NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 117 of 146

ka da shigowa amma babu Wanda ya kalla zuciyarsa gap take da bugawa ya isa palon hutawar mahaifiyarsa inda ya tadda su a tsaye dukkaninsu Banda meryam dake Zaune itama tana dafe da goshinta Aslam da HAILE kuwa a tsaye suke qyam kowannensu abinda ya faru a fadar yake son ji dan kuwa suna tsammanin jin zazzafan hukuncin da zai saka NUAB zuciya ya sake barin qasar gabaki daya. Yana shigowa suka zuba masa ido dukkaninsu suna jiran jin bayani a bakinsa amma ganin yana yinsa ya saka jikin meryam da Aslam sanyi suka zauna batareda sun furta komaiba sedai HAILE ne tace ‘Meya faru? Yaya akai a fadar? Wane hukunci sultan ya zartar masa? Zai bar qasar dai ko? Zazzafan fushi me tsananin zafi ne ya taso masa ya saka hannuwansa biyu ya dauki table din dayake gurin cikeda Kayan marmari da Kayan ciye ciye ya daga sama ya buga qasa da karfi komai ya fashe da karfi tareda watsewa da kara me karfi. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 56 HAILE data ga hakan take zuciyarta ta tabbatar mata da basu samu abinda suke so ba kenan, NUAB bai karba kowane hukunci ba daga sultan kenan, Matsalarsu akwai yiyuwar zata fara ne daga yanzu matiqar NUAB yana nan, Kallan ASIM da idanunwansa suka mugun jajir tayi tana bude Baki zatai magana ya Katseta da cewa ‘Ba dan taadda kadai bane mahaukaci ne,haukace da kanta take kwance a cikin jininsa bawai a cikin kansa bama,ya tabbatarda shine bastard son da sultan YASAR me BOYEM yakeda shi a Idon duniya’ Aslam da duka ba wannan take son ji ba dan bata jin kowace hauka ce akansa zai gagaresu su da suke su hudu ga kuma manyan fada a bayansu hakama ASIM ALMAZZ shi BOYEM ta sani a matsayin ‘dan sultan dayake tareda shi kawai ita hukuncin da akaiwa NUAB din takeson ji dan jin hukuncin ne zaisa su sani ko NUAB din zai tafi ne yanzu ko zaman qasar. Meryam kuwa da tsananin quncinta da rufewan Idon son cikar burinta ta samu abinda takeso to ita koma waye se hau mulkin BOYEM yanzu indai zai janye musu hukuncin dake kansu babu abinda ya shafeta muradinta kawai tayi auren kada ta qare a haka ta mutu a hakan tsufa na cimmusu a ba aure bare ‘yaya. HAILE kuwa guri ta nema ta zauna haka shima ASIM din zaunawa yayi yana zayyana musu abinda ya faru a fadar tas. Shiru Aslam da meryam sukai kafin suka dago suka kalli juna meryam na shaqar Wani Numfashi me zafi sbd tabbas ita kam yanzu takai karshe bazata yadda a fara wannan sabon rikicin da zai zama babban al’amariba a lalata Sauran lokacin da suke tinanin suna dashi na samun abinda suke so dan kuwa komai rikice zeyi yaqin Neman mulkin ya dawo sabo duk suna nan suna jiran a gama me hawa ya hau ita kam yayi mata tsayin da tabbas ba lallai ta iya jira ba dan haka duk inda taga alamar nasara da gaggawa wlh can zata koma ba bata lokaci koda kuwa hakan na nufin tabar ‘dan uwanta uwa daya uba daya ta zabi bastard son din. Aslam ma Zurfi tayi a tinanin da babu alkhairi ko daya a cikin ranta dan ita kam ko zata qara shekara nawa batajin zata taba kaunar ko Inuwar Wanda ma yake kaunar Ayanah da NUAB. Shiru sukai dukkaninsu suna tinanin ta inda zasu fara wannan sabon yaqin da suke ganin kaman yana tinkaro su batareda sunyi tsammanin Wanda sukewa kallan baida banbanci da almajirin yan taaddan shine taaddancin ma da kansa, Kuma idan har zai iya tsayuwa a gaban sultan me BOYEM da babu dan Adam din dayake BOYEM da zai ita tsayawa gaban idonsa ya kallesa bama bare tsayuwa ba kaya daga shi zai towel a gaban dukkanin manya fada da suma iya karshen rashin girmamawan rayuwa sun samesa a hakan da yayi musu to tayaya suke expecting akwai abinda zai girgiza sa, Numfashi HAILE ta sake me Zafin gaske kafin ta dago ta kalli ASIM da idanuwanta da sukai jajir itama ta bude Baki tace ‘Ka saka salman yayi kwakwaran binciken qarshe Akan NUAB din ya binciko waye shi da wainda yake tare da huldodinsa da matsayin dayake tinanin yanada shi dan da alama akwai Wanda ya tsaya masa, Hakama ta Dayan bangaren babban abinda zai kawo sassauci a wannan yaqin da zaayi dashi nasarar mu ta zarce tasa shine tabbatarda qiyayyarsa da sultan bame warware wa bace har abada hakama Ka tabbatarda an gano menene abinda yafi so da’ Shiru ASIM yayi baice komaiba sai idanuwansa jajir daya kafe Hailen dasu yana sauraronta dan kuwa ta hakan zai fara tabbas yana buqatan sanin komai Akan NUAB sbd abinda aka fara musu akansa ba shuke idanuwansu suka gane masu akansa ba. ******Sultan kuwa tinda ya bar fadar yake Zaune palon sa cikin nutsuwa Zaune yana jin tinanikansa da burikansa suna gauraraya da warware wa da saqawa sbd duka burinsa Akan NUAB ya zama tsayayyen Zakin BOYEM ne da zai riqe uwa da qasar da Amana amma hakan ya budewa alaqarsu sabuwar babbar alaqar nisanta da juna tareda zama Wanda fushinsa da zafinsa yayi yawan dabai tsammata dan haka ya basa umarnin tsayawa cikin masa
🏠