NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 113 of 146

, Ayau Asuba tsaka kawai cikin bacci da rashin tsammani ko a mafarki sukaji sautin sanarwar dawowansa batareda aiko da sakon dawowan tasa ba kaman yanda yake tilas kawai suka samu dirarsa a masarautar, Babban abinda ya girgiza kaf manyan fadar masarautar shine a bayan ASIM ALMAZZ suke sun shirya tsaf sun yanke kuma sun kudirta shine sultan na boyem dan kuwa daga ranar da aka wayi gari babu sultan bazaa qara awa biyu ba batareda sun nada ASIM ALMAZZ ba wannan Alkawari ne da burin da kowannensu yake dashi. Dan hakanne dawowan LEUL BOYEM ta girgiza su jijjiga me karfi sbd basu taba saka ran dawowansa ba Sun shirya goge sunansa da uwarsa a cikin tarihin boyem daga ranar da sultan YASAR yabar duniya hakama sun saka rai sun kwanta da tinanin koda zai dawo qasar to sanar da daya daga cikin iyayensa sun mutu. Meya dawo dashi kwatsam haka babu zata ba tsammani? Menene dalilinsa na dawowa Bayan shekaru masu tsayi? Idan ma yana tinanin ya dawo ne karban matsayinsa to tabbas ya makaro dan bazasu taba Bari ba korasa zasu sake yi inda ya fito wannan Karan ma shi da uwarsa kila dan haka a shirye suke dashi zasu nuna masa karfin matsayin da suke dashi Wanda sunada ikon zartarwa, ASIM ALMAZZ ne sultan na gaba Wanda da karfi zasu tabbatar masa da hakan ya tattara ya koma Gagarin dayake yi bada gatan masarauta ba hakama dole zai amsa kiran shugabannin Masarauta ya fuskanci hukuncin dokar daya taka ta masarauta ta zuwansa batareda ya aiko manzon aike ba da wannan zasu hukuntasa ya koma inda ya fito. Hakan ya saka kusan dukkanin manyan suke a cikin tinani daya da shiga tsananin son ganinsa da isar dayake ji da ita dan haka suke a cikin shirin isa fada da gaggawa sbd ko sultan dole yana can cikin bacin rai da fushin abinda LEUL din yayi. Koda karfe goma na safe ta buga duk Wanda yake masarautar ya samu cikakken labarin isowan sa, Hakama waje da garuruwan dake qasar sun fara samun labarin dawowan LEUL BOYEM, Yan jaridu ma da television tini suka fara yada Labaran Wanda Aleey ne da kansa ya basu cikakken bayanan ta waya sbd qasar BOYEM ta shedar da zuwan magajinta koda kuwa ziyace kadai ya kawo ba zama Yazo yiba, Yanda zancen ya ringa yaduwa da shiga koina ya saka mutane dama yan jaridu fara jefa maganganun to a yanzu waye asalin magajin da zai mulki BOYEM, Waye asalin me BOYEM a cikin magajin guda biyu da ake dasu, Waye sultan zai zaba bawa mulkin da kansa kokuwa jira zaiyi saiya bar duniya Allah ya bawa me rabo saa? Wannan maganganun ne suka fara daga hankalin wainda sai daga baya labarin dawowan LEUL BOYEM din ta samesu maana ASIM ALMAZZ kenan da HAILE wadda ta tabbatarda NUAB ALMAZZ dinne ya dawo da gasken gaske kenan. Gabaki dayanta da yayanta a Zaune suke babban palonta na hutawa sunyi shiru kowa da abinda yake ransa idanunwansu jajir babu Wanda jininsa baya tafasa yana hawa sbd tsagwaron zallan baqin ciki bawai dan suna tsoron sa ba sbd basa tinanin yanada abinda zai sakasu tsoron sa ko shakkarsa kawai dai sultan da suka gama samun cikakken kansa Akan tinanin yama gama Dora ASIM ALMAZZ a mulkin BOYEM yanzu kuma wannan ya dawo zai rikitar musu da tinani da raayin sultan dan haka suke cikin baqin ciki me tsanani amma Bayan hakan Sam sunsan tako ina babu inda zai kamo kafar ASIM a komai dan haka sukai shiru cikin takaici da baqin ciki, ASIM ALMAZZ dayake Zaune a kujeran datake ta Mutum daya idanuwansa a dan rufe yayi shiru da zurfafa a tinani bude idanuwansa yayi ahankali ya sauke Akan mahaifiyarsa kafin ya bude Baki cikin tasa Izzar da Wani irin yanayin dayake ji a ransa na babu Wanda ya isa ya rabasa da matsayinsa dayake Kai da Wanda yakeso a duniyar nan batareda ta aikasa inda ya kamacesa ba yace ‘Mamee babu abinda zai faru ki kwantar da hankalinki kokarinki na shekaru bazai taba tafiya a banza ba zan tabbatarda da hakan, Indai ba nine magajin karagar mulkin BOYEM ba to tabbas BOYEM zata rasa magaji da sultan din da zata kira nata, Kawai dai a yanzu ku Bari wannan dan gudun hijirar daya dawo ya gama abinda ya kawosa ya tattara mistress din mahaifinsa ya qara gaba da ita zuwa yawon bin yan taaddan da akace yanayi.’ Karban zancen HAILE tayi cikin wani irin radadin zuciya da cewa ‘Banda rashin tinani irin na Ubansa da tsufan dayake cinye kwakwalwansa tayaya zaiyi tinanin ma sauya Ka daga zama mai mulkin BOYEM Akan Wanda yagamo yawon duniya da taaddanci’ Numfashi meryam kawai ta iya saukewa me zafi tana fatar koma menene kowa zeyi yayi itadai buqatarta ASIM ALMAZZ ya zamo me mulkin BOYEM ya dauke hukuncin dayake kansu ta auri koma Wanene zata samu. Aslam kuwa can qasar zuciyarta Wani irin tsoro da fargaba takeji Wanda yake hanata cewa komai dan kuwa koma yayane dawowansa su dai ba alkhairi ce a garesu ba, ASIM ma a qasan zuciyarsa wata shakka ce ke son shigarsa da matsuwa da son haduwa da NUAB ALMAZZ dan yaga menene yake dashi a yanzu sannan ya sheda cewa shi ASIM ALMAZZ yanzu ya fisa komai musamman ilimin daya samu cikakke me kyau Wanda ko hakan zai saka a basa
🏠