basuyi darajar da zasu kallesa ba dan haka ko motsi me sauti babu me yi tsit hanyar ta dauka badan babu mutane ba Sedan tsananin bada girma ga jinin BOYEM.
Tinda ya tinkaro din shima kowane takunsa dawo masa da kowane Taku da yayi a ranar barin masarautar yake,dawo masa da takun da yayi a ranar daya rabu da mahaifiyarsa,rayuwarsa sanyi da hasken idaniyarsa wadda se yau ze sake haduwa da ita,
Babu hanyar da zata isar da shi bangaren mahaifiyarsa ko daya data bace masa duk da akwai manyan gyare gyare da sauyi da aka samu me yawa amma dai mahaifiyarsa na nan inda ya barta dan haka babu jiran komai Kai tsaye gurinta yake nufa.
Koda ya iso kofar bangarenta dayake dauke da sunan wishmah Baro Baro a jiki wani irin Numfashi me sanyi ya sauke yana dawo da kallansa kan Maa sakinah datake fitowa a hankali cikeda mutuwan jiki da mamaki idanuwanta na sauyawa da wani irin kallan datake masa zuciyarta na sake narkewa dan kamannin jinin GHAZ dayake bayyane a fuskarsa musamman Abaas Wanda yafi Kama da Ayanah sak dan haka kasa cigaba da kallansa sakinah tayi tana qasa da idanunwata hawaye na taruwa a cikinsu,
Maa tenya ma a sanyaye take fitowa dan tarbansa a matsayinta na jakadiyar Amminsa dan haka saukar da idanuwanta qasa tayi daga kallansa tana jinin Wani irin girmammen farin ciki da mutuwar jiki a lokaci daya dan haka bude Baki tayi zata fara gaisuwa da kirarin dayake dolenta…..
Katseta yayi Kai tsaye da muryansa data saka bayin dake bangaren sake Shan jinin jikinsu kansu a qasa,
‘Na dawo Maa’ ya fada a natse Kai tsaye yana kallansu su biyun zuciyarsa cikeda kauna da girmansu,
Tenya ce kauna da matsayin dayake dashi a cikin ranta ya danne matsayinta na jakadiyar sa data mahaifiyarsa ta dago tana fidda Wani murmushin farin ciki mai sanyi tace
‘Barka da dawowan me BOYEM da kansa,
Barka da dawowan Hayateem me zuciyar uwa da uba,
Barka da dawowan Zakin mazan boyem,
Barka da dawowan me jinin boyem da ghaz,
Barka da dawowan magajin asali na BOYEM,
Barka da dawowan LEUL me uwa uku’
Numfashi kawai ya isa saukewa yana kallan Maa sakinah da adduoin tsari kawai take jero masa a zuciyarta da ko bata bayyana ba ya sani haka take ita koyaushe bakinta a cikin adduar basa kariya da tsari daga kowane Sharri take kuma baa fili ba,
Ciki suka juyo suna qarasowa suna gaba yana bayansu dan yi masa iso ga inda mahaifiyarsa take,
A babban palon suka tsaya dukansu suna basa hanyar wucewa palo na gaba shi kadai dan isa ga mahaifiyarsa,
A natse ya wuce ya isa kofar ya saka hannunsa ya bude tareda saka kafarsa ciki idanuwansa na dagowa kallan kofar dakinta data bude itama tana fitowa da tsananin sanyin kafafu idanuwanta da sukai ja suna sauka akansa batareda ta kyafta ba
Shi kansa idanuwansa jajir suka a lokacinda ya kafeta dasu yana mata kallan da kowace gabar jikinsa ke amsa tsananin kaunar dayake mata.
Kasa motsawa tayi daga inda take cak duniyarta na Wani irin Juyawa sbd kasa yadda da abinda idanuwanta ke gani,
Da gaske ne NUAB dinta ne a gabanta kokuwa ire iren gizon da yake mata ne shi da Abaas,
Shi kansa mutuwar tsaye yayi a gurin dayake yake din yana kallan kowane yanayi da mahaifiyarsa ta koma Wanda hadda manyanci dayake nuna tsufa Yazo a tattare da ita ga ciwo fa qunci da damuwa da kadaici tareda rashin cikakken tinin kanta dan haka kan idanunwansa suke sake yin ja radadin rashin lokutan mahaifiyarsa da aka rabasa dasu tin kuruciya suna dawo masa dan kuwa an hanata yarintar ‘danta kaman yanda aka hanasa yarinta a gaban mahaifiyarsa,
An hanasa samun kulawa da tattalin a lokutan ciwonsa da baqin cikinsa kaman yanda kowane ‘da yake samu daga mahaifiya ko mahaifansa,
Shi shikadai yake ciwo yayi jinyar kansa ya kula da kansa ya tsayawa kansa yayiwa kansa komai tamkar marayan da baida uwa baida uba baida gata,
A lokutan ciwo mai tsanani da dama yayi kukan rashin mahaifiyarsa da dumin jikinta kadai zai iya basa warakar dayake nema da sassaucin kowace irin azaba amma duka an hanasa samun hakan an hana mahaifiyansa samun basa hakan daga karshe dai Bayan shekaru Ayau Allah ya hadasu haduwan da mutuwa ce yanzu kadai zata rabasa da ita badai kowane ‘dan Adam ba komai matsayinsa kuwa a duniya.
‘HAYATEEM’ bakinta ya bude ya furta a hankali cikin wani irin sautin daya saka gabaki daya tsigar jikinsa tashi ya tako bai tsaye komaiba ya janyota jikinsa ya rungume da Wani irin karfi yana rintse idanuwansa da har wani radadin yaji suke masa.
Sake ambatar sunansa tayi da sautin daya sake tada duk wata tsigar jikinsa tana Qanqamesa ta fasa wani irin kuka mai qarami da sanyayar sauti tana Jin nauyin kirjinta yana fadawa qasa ahankali ta sake qanqamesa tana ambatar sunansa.
Dagota yayi ya Kama fuskarta da tafukan hannuwansa biyu yakai bakinsa tsakiyar kanta yayi kissing cikeda tsananin kaunarta ya sake juya gefen fuskarta yai kissing ya dago hannuwanta duba biyu yayi kissing kowanne ya sake rungumeta jikinsa tsamtsam yana Jin kaman bazai taba iya rayuwa ba daga ranar da wani