NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 109 of 146

cikin Masarautar BOYEM wannan sautin yake tashi waye ya shigo masarautar da sautin dawowan jinin BOYEM yake tashi yana wargaza baccin dukkanin mai rai dayake masarautar ba bayi ba bamasu mulkinba…… Zuro kafafunta qasa tayi zata miqe tsaye Aslam da bata gani sosai sbd mummunan tashin hankalin data shiga da sanarwar da itamaa a cikin baccinta taji saukar sautin ta miqe tsaye zuciyarta na harbawa da Wani irin karfin gaske dan kuwa a yanzu kaf duniya idan ba sultan ba baa buga wannan qarar sai kuma Wanda yakeda matsayi da ikon mulkin BOYEM dan haka a duniya kaf yanzu ASIM ne kadai zaayi wa wannan karar sai kuma ‘dan da har abada bazai taba dawowa BOYEM ba, To idan sultan da ASIM duka suna cikin masarautar waye zaa bugawa wannan sautin idan ba Wanda baya nan ba kenan shi dinne ‘dan mistress din BOYEM ya dawo Bayan shekaru masu yawa. Jin Aslam tayi tana Neman rasa ganinta sbd shock da mamaki mai girma dan kuwa kwana da wuni sukeyi tareda kowace daqiqa ta rayuwarsu suna rokon Allah ya hanasa dawowa Masarautar da rayuwar sultan har abada dan haka ayanzu datake kasa yadda da shi dinne ya dawo doguwar Rigar sarauta me fadi da tsayi tareda adonta janyo ta Dora Akan Kayan baccin dake jikinta ta nufi kofa ta fice zuwa bangaren mahaifiyarta da a lokacin take tsaye tanason daga kafafunta zuwa toilet amma komai nata yayi nauyi takeji hakama kwata kwata kanta ya kasa dauka ko kawo tinanin LEUL BOYEM zai taba dawowa Masarautar BOYEM din sbd an tabbatar mata da babu alkhairi ko kadan a dawowansa gareta da zuriarta dan haka bata taba yin qasa a gurin aikin da har abada bazai taba dawowaba amma alamu sunata nuna hakan bazai samu ba dan haka aiki akeyi tuquru Akan mahaifiyarsa bazata taba shaawan dawowansa ba zataita hanasa dawowa duk kuwa yanda take Jin tsananin so da kewansa bazata iya bude Baki tace ya dawo ba dan haka wannan ya saka hankalin HAILE kwanciya koma dai menene su samu ASIM ALMAZZ ya hau mulkin BOYEM idan ya hau ko yaushe NUAB ya dawo din sun sai riga sun samu abinda suke so buri ya cika. Aslam na isowa Kai tsaye bedroom din mahaifiyarta ta nufo jakadiya dake palon karshe na hutawan HAILE tana bawa masu gyaran palon umarnin tsarin da zaa sauya cikin girmamawa ta kalli Aslam din zata gaidata amma ko ganinta Aslam bataiba ta wuce ciki Kai tsaye daidai lokacin da HAILE ta isa kofar toilet din mai girma da tsari zata shiga, Shigowan Aslam ya saka Hailen dakata wa cikeda mamaki mai dan girma idanuwanta Akan Aslman din sbd ganin lokacin da Aslam din ta taho Bude Baki tayi zatai magana Aslam ta rigata da cewa ‘Ya dawo, Shine ya dawo Bayan shekaru Mamee, Ya dawo Masarautar BOYEM, ‘Dan mistress din Sultan ya dawo Mamee, Ya dawo a daidai lokacinda muke kokarin ganin mun cimma burinmu kota yaya, Mamee tayaya zaki kawar da sultan daga duniya ASIM ya hau mulki a yanzu wannan yana masarautar? Tayaya zamuyi aure yanzu? Tayaya komai zai tafi yanda mukeso a yanzu da wannan din ya dawo? Tayaya sultan zai bar duni…….. Wani lafiyayyan mari HAILE ta sauke mata cikin kidima da rikicewa zuciyarta na wata irin rawa sbd gabaki daya Aslam wata irin mahaukaciyar zuciya ne da tinani da ita, matiqar zata shiga tsananin baqin ciki da bacin rai haka zata ringa tona asirin zuciyarta cikin tsananin baqin ciki da Zafin zuciya dayake fiddata hayyacinta dan hakanne ya saka haile bata barinta magana koina sbd zata iya aikata kuskuren da zaiyi karshen rayuwarsu gurin magana idan takai maqurar bacin rai, Marin da HAILE tayi mata ita kanta hayyacinta barin jikinta yakeyi da abinda Aslam din ta fada dan kuwa bazai taba yiyiwa ace NUAB ALMAZZ ya dawo Masarautar BOYEM din ba dan haka tafi yadda da sultan ne ya fita kila ya dawo batareda saninsu ba dan haka Kai tsaye toilet ta fada kafafunta na dan rawa hakama zuciyarta na tsalle. Alwalar sallar asuba zatai amma gabaki daya ta rikice hannuwanta rawa sukeyi bata Kama ruwa ba alwala tayi ta fito har lokacin kafafunta rawa sukeyi zuciyarta data kasa yadda da abinda Aslam ta fada amma sai bugawa takeyi sosai tana Jin batada Sauran nutsuwa idan zuwa tayi ta tabbatarda waye ya shigo akai wannan sanarwar. Kallan Aslam dake Zaune cikin matsanancin yanayi tayi zuru ta bude Baki tace ‘Kije kiyi sallah zan tabbatarda me yake faruwa idan na kammala komai da kaina zan tafi gurin sultan dan tabbatarda komai.’ Miqewa Aslam tayi batareda tace komai ba sbd jikinta dayake matiqar a sanyaye babu kowace irin kuzari a tattare da ita dan kuwa a duniya babu abinda zai iya kashe zuciyarta lokaci daya ta buga irin ace bazata samu cikar burinta na aure ba Wanda shine maqasudin ragewansu Akan ASIM ALMAZZ ya hau mulki, A yanzu rana tsaka idan NUAB ALMAZZ ya dawo BOYEM tabbas zasu samu babban katangar da zata iya shiga tsakaninsu da burinsu duk da bawai yadda zasuyiba zasu iya aikata komai Akan cikar burinsu ciki kuwa hadda kawar da rayukan wainda baa taba tinani ba. Ficewa Aslam tayi zuciya da gangar jiki ba nutsuwa hakama HAILE tada sallarta tayi itama zuciyarta ba
🏠