NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 106 of 146

ta a basa ita kawai shine cikar duk wani burinsa na rayuwa Bayan hakan baya buqatar komai a rayuwarsa. Saukar muryan Maa sakinah a kunnuwansa ya sakasa bude idanuwana jajir yana bude baki a natse da kulawa yace ‘Maa akwai abinda yake faruwa ne?? Akwai abinda ya kamata na sani ne?? Amminah na da damuwa ne? Akwai abinda yake faruwa a masarautar ne daya taba Amminah? A Jere ya jerowa Maa sakinah tambayoyin da suka saka jikinta sanyi ta sauke ajiyan zuciya mara karfi tareda bude Baki cikin nutsuwa ta manyanci tace ‘Babu komai dayake faruwa kawai dai yanayi ne na kewanka datake yi shine kadai ya saka amma ka damu babu abinda yake faruwa’ Shiru yayi itama Maa sakinan yana karantar yanayin muryanta datai sanyi sosai, Kai tsaye yace ‘Maa akwai abinda yake damunki kema? Menene yake faruwa a masarautar nan? Waye ya tabaku? Katsesa tayi da sauri tana kokarin daidaita kanta cikin sauti da dan sauri sbd Jin yanda muryansa ta fara sauyawa tana daukan Zafi da fushinsa da babu me iya kashe wutarsa tin yana yaro tace ‘Babu komai Ka yadda da hakan LEUL,kada Ka bata ranka ko kadan dukanmu muna cikin kwanciyan hankali da lafiya’ Kasa nutsar da zuciyarsa dake daukan zafi yayi ya bude Baki cikin sassauci yayi sallama da ita Kai tsaye wayar Maa tenya ya kira yana bude idanunwansa da sukai jajir Akan Agogon dayake palon dan kuwa matiqar yaji ya tabbatarda akwai damuwan dasuke ciki babu abinda zai Hana jirginsa sauka BOYEM kafin fitowan alfijir din asubar gobe. Maa tenya dake dakinta ta gama sallar nafila wayarta dake kan marble center table din dayake lafiyayyan dakinta da babu duniyar da babu a cikinsa koina na Qamshi da sanyin ac tafara ringing. Hannunta ta miqa a sanyaye ta dauki wayar tareda dauka ta Dora a kunnanta cikin sanyi tayi sallama tana miqa masa gaisuwan data zama kaman dole kasancewansa jinin BOYEM kuma asalin magajin karagar mulkin. Bai amsa gaisuwan sarautarsa ba ya miqo mata tasa gaisuwan ta zamanta uwa a garesa kafin ya Dora da cewa ‘Maa idan akwai abinda yake faruwa ki sanar dani sbd ina rasa hankalina anan sbd Amminah akwai abinda yake damunta kuma Inason saninsa koma menene’ Ajiye Numfashi me sauti sosai tayi kafin ta sake shiga sanyi da nutsuwa tace ‘Allah ya qara maka lafiyar zuciya LEUL BOYEM Amminka jikinta yana Neman dawowa sosai a kwanakin nan rikicewa kawai lafiyarta ke kokarin yi Wanda tabbas tana buqatan ganinka takeso kafin ta qarasa rasa cikakken hankalinta ta manta waye Kai………. Shiru da tsit yaji duniya gabaki daya tana masa sai yanajin muryan Maa din tamkar sautin dayake tahowa daga nesa sbd straight zuciyarsa labarin ya caka yanajin dumi na gauraye jikinsa koina musamman idanuwansa da sukai jajir. Kasa iya cewa komai yayi sai sallama da yayi mata yana kashe wayar idanuwansa na tsananta ja ya da dago ya saukewa aleey su dayake tsaye gefe yana jiran umarnin koma menene yakeson Ayi. Kallan da yayiwa aleey Wanda ke kallansa cikeda nutsuwa da girmamawa take aleey ya fahimci umarnin sa dan haka Kai tsaye cikin girmamawa da cika umarni yace ‘Aiit B’ iPad din hannunsa ya daga yafara dannawa yana fidda wayar sa itama ya saka kira yana Juyawa yabar gurin yana fara aikin da baya buqatan bata lokaci dan kuwa kome zai tsaya cak sai LEUL BOYEM ya isa fadar da tasa ce gabaki dayanta. Shi kuwa ajiye wayar hannunsa yayi tareda Dora kafarsa Ka daya a hankali yana jingina bayansa da kujeran dayake Zaune yayi folding hannuwansa duka biyu kirjinsa yana Lumshe idanuwansa ya rufe dan kuwa a yanzu komai na rayuwarsa ya tsaya cak har saiya isa yayi tozali da mahaifiyarsa wadda shekaru masu yawa jikinta bai taba tashi ba sai yanzu Wanda a qasan zuciyarsa yasani dole akwai abinda yake faruwa daya saka lafiyarta fara rawa Wanda yana fatar koma menene ya kasance ba wani ne ya aikata komaiba dan a yanda jininsa ke tafasa komai zai iya faruwa Akan koma waye. Dayar wayar ce ta fara ringing Wanda ya sakasa miqewa tsaye ya isa bakin makeken Windownza mai tsare da lafiyayyan grey velvet smart automatic curtains ya zubawa waje idanuwansa da a wannan lokacin da zai sauke maka su zaka iya zubewa qasa kan kafafunka gabansa batareda Ka sani ba. Aleey kuwa yana ficewa daga palon nasa lafiyayyan palon dayake hade da babban bedroom dinsa ya nufa ya fara wayo yi yana aika wasu sakonnin ta iPad Akan tafiyar da zaa hada batareda bata kowane irin dogon lokaci ba ko tashin hankali da hayaniya kawai dai umarni ne da zaa cika a cikin lokacin da sai Wanda ya isa yake iya samun cikawar hakan a qanqanin lokaci. Wuni guda aleey bai zauna ba bai bata kowace daqiqarsa Akan komai ba Bayan shirin hada tafiyar isar LEUL BOYEM zuwa qasar BOYEM din tareda manyan GHAZss dinsa da baya tafiya koina saida su sune manya a cikin kaf Yaransa da kaf duniya bayan aleey daya san kowanne qanqanin sirrinsa da komai na rayuwarsa sune amintattun dan haka aleey baida Sauran kowace nutsuwa saiya gama tabbatarda komai na tafiyar ta kammala a cikin lokacin da uba
🏠