a mintina biyu batareda ya cika umarnin ba,
Duk abinda NUAB ALMAZZ yake so ko menene shi aleey yake so ba me kyau bane kuwa hakama abinda NUAB ALMAZZ yakeso to aleey yana sonsa da dukkanin rayuwarsa dan hakanne burin Ammi ya zama qudurarren burinsu da dukkanin Wanda yake qarqashinsu na Neman Abaas a duk duniyar dayake koda hakan na nufi zasu juya nahiyoyi da dama.
Tin daga kan aleey NUAB ALMAZZ ya zama gatan kowane mara gatan,
Sama da daruruwan yan taaddan qasashe daban daban da kaddara ta sakasu fadawa taadanci da shaye shaye NUAB ya tallafi rayuwarsu ya sakasu jikinsu ya kawo sauyi a rayuwarsu suka zama Yaransa cikin sauyawa zuwa masu abin yi,
Duk Wanda bai gama karatu a cikinsu yana sakasa ya qarasa karatunsa ya fara aiki a qarqashin sa wainda kuma Sam basuyi karatun ba suma aikin da zasu iya a duniyarsa yake sakasu dan haka kusan duka wainda suke a qarqashinsa ire irensu ne amma kuma ilimin sosai suke samu dayake ratsa su sun zama yan business din gaske da kamar da saa kowannesu yake yawo dan kuwa tako ina cigaban GHAZ empire ake samu,
Tamkar zakuna suke a cikin duniyar manyan business tycoons sbd tsananin ilimi da saarsu harma da qwanjinsu dayake bayyane Akan zasu iya komai akai ubangidansu da ayanzu kusan koina duniya ta sansa sbd tarin yan amanarsa kuma yan taaddansa dan duk da sun sauya rayuwa sun taka matsayin cigaban rayuwa wannan rayuwar ta rashin sauki da rashin tsoro yana nan a tattare dasu,
Ilimi da kudi tareda power da suke samu daga shugabansu NUAB ALMAZ ya qarawa rashin tsoro da zuciyarsu kafin gaske da basa shakkar komai da kowa a duniya idan ba shi dinba da babu Wanda baya sauke masa Kai idan ya fito sbd girmamawa dan shine ya jasu cikin jikinsa da dukiyrsa ya maidasu mutanen da kowa yake shakka a yanxu dan haka duk da wasu sun girmesa wasu kuma tsarin shekarunsa ne da wainda ma ya girma gabaki dayansu a uban dayafi kowane uba daraja kimar da zasu iya tasa yaqin duniya akansa suke kallansa,
Tsoronsu akeyi shakkar su akeyi sosai sbd uba gidansu yana dukiyar da suke juya duniyar yanda suke so,
Kusan dukkanin yaran nasa babu Wanda baiyi zaman gidan yari ba sbd rashin adalcin sharia amma ayanzu sun Kai sun taka matsayin da koda a gaban mutane zasuyi Kisa babu Wanda zai dago ya kallesu amma kuma ba irin rayuwar suke yiba yanzu dan kuwa business suke me tsafta da class da tsari amma duk da hakan kallan yan taadda masu karfin gaske ake musu Ana tsananin shakkarsu.
Yaransa sune yan uwansa,
Sune danginsa,
Sune yake shiga cikinsu yayi nutsuwa ko babu hayaniya sune ahalin da suka cike gurbin ahali da dangin da baida kaman yanda shima shine ya cike gurbin iyaye da yan uwan jini da suka rasa dan haka Bayan komai akwai kauna mai tsananin karfi a tsakaninsu dasuke wa juna su dashi,
Iya kafuwa da tsayuwa GHAZ empire ta tsayu,
Manyan qasashe da Masarautu ne da manyan tycoons na karshe ne abokan huldarta dan hakkanne NUAB ALMAZ yayi suna da fice a duniya da yake da Wani irin matsayi da girman gaske a idanuwan duk wani marasa karfi da galihu,
A cikin abokan huldarsa kuka shi din Zakin dayake yawo ne da saa a rayuwarsa,
A gurin tarin yaransa da uwansu ya kere na Masarautu da dama shi sarki ne da a duniyar nan idan yace A to A dince idan yace kuma B ce to dince kawai ko uban kowa ya yadda ko kada ya yadda,
Shi sarki ne da ko masarautar ubansa yace su tayar bazaa kwana ba saisun saka jini gudana a cikinta ta shefe kaman baayi kowa a cikinta ba.
Duk suna da tambarin da ake masa Akan zamowa gatan yan taadda bai taba bawa ko yan jarida daman fira dashi ba Akan hakan sbd baya buqatan yiwa kowa a duniya bayani kawai dai yasan yana samun feelings na nutsuwa daga sauya musu rayuwan da yayi hakama kusan yanajin radadin daya sauya rayuwarsu zuwa ga illa sbd yasan ciwo da radadin abubuwa ire iren wainda suke tinda shima tin da qananun shekaru aka rabasa da tasa uwar da haryanzu baiji dumin jikintaba taji nasa,
Fushi ne a zuciyarsa da haryanzu bai huceba,
Zafi ne a cikin kansa da haryanzu wutarsa bata mutu ba,
Qiyayya ce me karfin gaske dayake wa jamaar Masarautar BOYEM da haryanzu bai sauka ba sai ranar da mahaifiyarsa ta shigo hannunsa ne kadai komai zai iya fara sassautowa.
Duk wani Zafi da fushinsa a zuciyoyi da kan Yaransa take ci batareda sun San menene a ransa ba dan haka iya gane menene zuciyarsa amma dai tinda suka sansa sukasan da wannan wutar dake ci a cikin idanuwansa dan haka tasu zuciyar da ruhin basu taba Dena ci da wutar Zafi ba da jiran kowane umarnin sa Akan koma menene ba.
Duka wannan rashin tsoron da rashin shakkar da GHAZs kaman yanda ake ambatar su sbd sunan komai nasa daya mallaka a rayuwarsa sunan mahaifiyarsa ne amma iya GHAZ din suke dashi sun samo izzar hakan ne daga ubangayyarsu LEUL NUAB ALMAZZ da babu sunan shakka ko tsoro bare fargaba a cikin littafin rayuwarsa datake tsaye cak kaman mashi,
Komai Zafi da rashin saukewa kowa Kai a duniya idan ba shi ba basu kamo sa ba ya dame dukansu ya shanye babu Wanda kaf duniyar baya iya dagowa ya kalla