NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 101 of 146

qura musu ido ta ringa kiransu da Zuhrah da Nurat tana hawaye tana rintse ido sbd ciwo da radadin na taso mata a kirji da baa son kwata kwata taba tinawa da wannan kuncin sbd lafiyarta da kome zai iya faruwa idan wannan quncin da baqin cikin ya dawo mata cikin kwakwalwa dan hakanne kwata kwata Bayan kokarin kulawa da sake mantar da ita komai babu abinda su tenya ke kokarin yi, Baa iya zuciyar wishmah sukeda matsayi me girma ba a zuciyar NUAB ALMAZZ su din taurari biyu ne da bazai taba iya biya ba har qarshen rayuwarsa, Su din haske ne a rayuwarsa da suka bawa halittar datafi komai na duniyarsa daraja kulawa da tattalin datake buqata a lokacin da bata kowa a duniya Bayan shi kadai kuma aka rabasa da ita, Sun kular masa da ita tin baizo duniya ba harma Yazo duniyar ya zama abinda ya zama yanzu Amma haryanxu sune suke tsaye akanta Bayan Wanda take full responsibility yayi watsi da rayuwarta batada amfanin komai a rayuwarsa baya buqatanta bayin matarsa ma sunfita daraja. Bayan zallar kauna mai girma da darajar su dayake gani matsayin iyaye mata da tamkar sune suka haifesa yake basu dan hakanne kowacensu takejin sa Aranta tamkar itace ta haifesa musamman sakinah da bata taba sanin menene namiji ma bare haihuwa dan haka take Jin LEUL NUAB tamkar dan data haifa da cikinta hakama tenya dake da yaya biyu mata da tini sukai aure basa masarautar jinsa tamkar ‘da namiji da Allah bai bata ba, Da wannan rayuwar bangaren wishmah AYANAH samun nutsuwa da kwanciyan hankali a tsakaninsu da bayinsu gida bakwai dake hidimar bangaren komai nasu a kebance hankali kwance da nutsuwa, Basu taba damuwa da komaiba a yanzu da komai na masarauta tinda komai baayi dasu sun koma kamar babu su, Sultan ya yafe wishmah bata ma cikin masu zuwa tiraka tin shekarun da suka gabata hakama babu wata hidimar dake tasowa ta fito sbd yanayinta, ‘Danta da ake tinanin matsayinsa a Masarauta shima baya nan dan haka basa lissafi Sam idan ba tozartasu zaayi ba baama ambatar su dan haka suka zama bangaren dayafi kowane bangare shiru da rashin hayaniya, Tenya tini ta rasa matsayinta sbd anrufe karban imebeti dan haka Kai tsaye ta koma tamkar yaya kuma jakadiyar wishmah da LEUL da babu ranar dawowansa. Tinda NUAB ALMAZZ yabar qasar boyem tsawon shekarun sultan YASAR baitaba maganarsa da kowa ba kaman yanda bai taba Nemansa ba hakama NUAB din kansa bai taba Neman mahaifinsa ba sbd sun rabu Akan zazzafar zuciyar dake cin kowannesu ta jini daya dake yawo jikinsu, NUAB ya tafi da Wani irin ciwon da har abada bazai barsa ba wato ciwon ganin idonsa yanda mahaifinsa ya wulaqanta masa mahaifiya batareda tinani da tausayin ciwon datake rayuwa a cikinsaba, Ya tozartata ya bawa duniya da dabbobin dake duniyar harma da ‘yayan dabbobin tozartata, Littafin tarihi ya buga sunanta a matsayin daba kowa ba face mistress din da batada kowane irin muhimmanci da daraja a Masarautar da a gurinsa takarmin Ammin tasa ya fita daraja a idonsa da zuciyarsa, Duka wannan bai isa ba saida ya rabata da ‘danta tareda saka dokar karya taba dawowa masarautar saiya gama karatunsa duk sbd a quntata rayuwarta….. Da wainnan abubuwan waye Sultan din da zaiyi fari a zuciyarsa? Bayajin laifin mahaifiyarsa ne data zo a matsayin imebēti zuwa wishmah dan haka babu Wanda duniya ya isa ya wulaqanta masa uwa batareda ya takasa ya shayar da nasa dabbobin jininsa ba Bayan mahaifinsa Wanda shima daraja ce da girmansa na uban dayayi cikinsa aka haifesa yake ci amma kaf boyem babu Wanda bazai iya tara jininsa a pool yayi wanka dashiba indai Akan wishmah AYANAH GHAZ ne. Bayan gama karatunsa sultan dayake biye da kowane irin motsinsa a rayuwa jiran dawowansa ya fara yi sbd ya zama abinda yakeson ya zama din wato mai cikakken tarin ilimi da rashin tsoro da Izzar dake yawo jininsa amma ga mamakin sultan mai girma NUAB ALMAZZ babu boyem a ransa ya shafeta kwata kwata har abada bai niyar dawowa dan babu ita a ransa ya cire, BOYEM bata cikin abinda yake da shirin dawowa a tsari da qudirin rayuwarsa mai karfi daya shirya. Wata irin rayuwa mai karfin gaske da power data fara saka zuciyar sultan nauyi NUAB ALMAZZ ya fara ginawa a Russia wadda ta fara bayyanar da irin karfi da power din dazaiyi wadda hakan zata ma iya zama hadari da boyem sbd babu ta yanda boyem zata zama Abokiyar gaba ko fada da ‘dan daya fito daga jininta. A zuciyar NUAB ALMAZZ ya jima da goge boyem a rayuwarsa dan kuwa tabbas baida niya ko raayin komawa har abada aransa, Baida kowa da komai da zai sakasa komawa Bayan Amminsa wadda yakeda kudirin daukota ya dawo da ita hannunsa itama tabar BOYEM kenan har abada, Duk Wanda yake duniyarsa yasan alaqa daya ce ta rage wadda ta liqesa da Masarautar boyem wato mahaifiyarsa dake hannun masarautar haryanzu, Buri da babban qudurinsa dazai qarasa yanke masa boyem a rayuwarsa shine Amminsa ta kasance a hannunsa to daga ranar ko sunan boyem bazai sake bayyana a cikin sunansa ba bare wata bayyananniyar alaqa….. Sultan YASAR ya dade da sani da fa
🏠