NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 10 of 146

aune tana Jin rashin nutsuwa, Shiru tayi tana Dora hannunta kan kirjinta dake bugawa sosai cikin rashin Jin dadi, Koma wa tayi ahankali tana kokarin kwanciya taji motsi me karfi daga waje dan haka gabanta ya sake faduwa ta zuro kafafunta qasa da sauri tana saukowa gadon tareda daukan mayafi tana Daurawa akanta ta nufo kofa tana bude kofar ta fito Kai tsaye batareda tsoron duhun Daren ba. Takawa tayi Kai tsaye ta nufi dakin Ayanah sedai kafin ta isa dakin wani irin jan haske taga yana gauraye saman garin na alamar wuta. Saman ta ringa kalla tana nufar dakin sai kuma hayaniyar tashin qara daga nesa Wanda ya sakata qarasawa dakin da sauri tanajin tsoro na shigarta. Tura dakin tayi ta shiga da sauri ta qarasa gadon Ayanah ta haye gadon tana shigewa jikinta ta qanqameta. Cikin bacci Ayanah taji Nurat cikin jikinta wadda tasan itace Kai tsaye sbd itace Kai tsaye take zuwa lokuta da dama cikin dare gurinta idan ta kasa bacci. Numfashi da ajiyan zuciya Ayanah ta sauke tana Shafa kan Nurat din sedai kafin ta bude baki tayi magana aka sake turo dakin cikin wani irin sauri da karfi. A tare suka miqe Zaune cikin faduwan gaba da mamaki, ‘Abaa’ Ayanah ta Ambaci sunan mahaifinsu dake shigowa da qaramin hasken wuta a hannunsa. Nurat ma cikin fargaba tace ‘Abaa’ Qarasowa yayi da sauri batareda ya amsa su ba Amma na gefensa da hasken itama jikinta na tsananin rawan mummunan tashin hankalin da basu taba samun kansu a ciki ba tsawon tarihin GHAZ. Riga me tsananin kauri ya janyo a cikin Kayan Ayanah ya miqa mata cikin kokarin hana mummunan tashin hankalinsa fita sbd kada su firgita yace ‘Saka wannan Ayanah’ Karba tayi hannuwanta na dan rawa tana sakawa akan kayanta tace ‘Abaa meya faru ne?’ Bai amsata ba ya janyo wata rigar ya saka a hannun Nurat dake sake shiga rikici idanuwanta na raurau Amma ce ta taimakawa Nurat din gurin saka rigar Abaa ya Kama hannunsu su biyun ya nufo kofa dasu wannan Karan Amma ce riqe da hasken gaba daya. Dakin Zuhrah suka isa wadda take bacci sosai hankali kwance Cak Abaa ya tadata Zaune Wanda ya sakata bude ido tana sake lumshewa zata zame ta sake komawa kwance ya miqar da ita gabaki daya yana cewa ‘Ayanah samo mata Riga me nauyi sbd sanyi’ Da sauri Ayanah ta nufi Kayan Zuhrah din ta dauko Riga da sauri ta kawo tana miqa masa Da Kansa ya sakawa Zuhrah din yana Kama hannunta itama suka fito. Dakin Abaas suke kokarin nufa wani irin kuka da Ihun mutane mara dadin saurare ya sake tsananta yana gauraye garin tareda qaruwar hasken wutar dake cin garin sosai. Sai a lokacin bacci gabaki daya ya sake su Ayanah suka shiga tsoro da faduwan gaba me tsanani suna kasa ma tambayan meya ke faruwa. Abaas ma baccin yake Ayanah ce tayi saurin isa gurinsa ta tadashi da sauri dukkanin jikinta na rawa. Fitowa sukai Abaa yaja su zuwa kofar baya ta fita gidan ya tura su wani daki tareda dukkanin bayin gidan mata ya kalli Amma batareda yace komaiba ya qanqame hannunta ya kalli Ayanah itama yace ‘Ku kula karku fito saina dawo Idan kuma kunji shiru ban dawoba ku fita ta baya akwai hanyar dana tanadar muku ta barin gari ku bi karku tsaya sai kun fita ruwa gabaki daya kun fada nahiyar yom acan zaku samu rayuwan kwanciyan hankali idan har kuka fadawa sarkin garin ku GHAZ ne. Shiru sukai dukkaninsu Banda Ayanah da Amma da suka riqe hannunsa suna girgiza kai, Nurat da Zuhrah tareda Abaas kuwa cikin tsananin tashin hankali da wani irin firgici suka ce ‘Abaa ina zaka? Karka fita dan Allah kazo mu tafi din bama sai mun jira ba dan Allah Abaa’ Girgiza kai yayi yana kallansu da jajayen idanuwansa da suke rine da tsananin ‘daci da baqin ciki yace ‘Ni shugaba ne ta yaya zan tafi nabar mutane na batareda nasan meya ke faruwa a garin ba…….. Katsesa Amma tayi cikin wani irin mugun tashin hankali muryanta na rawa zufa na tsiyayo mata da cewa ‘Koma menene ba alkhairi bane sbd Ihu da kukan da garin gabaki daya ya dauka ya tabbatarda hakan, Masifa ce da balai a garin yau karka tafi dan Allah ka tsaya’ Zare hannunsa yayi cikin nata idanuwansa na sake kada wa jajir. Cafke hannunsa Ayanah tayi tana fadawa jikinsa ta qanqamesa wasu hawayen tashin hankali me tsanani suna kufce mata a rikice tace ‘Abaa dan Allah karka tafi mu tafi mubar garin tare bazamu iya tafiya koina babu kai ba’ Nurat ma qanqamesa tayi Zuhrah ta fada jikin Amma tana qanqameta Abaas ma Abaan ya riqe yana wani irin rawar jikin tashin hankali da tsoro take ya fasa kukan daya saka Abaan kallansa yanajin tsananin tausayinsa. Banbare Ayanah da Nurat yake a jikinsa suna qanqamesa Ayanah tayi fashewa da wani irin kukan da bata taba sakewaba a rayuwarta tana ambatar sunan Abaan. Fincikesu yayi da qarfi yana hana zuciyarsa karyewa ya turasu jikin Amma ya fice da sauri yana janyo marufin dakin. Rawa da kuka sukeyi sosai Wanda gabaki daya gurin yayi tsit sai sautin kukansu dake tashi ahankali cikin mummunan tsoro,fargaba
🏠