e
50
Gashin jikinsa ne suke qarasa miqewa ahankali maganarta ta ratsa kunnuwansa zuwa kwakwalwan kansa da zuciyarsa data tsaya cak gurin bugawa,
Numfashi me sanyi mara sauti ya sake a natsensa dan gasgatar da maganar Ammin tasa da bata taba raayin dawowansa BOYEM ba haka kawai amma Ayau kunnuwansa na jiye masa sabanin kalamanta na koyaushe da kullum,
Bude bakinsa yayi cikin sautin da ita kadai yakewa magana dashi sbd sanyinsa da nutsuwansa yace
‘Ammi,kina buqatan ganina?
Akwai abinda yake damunki Ammi?’….ya qarasa maganar da zallan kulawansa da kaunarsa akanta yana jiran amsarta dan karantar yanayinta dayake cikin sautin muryanta.
Shiru tayi itama acan bangaren nata tana rufe idanuwanta ahankali sbd muryansa dake ratsata a duk lokacinda zata ji muryansa tsananin kaunar danta kaman zata qarasata takeji amma hakanan take daurewa shekaru masu yawa sbd koyaushe zuriyarta na hanata barinsa dawowa sbd kada aci gaba da kiransa dan mistress Wanda ako Yaushe aka ambacesa da hakan har cikin ranta da zuciyarta take Jin radadin hakan musamman data ga sunan yana kokarin zama abin alfaharinsa dan baitaba Jin ciwo ko damuwan abinda ake ambatar sa dashiba amma su sunajin ciwon hakan,
A yanxu zuciyarta takai maqurar kasa daurewa da hakurin rashin ‘danta a tareda ita musamman da zuciyarta take cikin rashin sukuni sosai da Wani irin tsoron da batasan na menene ba dan haka jikinta yake Neman rikicewa sbd ko bacci kwata kwata ta rage sosai Wanda shima yake qarawa lafiyarta illa me girma dan haka su tenya da sakinah suke cikin tsananin damuwa da rashin yaya zasuyi gashi basuda ikon sanar da sultan suke gani tinda bata gabansa babu abinda yake gabansa nata likita dayane tinda ya nadasa mai duba lafiyar Ayanah din shikenan baitaba fasa zuwa bibiyan lafiyar taba koda Yaushe a tsawon shekarun nan,
‘Ammi’ ya Ambaci sunanta cikin sanyi da kauna me girman gaske tareda nutsuwan da bayason damar da ita sbd jinta shiru.
A sanyaye ta sauke bayyananniyar Numfashi jikinta gabaki daya a mace ta bude Baki tace
‘NUAB,Yene HAYATEEM,Yene LEUL idanuwana suna son ganinka,
Zuciyana da ruhina duka san ganinka sukeyi kafin na…..’
Katseta yayi da tsananin nutsuwa da cewa ‘AMMI’ sbd yasan kalman mutuwa ne zata qarasa dashi,
Tsigar jikinsa ne suka sake tashi a hankali Wani irin yanayin da mahaifiyarsa ce kadai ke motsa zuciyarsa na ratsashi sbd ya tabbatarda akwai abinda yake damunta ko zuciyarta dayayi girman datake buqatan ganinsa harta furta da bakinta,
Dole wata damuwarce take faruwa da kila batasan tayaya zata iya gane wa ko fada masa ba kawai ta buqaci ganinsa sbd zuciya da ruhinta su sanyaya,
Numfashi mara sauti ya kuma saukewa tareda dagowa idanuwansa farare tas masu Kayar da gaba da suka sauya a take suna dan rikida da ja ya bude Baki a natse yace
‘Ammi bakida lafiya ne?
Girgiza masa Kai tayi a hankali da sanyi kaman yana kusa da ita Wanda sautin ya shigar masa kunne a cikin sanyi dan haka ya rufe idanuwansa ahankali ya kuma bude su yace
‘Akwai abinda yake damunki Ammi?
Nan ma girgiza Kai tayi a natse batareda tinanin ba lallai ya fahimta ba,
Nan ma yaji Gyada kan sbd akwai yan kunnen zinari masu dan fidda sauti kadan a kunnuwanta Wanda ya saka idan ta girgiza Kai sautin su ke shiga kunnuwansa suna narkar da zuciyarsa da babu abinda take tsananin so da kauna a duniya idan ba ita din ba
‘Ammi akwai Wanda ya saka miki damuwa’
Girgiza Kai tayi ya sauke Numfashi me sauti wannan Karan ya bude baki zaiyi magana muryanta ta Katsesa a sanyaye tace
‘Idan zaka taho kazo da Abaas,ina son ganinsa HAYATEEM’
Rufe idanuwansa yayi a Wani irin yanayin da zuciyarsa ke cizo da radadin kasa bawa macen da ita kadai ce rayuwansa abinda takeso sama da shekaru masu yawa.
‘Ammi zan taho gareki ba tareda Abaas ba amma nayi miki alkawarin indai Abaas yana raye zan kawo miki shi a gabanki,
Nayi miki Alkwarin indai Abaas yana raye zan Nemo miki shi zai qarasa rayuwarsa a gabanki bazai taba barin gabanki ba har sai mutuwa ta rabaku…..
Wasu hawaye ne suka gangaro idanuwanta da suka saka hankalin sakinah dake tareda ita a palo Zaune tashi sbd bata kuka Sam a yanzu sbd kuncinta da baason ya dawo dan haka a natse ta iso gurinta ta zauna gefenta ta kalli wayar hannunta ta miqa hannu tace
‘Nima zan gaisa dashi’
Miqa mata wayar Ayanah tayi cikin nutsuwa tana cewa ta yadda da NUAB zai cika mata wannan alkawarin ko Bayan ranta ne zai nema Abaas.
Maganar tata har kunnuwansa ta sauka ta shigesa a hankali ya Lumshe idanuwansa yana Jin wata wuta mai Zafin gaske tana kunnuwa a zuciyarsa ta son kasancewa da mahaifiyarsa da tabbas lokaci yayi da zai dawo da ita hannunsa dan kuwa daman magana daya ce duk ranar daya saka kafa a BOYEM to bazai taba tafiya batareda mahaifiyarsa ba,
Babu me buqatarta a masarautar da qasar gabaki daya hatta Wanda take zamansa baya buqatanta ya watsar da ita tin tanada kuruciya dan haka shi babu abinda yake buqata a rayuwarsa sama da i