ko tsoro ba dan haka shi ASIM a yanzu baida muradi Bayan NUAB yabar BOYEM har abada ba dawowa dan ko ya mutu basa kaunar a kawo musu gawarsa BOYEM dan haka idan hakan zai faru to dole saisun kawar da wadda sbd ita kadai yakeda alaqa da BOYEM ayanzu da harma a gaba.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
57
Yanda masarautar ta dauki Zafi kusan haka kan kowa ya dauki Zafi kowa tinaninsa da burika tareda kudirinsa daukan zafi sukeyi babban matsuwar kowa burinsa ya cika ya samu abinda yakeso dan hakanne a wannan lokacin kowa harkarsa ce sa burinsa a gabansa,
Aleey shirye shiryen ganin komai na tafiyansu ya kammala yakeyi da Ammi wadda hakanan ta sakawa ranta NUAB ta kwallafa ranta fiyeda tinani akansa bata kaunar ko dare yayi ya tafi ya barta jin takeyi kaman kowane lokaci zai iya tafiya ya barta dan haka ta kasa samun sukuni da nutsuwa idan baya tareda da ita,
Hakan ne ya saka gabaki daya zuciyarsa ta sake riquwa da alkawarin tafiya da ita bazai taba sake rabuwa da ita ba har abada,
Su kansu Maa tenya yanda Ayanah ta qwallafa ‘dan nata a wannan Karan ya saka zuciyarsu shiga zullumi da faraban komai zai iya faru da lafiyarta me muni idan NUAB din ya tafi dan haka suma suke fata da tsananin adduar NUAB ya zauna a masarautar sbd sun San babu ta yanda zaayi wishmah tabar Masarautar matiqar sultan nata rai a cikinta zata rayu sai koma idan sultan dinne ya fita da ita da kansa zuwa rayuwa Wani gurin.
Shirye shiryen tafiyar da akeyi hadda Maa tenya da sakinah akeyi sbd suma full nauyinsu yana kansa kaman yanda na Amminsa yake kansa dan haka shirye shiryen suke samu dan delay sbd tafiya ce ta kwata kwata zaiyi dasu su da BOYEM se labari.
Tinda Yazo qasar bai fita koina ba koyaushe yana tareda mahaifiyarsa dan bata lokacinsa kuma baida kowane irin business a qasar kuma baya shaawan kullawa dan haka sun cikin fadar hutu kawai sukeyi suna jiran komai ya hadu.
A hakan suka share sauti hudu Ana Sauran kwana biyu wata Dayan da aka yanke masa ta cika komai na tafiyarsu ya kammala tsaf Wanda ya sakasa jin wata irin nutsuwa da sanyin zuciyar cikar burin tafiya da Ammi,
Aleey ne yaje har fada shi da securities biyu suna biye dashi ya isarwa da kadir babban hadimin sultan dashi kadaine duniya yakeda sirrin komai na zuci da bayyane na sultan sakon LEUL BOYEM yana buqatar ganawa sa sultan ganawar uba da ‘da bata sultan sa magajinsa ba.
Kadir cikin girmamawa ya Karbi sakon da kunnuwa sa zuciyarsa ya isa gurin sultan daga gefensa ya dan ranqwafa cikin girmamawa daya sanar masa batareda duk Wanda yake fadar ba yaji sundaiyi tsit sbd ganin su aleey da securities din NUAB din sunsan sakon daga bangarensa ya taho.
Sultan daya gama sauraron sakon bai furta komai Wanda yanayinsa kadai kadir ya kalla ya gane me sultan din yake nufi dan haka ya juya ya koma
Inda suke ya isar musu da sakon cewa sarki zai ga LEUL BOYEM anjima Bayan sallar ishai a palon hutawarsa.
Da wannan sakon su aleey suka koma ya sanar da NUAB din Wanda yana Jin hakan ya ajiye wayar dake hannunsa gefensa yana nade hannuwansa biyu a kirji fararen idanuwansa na kafe a makekiyar flat screen din dake gabansa.
Da kansa ya sanar da mahaifiyarsa tafiyarsu a Washe gari insha Allah hakama su tenya,
Su tenya da sakina sanyi jikinsu yayi suka shiga zullumi da tinani Kala Kala zuciyarsu na rasa nutsuwa da sukuni sbd sanin hakan ba abune me yiyiwa ba batareda tashe tashin hankali ba da tsallake karfaffun sharudda daban daban dan haka a tsaye zukata da hankalinsu yake suna jiran abinda goben zata haifar idan har zasu samu barin masarautar kaman yanda NUAB ya kudirta da su kansu yanda suke so indai Zasuje suyi rayuwa da Ayanah da NUAB din sun shirya barin Masarautar BOYEM da basuda kowa a cikinta tinda ita kanta tenya yayanta duka basa nan suna gurare daban daban suna aurensu.
Tinda ya sanar dasu suke cikin zullumi da tashin hankalin da baya faduwa kuma baya nunawa musamman tenya data San aka samu matsala akasan dasu ake shirin barin masarautar da wishmah hakan zai iya zama bakin rayuwarsu dan haka suke a rashin nutsuwa da sukuni kwata kwata tareda jiran goben da zasu bar masarautar da qasar gabaki daya shikenan komai ya qare na tashin hankali da damuwa Ayanah zata rayu da ‘danta.
Ita kanta Ayanah din Wani irin rashin sukuni da zullumin goben takeyi sbd tabar nan tabi HAYATEEM duk inda yake rayuwa itama tayi rayuwar acan tareda shi da Abaas da shima yayi mata alkawarin a kwanakin nan zai fara Neman kawo mata shi.
Gabaki dayansu wunin a cikin zullumi me tsanani suke yinsa kaman yanda bangaren HAILE da yayanta suma suke cikin zullumin watan daya cika hakama manyan fada da suma suke cikin zullumin abinda zai iya faruwa a fada yanzu kuma dan suna ji a jikinsu duk Wanda yayi garajen kasa tsayawa ya duba kalaman sa da kyau zai iya rasa ransa batareda yakai qarshen l