rautar ne batareda ya fita koina sbd ya samu lokaci isashe me tsayi da nutsuwa tareda mahaifiyarsa kafin ya basa umarnin dayake ransa na shekaru Akan amsar mulkin BOYEM cikin lumana dan kuwa ana fara wannan yaqin bazai samu irin wannan nutsuwan kulawa da mahaifiyarsa ba dan tako Ina fitina ce zata bude kofa musamman ga wainda suke jiran amsar mulkin da manyan fada dan shi koma menene NUAB din ya zama shi shine yake son ya zama mai mulkin BOYEM bayansa kota halin yaya ya shiryawa kowannensu a tsakanin shi NUAB din da bazai karba ta lalama ba da wainda zasu tada hankalin baa basu ba da manyan fada da duka zasu iya kasa Aminta da hakan a shirye yake da kowa.
******a bangaren LEUL kuwa koda suka koma saida ya sake sabon wanka ya shirya cikin ash Rb wears da suka zauna jikinsa a natse qamshinsa me sanyi na tashi ya fito palonsa inda aka kawo abincin rana daga bangaren Amminsa aka cika dining din a Jere babu kalan fruits din da babu Bayan lafiyayyan abinci Kala uku.
Zaunawa yayi a natse batareda damuwan komai a ransa ba duk da har lokacin zuciyarsa daukan dumi takeyi idan ya Tina rashin daar da aka nuna ta aiko bayin mahaifiyarsa kiransa,
Bai damu da hukuncin sultan akansa ba sbd bayajin akwai dalilin daya isa ya hanasa fita idan ya tashi fitar musamman da Ayau din ya basa umarnin aleey ya fara shirin tafiyarsu da Amminsa barin qasar gabaki daya Wanda da kansa a shirye yake da samun sultan ya fada masa da Amminsa zai tafi Kai tsaye idan shirye shiryen suka kammala kenan.
Tareda Yaransa gabaki daya suka ci abinci a dining din Wanda hakan ke qara musu kaunarsa da tsayuwa Akan kowane lamarin sa dan babu kyama ko nuna banbancin matsayi a tsakanin sa dasu,
Cikin kulawa da sakewa sukaci abincin aleey na sake koro masa bayanin manyan fada guda nawa ne a tarihin Masarautar hakama guda nawa ne suka Halarta taron yau din da dukkanin yanayinsu daya nuna a fuskarsa tareda sunayensu babu Wanda bai dauko komai akansa ba tsaf dan haka kwakwalwansa take tamkar computer.
Bayanin full binciken rayuwar ASIM daya hada da abinda ya qara karanta tattare da yanayi sa na yau din shima ya fara koro bayanin a tsare dalla dalla cikin ilimi da tabbaci tin daga kan karatunsa na primary har zuwa yanxu dayake da har masters da Sauran ilimin wasu abubuwan tas.
Dakatar dashi NUAB yayi daidai lokacin da zai zayyana bayanin su Aslam da mahaifiyarsu tas sbd baya buqatan sanin kowa da komai a masarautar tinda baida alaqa dasu bakuma zama zaiyiba bare rayuwa a cikinsu.
Sai yamma Bayan magrib ya sake komawa gurin Amminsa wadda take jiransa zuciyarta cikeda ‘doki dan haka tare suka ci abincin dare tana jin kaman zata maidasa ciki sbd tsananin kaina shi kuwa kowane motsinta kashe jikinsa yakeyi sbd yanayinta dake nuna she’s very weak hakama fatarta kaman tanayin pale.
Sai dare sosai Bayan ya tabbatarda tayi bacci kafin ya Baro bangaren ya koma nasa,
Wanka yayi ya saka Kayan baccin James plebe ya daure gashinsa tsakiyar kansa ya dauki wayar sa ya kunna ya Nemo numbern likitansa dayake Greece ya sanar masa da yana buqatan qwararrin likitan zuciya da kwakwalwa su shirya su hadu a qasa daya ko Greece din dazai kawo mahaifiyarsa a duba masa lafiyarta cikakkiya.
Washe gari haka ya dake tafiya gurin mahaifiyarsa ya wuni tareda ita yana bata lokacinsa da rayuwarsa gabaki daya ta wannan lokacin kafin sbd ganin hakan na taimakawa gurin samun kuzarinta.
Kaf masarautar haryanxu bame samun damar ganinsa dan kuwa duk lokacinda zai fito daga bangarensa zuwa na mahaifiyarsa watsewa kowa keyi sbd Yaransa dake tare hanyar sbd tsaro,
HAILE da ‘yayanta kuwa baqin cikin jiran wata Dayan ta cika ya hanasu kowane irin motsi tinda dole dik shirinsu su jira wata dayan tayi su ji me sultan zai yanke akansa,
Fada ma gabaki daya sun kasa sakewa sbd shakka da zullumin me wata Dayan zata haifar idan ta cika,
Duk tsawon wannan lokacin NUAB bai taba zuwa gurin sultan ba dan haka basu sake haduwa ba bakuma su da niyar haduwar kowa da abinda yake ransa Akan haduwar tasu sbd NUAB jiran komai ya kammala yakeyi ya samu sultan din ya tsaya a gabansa da kansa ba sako ba ya sanar masa zai tafi da mahaifiyarsa.
Shi kuwa sultan ranar yake jira sbd yana sane da dole bazaa rasa dalilin da zai saka NUAB zuwa garesa ba indai Ayanah tana raye dan haka ranar shima yake jira.
********koina masarautar ta fara daukan zafi sbd watan nan daya tafiya yakeyi amma kamar shekaru suke jinsa ganin baya gudu dan kuwa Kai tsaye su HAILE sun gama yankewa da tsayar da sabuwar shawara me karfi Akan NUAB na barin BOYEM zasu kawar da abinda ya rage masa kadai a BOYEM
Wanda zai sakasa dawowa koba yanzu ba wato uwarsa dan kuwa tana barin duniya sunsan bazai taba dawowa BOYEM ba,
Wannan sabon burin ya kafu ne a ransu sbd zuciyarsu kaf data rasa nutsuwarta sakamakon tarihin LEUL BOYEM tas da suka samu daga kwakwaran bincikensu Wanda ya gigita kwakwalwansu da sanin cewa su idan a boye zasu iya daukan ran mutane shi a tasa duniyar a bayyane sukeyi batareda shakka