NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 100 of 146

uma mazan ne kadai basada ikon auren macen daba jinin ahalin ba amma matan Ana aurar dasu wani gurin kuma Sam baa taba yiwa macen datake jinin BOYEM auren tilas saida cikakken raayinta sbd zataje ne qasar daba tata ba idan akai mata tilas zata rasa ahalinta kuma taje tayi qunci dan haka basa tilas tin farko ga matan boyem, Wannan dalilin ne ya saka yayan nata suke Zaune masarautar mahaifinsu haryanzu hakama a tsaye suke qyam Akan tabbatarda karban mulkin dan uwansu Wanda tsufa ya kamasu a gida batareda sun ankare ba takai sultan ya rufe kofar Neman aurensu kwata kwata hukuncin su sai ranar da aka nada sabon sultan a Masarautar BOYEM shine zai bude musu kofar Neman aurensu daya rufe, Hukuncin ya rikitar da rayuwarsu kwata kwata ta juye ta zama baqin cikin da babu Sauran hasken sauki a cikinsu sai zallar rashin imanin yadda da hakura daga abinda suke so dan kuwa indai wannan hukuncin dake kansu zasu jira to ko zasu kashe rai nawa suma saisun tabbatarda ASIM ne ya zama sultan dan kuwa idan ba shidinba ya hau babu me dauke wannan hukuncin zasu tsufa su mutu ne ba aure dan haka babban burinsu na rayuwa Akan tasu dalilin na tsananin son aure ya karfafa kudirinsu Akan hawan ASIM boyem dan yanzu wannan ne ma babban dalilinsu na jajircewa, Ita kanta queen HAILE wannan shine dalili na biyu me karfi daya sakata tsayuwa Akan qudiri daya na tabbatar da ASIM ya karbi mulkin boyem sbd ganin yayanta zasu suna shirin tsufa su mutu babu aure ga qanwarsu neesat dake aure Masarautar Malaysia yayanta hudu babban ‘danta ma yana kokarin shiga university amma su Sauran suna gida manyanci yana sako musu Kai dan kuwa shekaru ashirin ake magana yanzu ko Bayan Barin NUAB ALMAZZ kasar idan aka hada da shekarunsu na baya ma suna hararar shekarun da suke Neman na wuce aure ma. *******wishmah Ayanah tinda ‘danta hasken idaniyarta da zuciyarta ya tafi bata taba sake walwala ba a tsayin shekarun nan, Bata taba manta tsananin soyayya da kaunar datake masa ba kona daqiqa daya, Bata taba manta kamanninsa ba, Bata taba dena kewa da tsananin son ganinsa ba duk da babu ranar da baya wuni kiransu akai akai yana video call da itaba sbd tsananin kauna da soyayyar dayake mata wadda ta zarta rayuwarsa da babu komai a ciki sai emptiness da Wani irin Zafin jinin sarauta dayake yawo a jininsa fiyeda mahaifinsa, Wishmah a hankali taci gaba da manta komai da kowa harta gama mance komai a rayuwarta bata tina komai da kowa Bayan mutane biyar da sune rayuwarta,sune ji da ganinta a yanzu datake tamkar sabuwar haihuwa, Qunci da baqin cikinta sun wanke babusu a zuciyarta sbd Manta komai datai dan haka rayuwarta take simple fayau ba damuwa da tashin hankali Bayan damuwan rashin HAYATEEM dinta da baya tareda ita Wanda shima hakanan koyaushe take rasa dalilin daya saka bakinta yake furta masa kada ya dawo qasar BOYEM Wanda shi kansa NUAB din wannan furucin nata ne ya hanasa dawowa qasar wadda har abada ya fitar da ita cikin ransa baida niyar dawowa rayuwa a cikinta. Mutane biyar da su kadai ne a zuciya da kwakwalwan wishmah sune, Shi kansa HAYATEEM din nata sai Mahaifinsa sultan data kasa cirewa a cikin kanta Wanda duk tsawon shekarun nan babu ranar da shima baya video call da ita kowace asuba sedai bata cewa komai haka zai kira ya zuba mata idanuwansa yana kallanta tana masa shiru batareda cewa komaiba itama tana kallansa harta gaji ta kife wayar tayi kwanciyarta tenya tazo ta dauki wayar ta fice da ita Wanda hakan wani sirri ne da babu Wanda ya sani a duniya daga sultan din se tenya wadda itama ta rasa dalilin sa na hakan a kowace asubar bayan kuma ya Riga ya nunawa duniya wishmah da ‘danta basa gabansa. #MAMUH #LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM #BOYEM LEUL #ALMAZZ NUAB HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 48 Bayan NUAB da sultan YASAR dake zuciyar Ayanah ABAAS ne Wanda bakinta bai taba qasa da kasa fada ba hakama zuciyarta bata taba mantawa da tsananin sonsa da kaunarsa ba hakama bakinta bai taba gazawa da fadawa NUAB yayi mata alkawarin kawo mata Abaas kada ta mutu bata gansa ba ta sake rungumar sa a jikin taba Wanda ba ita kadaiba zuwa yanzu babban kudurinsa na rayuwa ya zama na bawa mahaifiyarsa abinda takeso, Sauran mutum da sukafi kowa zamowa rayuwarta ta yau da kullum Bayan ‘danta da Abaas sune sakinah da tenya da suka sadaukar da rayuwarsu tin daga Sauran yarinta da suke da ita har zuwa yanzu da manyanci ya Kama su dukan sun tsaya da lafiyarsu da lokacinsu da rayuwarsu sun bata kariya da kulawa kuma sun shirya hakan har qarshen rayuwarsu data rage musu dan haka itama duk da a yanayi na rashin memory da rashin nutsuwa da lafiyar tinani sune wainda ta sani kadai a rayuwarta datake jinsu har jini da ruhinta da suka zame jininta koda basu hada jinin ba a yanzu sune asalin jininta datake kalla dan a lokuta da dama idan dan tinaninta da ya hau daidai takan zauna ta
🏠