da idanuwansa idan ba iyayensa mata ba sai kuma ubansa dabai San yaya zai kallesaba tinda basa tare shekaru.
Izzar dayake bugawa da iko tareda taqama da tsananin power dayake Juyawa da ita sun hadu hade ne da jinin dayake yawo a jikinsa na sarautar BOYEM,
Duk wannan shekarun yayi su ne yana jiran ranar da Amminsa zata furta masa ya taho ta janye kamalanta na kada ya dawo,
Daga ranar da Amminsa ta furta masa tana son zuwansa to tabbas a ranar bazai kwana ba sai jirginsa ya saukesa qasar BOYEM hakama bazai Baro ba saiya tabbatarda uwarsa ta dawo hannunsa.
Wannan kiran shine kiran dayake jira daga mahaifiyarsa kowace daqiqa dan haka aleey ma koyaushe a shirye yake tsaf da jiran kiran ya shirya saukar su BOYEM da me BOYEM din gabaki dayanta duk da baya buqatan mulkinta.
Villa dins datake kamar gari guda kusan fiyeda rabin Yaransa dake Russia suna cikinta bangare daban daban Sauran yaran nasa kuwa suna qasa daban daban inda yake da companies dan haka villa din akwai tsaro mai tsari da rashin hayaniya,
Duk Wanda yake karkashin GHAZss baya cikin wahala ko talauci Bayan kwanciyan hankali da rashin hayaniya sai zallar iko da rashin tsoro dan Sam baya kaunar lusari ko sakaran namijin da bazai iya tsayawa namiji ya cire tsoro a zuciyarsa ba a karkashinsa dan hakanne ya kasance duk Wanda yake karkashin GHAZss babu Wanda ba tsayayyen namiji mai zarra ba hakan ne ya saka koina suke kwarjinsu daban yake bare ace uban kwarjinin nasu na guri.
*******
Hayaqi ne da qamshi yake fitarwa me nutsuwa yake cike da gauraye toilet din mai tsananin girman da koina daukan ido yakeyi sbd kyallin tsaddan luxury vinyl tiles da komai na Duravits toilets dayake tsare a toilet yana saka jikin duk Wanda ya kalla mutuwa,
Qarar shower ce yake tashi a cikin luxury steam and sauna shower room dake cikin toilet alamar wanka akeyi da ruwan dumin da hayaqinsu yake bada qamshin shower gel dinsa na the Noir,
Tsawon mintina a ciki kafin ya kammala
Hannunsa me tsananin haske da lafiyar fata ya bude kofar kafin kafafunsa suka fito ya fito gabaki dayansaa ruwa na gangarowa daga lafiyayyar farar fatarsa da Hutu da lafiya kawai take bayyana wa tana daukan ido,
Ruwan ko zama basa yi a farar fatarsa Kal sbd santsi da lafiyarta gangarowa sukeyi kawai suna sauka qasa.
Gurin da towels suke a Jere a tsare kaman bundles na kudi ya nufa ya miqa hannunsa daya ya dauko daya ya daura a kuqunsa kafin ya sake daukan daya a natse cikin asalin nutsuwan sarauta dake yawo a jininsa ya Dora a kan gashin kansa dayake tamkar na mahaifiyarsa yafara gogewa ahankali kafin ya fito sanye da fararen soft sole bedroom slippers yana nufar makeken dresser mirror din dayake closet dinsa mai girman dayafi na daki biyu dan kuwa tarin sutura ce a Jere da basada adadi babu kalar designer din data amsa sunanta da babu a gurin tin daga kan bangaren agogunansa da suke bugun mahaukatan dollars har zuwa kan takarman sakawansa da suke cin manyan kudi da bangaren wandunada shirts da suits da underwears hatta ties na wuyansa da socks dinsa kowanne da bangarensa daban inda aka jerasa.
Ga turaruka suma da pins da combs nasa suna kowanne baida adadin number dan babu abinda ake siya kadan hakama akai akai ake qaro wasu Ana jibgawa.
Cikin nutsuwa da rashin hayaniya ya shirya tsaf a cikin navy blue loro pianas vicuña polo shirt da Michael kors trousers fari tas ya komai na jikinsa na fidda wani tsadadden qamshin Gaultier elixir na yana gauraye niimar duk inda ya wuce da inda yake tinkara a cikin sanyi.
Palonsa na hutawansa y wuce Kai tsaye cikin nutsuwa zuwa palon da dining room dinsa yake inda zaiyi breakfast da aka gama cike dining din a tsare da aji,
Tin daya doso qamshin sa ya sanar da aleey fitowan sa dan haka ya miqe daga Zaunen dayake riqe da iPad me girma dayake wani aikin report da aka turo daga kamfaninsu dake Brazil.
Ajiye iPad din yayi yana dago Kansa ahankali ya sauke Akan hanyar da NUAB ALMAZZ din daya fito kwarjinsa da Kyansa dayake sake cika idanuwan duk me kallansa na cike gurin gashinsa dayaji tsadaddun mai yana sake a kafadarsa ya dago idanuwansa da babu abinda suka Baro na mahaifinsa ya Dora Akan aleey din yana qarasowa kenan wayar sa da iya mahaifiyarsa kadai ke kiransa da wannan layin tayi haske tana ringing mara qara.
Dago wayar da hannunsa yana dakata wa cak ya fasa isa dining din ya isa kan wasu mahaukatan luxury sofas dake palon ya zauna a natse tareda ajiye Dayar wayar hannunsa a gefensa kafin ya daga wayar cikeda nutsuwa da kulawan da baya bawa kowa duniya sai ita ya bude Baki muryansa mai tsantsar nutsuwa da Izzar sa da bata boyuwa yace
‘Ya Ammi….
Katsesa maganarta da muryan data tada tsikar jikinsa gabaki daya da cewa
‘HAYATEEM Inason kasancewanka a tareda ni duk lokacinda Ka samu daman hakan……
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhge