NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 112 of 146

mummunan abu ya sameta dan itace kuzarinsa kuma itace weakness dinsa dazai iya bada komai nasa da kansa akanta. Kuka takeyi sosai tana Jin zuciyarta kaman zata fashe da tsananin kauna da son ‘danta Wanda bata taba ji a ranta zata gansa a gaban idonta ba,ta cire rai daga ganinsa har rayuwarta ta fita tabarta, Da kewa da radadin rashin sa take kwana take tashi tareda wuce kowace daqiqar rayuwarta amma bakinta kaman an riqe bata taba iya cewa ya dawo koyaushe sedai kada ya dawo bama zata iya tina yaya bakinta ya iya furta masa tana son dawowansa ba kuma duk da ta furta din bata saka ran zuwan nasa ba bare ganinsa ba dan haka take Jin Wani yanayi na tsananin farin cikin rayuwarta a karo na farko Bayan shekaru masu yawa cikin qunci da baqin ciki Ayau ruhinta ya dandana dandanon farin ciki da samun abinda zuciya ke so dan haka take sake qanqamesa da rashin kuzarin datake fama dashi tana rufe ido sbd kuka. Sun jima a hakan tsawon lokaci kafin a natse ya zaunar da ita Akan sofa mai Laushi yana riqe hannunta cikin nasa cikeda dukkanin kulawa da bayyananniyar kaunar datake shigarta tana sake kashe jikinta akansa tana kasa dauke idanunwata Akansa farin cikinta a bayyane. Hannunta ta daga ahankali ta Dora Akan fuskansa ta shafa tareda sakin murmushin daya saka idanunwansa qarasa rikidewa jajir sbd Ayau itace ranar farko dayaga murmushi Akan fuskar mahaifiyarsa tinda ta haifesa, Bude Baki yayi da Wani irin sauti daya sake sakata shafa fuskarsa tana ganin kammanin da bazata taba mancewaba shimfide a fuskarsa yace ‘Ammi,Ammi na dawo gareki bazan taba sake rabuwa dake ba koda zan rasa komai Akan hakan, Ammi bazan iya sake rabuwa dake ba, Ammi zan nema miki lafiya da duk abinda kikeso nayi miki Alkwarin cika miki shi, Ammi zan tafi dake na Nemo miki Abaas a duk inda yake fadin duniyar nan na kawo miki shi gabanki, Ammi ina son ki cire dukkanin damuwa da quncin dayake ranki sbd lafiyarki, Ammi……. Hannunta ta Dora a bakinsa cikin nutsuwa kafin ta rungumesa tana kwantawa gefen kafadarsa ta bude Baki tace ‘Zan bika duk inda zaka tafi dani HAYATEEM, Bazan iya rayuwa ba idan Ka tafi Ka sake barina, Zuciyana bazata iya sake daukan rayuwa babuka ba HAYATEEM, Karka banni Ka tafi dani ko ina ne zan bika na rayu tareda Kai sanyin idaniyata…. Yanda take maganar ya sake Sosa zuciyarsa fiyeda yanda zai iya boye wa dan haka hannuwansa suka dan ringa rawa ya rungumeta sbd akwai alaman rashin lafiyan jiki da tinina sosai a bayyane da sautin maganarta. Maganganu ya bude Baki yafara jero mata masu nutsuwa da samar da nutsuwa a kwakwalwanta yana bayyanar mata babu abinda zai qara rabasu sai mutuwa dan haka ta kwantar da hankalinta ta cire damuwan komai dan babu inda zashi batareda ita ba. A daidai wannan lokacin aiki akeyi gadan gadan a bangaren me girma LEUL din Yaransa suna tsaye qyam Akan aikin Wanda take aleey yayi ordern wasu manyan Kayan da abubuwan da suke buqata na ubangidansu daga wajen masarautar kuma aka kawo cikin gaggawa suka duqufa sbd kafin ya gamo ganawa da mahaifiyarsa suke buqatan komai na bangaren ya kammala daidai da hutawarsa, Acan bangaren wishmah dinma Maa sakinah ce a tsaye tareda masu aiki da bayi Ana aikin abinci na musamman me tsari da tsaftar gaske tareda lafiya daidai da taste dinsa tin na yarinta duk da sunsan ya sauya tako ina amma dai sunsan zai kaunaci komai da zaayi masa sbd kewansu da kewan kulawansu akansa da girkinsu. Maa tenya kuwa take qwanjinta da kuzarinta harma da walwalanta ta dawo a lokaci daya Jin kanta takeyi tenya dinta ta baya da zata iya tsayuwa ako ina dan bawa NUAB da Ayanah kariya da duk abinda sukeso dan haka take ta bada umarnin a tara bayin da zasu ringa hidimar bangaren LEUL boyem da kanta zata zabesu ta basu training me karfi da kyau dan kuwa karfinsu ya dawo fiyeda ma Wanda suke dashi a baya dan kuwa a bay suna shakkar a cutatar musu da NUAB suna basa kariya amma a yanzu shine Wanda zai basa kariya a karkashin iko da karfinsa. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 54 Tin asubar da sautin karar dawowan LEUL BOYEM ta shiga kunnuwan duk wani babba me matsayin dayake masarautar a tsaye suke suna kaida kawo cikin mamaki me girma da shakka tareda tinani kala kala Wanda rashin tinanin kamawa ma yafi yawa a cikin kwakwalwansu sbd a tsawon shekarun nan sun manta sun shafe magana da tarihin LEUL boyem daga masarautar babu Wanda ko a maida zance ya kuma tada maganarsa kaman yanda sukaga sultan bai taba maganarsa ba saisu ma suka watsar dashi da zancensa kaman yanda aka rufe babin mahaifiyarsa kwata kwata baa ma sakota a lissafin matan sultan kokuma wanzuwarta ako wace hidimar masarautar da ake buqatan halartar matan sultan din dan duk inda akace matan sultan to su uku ne keda cikakken ikon sunan sbd zamantowanta wishmah duka ya Halarta mata wannan suna da matsayin
🏠