwansa. Sakin yaran hannunsa yayi yana tarota da sauri ta fado jikinsa babu rai idanuwanta a bude….. Jininta ne ya fara gangarowa daga wuyanta zuwa tafukan hannunsa dake tallafe da ita, Mummunan rawa dukkanin jikinsa keyi daya kasa riqeta din ta zame daga jikinsa. Rufewa idanuwansa sukai baya gani amma a hakan ya miqe ya sunkuceta ya Dora a kafadarsa ya Kama hannuwan yaran da hannunsa daya suka bar gurin da wani irin mummunan tashin hankali sbd gari kam an gama cinyesa wutar ta kawo gurin su sosai dan haka yake tsananta gudu. Gida ya nufa da tsananin tashin hankali sabo sbd dai dole yabar garin da yayansa sbd kowane lokaci zaa iya kashe su ko kamawa sbd wutar harta fara shigowa gidan nasa sosai. Yana shigowa ajiye gawar Amma yayi daga gefen dakin ya fizge rigarsa ta sama me dan kaurin saqi ya rufeta da ita. Ihun shigowan mutane dake Neman hanyar tsira ne da Ihun wainda wuta ke ci ne ta cike gidan nasa dan haka da gaggawa idanuwansa jajir fuskansa duk jinin Amma daya dauko koina ya bata fuskansa hakama hannuwansa da jikinsa koina jini ne. Tura kofar dakin yayi da karfi Wanda ya saka dukkaninsu miqewa tsaye cikin tsananin firgici da tsoro, Nurat ce ta fara cewa ‘ABAA’ cikin mummunan tashin hankali Tana nufosa da gudun gaske ta fada jikinsa. Abaas ya miqawa hannu ya Kama ya janyosa hakama Zuhrah koina jikinta wani irin mazari ya dauka ta fara ja da baya tana fita hayyacinta, Ayanah ma jinin jikinsa da fuskansa take kallo Tana kasa hawaye ma sai rawan jiki da jajayen ido, Fizgo Zuhrah Abaa din yayi yana cewa Ayanah ‘Muje,ku fita da sauri,Kuyi sauri ba lokaci’ Daqyar Ayanah ta iya bude bakinta daya bushe qayau sbd masifar tashin hankali tace ‘Abaa Amma bata nan,taje nemanka, Ina zamu ba tareda ta dawo ba? Qin kallanta Abaan yayi ya Kamo hannunta itama da karfi ya fito dasu Sauran mutanen da zasu samu kubuta tareda su suna biye dasu. Nurat dake da kokarin wucewa kaman ance ta juya idanuwanta suka sauka akan gawar Amma dake shimfide fuskanta kawai ne a rufe abin hannunta ta gane take ta tsaya cak tareda cewa ‘AMMA’ cikin wani irin sanyi da mutuwan jikin kasa yadda. Ayanah ce ta kalli gurin da sauri itama Tana Jin jininta na Neman kafewa, Abaas ne ya kwace daga riqon mahaifinsa ya nufi gurin da gudun gaske yana isa ya yaye rufar take ya some a gurin, Nurat ma silalewa tayi a gurin some sbd kasa dauka da zuciyar su tayi Ayanah ma salalewa qasa tayi zuciyarta na Neman bugawa ganinta yana disashewa Abaa yayi saurin dagota da karfin gaske shima zuciyarsa radadin gaske take kaman zata Dena bugawa amma sbd su bazai iya karyewa a lokacin ba sbd kubutar da rayuwarsu daga garin, Girgizata yayi da karfi tareda ambatar sunanta yana danne abinda yake Ji a kirjinsa na bugawan zuciyan dayake kokarin samu yace ‘Ayanah karki karye ke uwa ce a yanxu da babu Amma, Kece zaki zama garkuwan yan uwanki, Kece Amma yanzu, Kece madubi fitilar da zata haske hanyar da rayuwanku zatabi, Karki karye kiyi jarumta ba yanzune lokacin kukan rashin Amma ba, Ki dake zuciyarki ki kubutar da yan uwanki daga nan Allah ya Riga ya karbi Amma karki Bari burinta na kubutar da rayuwanku ya tashi a banza.’ Wata irin jijjiga jikin Ayanah keyi taba girgiza kai kuka me tsananin gaske na zuwar m
🏠