NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 110 of 146

bu sukuni. *****Motocin daya bayan daya suna zuwa can quryar harabar da iya jinin sarautar suke isa can a Jere suka fara Parkin daya bayan daya cikin tsarin da suka saba motar LEUL dince a tsakiya Kai tsaye suka fara fitowa daya bayan daya aka bude kofar da LEUL BOYEM yake Zaune ya ziro kafafunsa cikin izza waje kafin ya fito gabaki dayansa yana shakar iskar Masarautar datake jininsa, Lumshe fararen idanuwansa masu kyau da kwarjini me zafi yayi yana Jin Wani bangare na zuciyarsa yaja cikewa da gurbi me Zafin dayake ciki da wani sanyi me ratsa zuciyar sbd Ayau gashi inda mahaifiyarsa ke rayuwa yana shaqar iskar Numfashi daya da ita, Gabaki dayansu a tsaye suke qyam babu alaman gajiya ko buqatan Hutu a tattare dasu ko kadan saima karfinsu mai daga hankali dayake sake bayyana. Sarkin bayi ne cikin wata irin gaggawa ya iso gurin tareda tarin bayin da suka zube qasa gabaki dayansu kansu a qasa suna gaidasa batareda sanin yabar gurin ba Kai tsaye bai jira komai da kowaba ya doshi bangaren mahaifiyarsa shi daya tak sbd babu me hurumin shiga bangaren matan sarki idan ba ‘yayansu ba dan haka gabaki daya Yaransa suna tsaye a inda motocin su suke babu alaman sauki ko rahama ko daya a fuskarsu. Aleey ne ya sanar da sarki bayi LEUL BOYEM ya Riga ya wuce bangaren mahaifiyarsa nasa bangaren suke buqatan a kaisu dan tabbatarda tsaronsa. Babu bata lokaci Kai tsaye aka wuce dasu bangaren nasa me girma Wanda yake part guda mai tsari da kyau, Duk da baya nan babu shekarar da baa sauya furnitures da komai na bangarensa sbd haka doka da kaidar take, Komai na sauyin da ake masa ahankali ahankali yana tafiya ne da cigaban zamani da ake samu har zuwa yanzu da aka zuba duk wani luxury na rayuwa da zai basa Hutu da nutsuwa isasu, Komai a tsare yake da duk abinda zai saka yaji kaman yana gidansa na Moscow kawai dai yar qura ce sosai itama a take Sarkin bayi ya fara bada umarnin a fara gyara. Dakatar dashi Aleey yayi cikin nutsuwa da buqatar full control na kulawa da komai daya danganci lamarin LEUL komai qanqantarsa, Babu abinda babu a Masarautar BOYEM na Jin dadi da biyan buqata dan haka take Aleey ya bada umarnin a fara sauya komai dake bangaren a cikin kankanin lokaci dan haka ba bata lokacin Sarkin bayi ya saka a fara fidda Kayan a fara shigo da wasu da suka fisu komai. ******Sultan YASAR a daidai lokacin da sautin qarar dawowan magajin dayayi shekaru yana jiran wannan ranar ta dawowansa a wannan lokacin wayar sa ne da wishmah ayanah ghaz wadda a tare sautin ya shiga kunnuwansu ya isa ga zuciyarsa yana sanyayar da wani gurbi me girma da yayi shekaru a zuciyarsa, Ahankali sautin yake sake ratsashi ya rufe idanuwansa masu kyau da kwarjini yana jan wani Numfashi me dumi ya saukesa a hankali tareda bude idanuwansa Akan fuskar Ayanah dake bayyane kan screen dinsa shiru ta zuba masa ido a sanyaye bata iya cewa komai. A natse cikin sanyin nutsuwa ya sauke ajiyan zuciya datake dauke da shirin zartarwa da shirin fuskarta abubuwa da dama a masarautar da wainda suke cikin masarautar dan kuwa wannan ranar yake jira Wanda NUAB ALMAZZ zai kawo kansa masarautar da kansa amma kuma fitarsa da kansa ya rasa kenan saida umarnin sa dan kuwa shine yake riqe da cokalin juya rayuwarsa yanda yaso har sai ya cika masa burinsa daya dauka akansa tin daga ranar daya diro duniya, Burinsa daya saka ya banzatar da abinda yakeso fiyeda komai da rayuwarsa. Kallan Ayanah yayi a natse ya Lumshe ido akanta ya sake budesu akanta kafin ya bude Baki cikin mulkin dayake yawo jininsa shima da sautin daya shigeta yace ‘HAYATEEM dinki Zaki me BOYEM ya dawo gareki a matsayin cikakken namijin da BOYEM ke buqata’ Motsa idanuwanta tayi akansa tana Jin maganar tasa ta sauka cikin hankali da tinaninta harma da gangar jikinta dan haka ta motsa tana tashi Zaune da kyau duk da bata karfi ko kadan sbd rashin lafiyan datake cinta, Juya kanta tayi ahankali zuwa kofar ficewa bedroom din nata datake ciki daidai nan sultan ya kashe wayar yana jinginar da bayansa ga lafiyayyar kujeran dayake Zaune ta bedroom dinsa tareda dake rufe idanuwansa ahankali zuciyarsa na yin dum tareda shiga tinanika da dama. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 53 Ahankali tafara Takawa tana nufar kofar bedroom din nata idanuwanta na kafe kofar da idanuwanta tanajin jikinta na qara rasa karfinsa da kuzari, Duk takunta daya nauyi kirjinta qaruwa yakeyi ta daga hannunta da baida karfi ta Dora a kirjinta tana dafe sa sbd kaman gangar jikinta bazata iya daukan nauyinba Wanda tsawon shekarun tana jinsa amma Ayau yayi tsananin da jikinta ke sake sakewa ta isa kofar ta zubawa hannun kofar idanuwanta da sukai jajir a take batareda tasan menene takejiba a yanxu kuma, NUAB kuwa tinda ya doso bangaren bayin dake hanyar gabaki dayansu suke zube qasa kansu na yin qasa dan idanuwansu
🏠