NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 9 of 34

zai yi da ita, kai ko dai in yadda ta ne, tom in kuma fa nayadda ta kuma bata mutu ba fa?" Nan dai ya yanke ma kan shi shawara akan ya kai ta gidansa alabashi yakira alheri ta dubata ta tagani ko tanada rai. Bashi ya isa gida ba sai shida na yamma (6: 00pm) lokacin garin yafara duhu. Yana shiga gidan ya d'akko ta daga mota kasan cewar yana fita gab'ar ruwan yayi parking a inda suke aje jiragan su. Ya d'auki drop d'in mota har gidan sa." Bayan ya kwantar da ita ne nalura she Na'ima ce. Waya ya d'auka ya turama alheri sako tazo yanzu yana son ganin ta. Cikin mintina kad'an alheri ta iso gidan. Alheri kallan shi tayi damamki ta ce, "Abdurrahim wannan fa, ina kasamota?. " Banza Abdurrahim yayi da ita kamar bazai amsa mata ba, sannan ya ce ahankali kamar an mai dole "Tsintarta nayi, ki dubata mana" Alheri da mamaki take kallan Abdurrahim , so take tak'ara tambayar shi amma bataga fuskar hakan ba, dan haka taja bakin ta tayi shiru, ta fara aikin da yakawota. Alheri tad'an kwashi mintina tana dubata, sannan takalli Abdurrahim ta ce, "Abdurrahim k'alau take inajin furgicin da tayi ne yasata cikin wannan yanayin amma bari ina zuwa akwai allurar da zan mata yanzu. Cikin k'ank'anin lokaci Alheri tadawo da allura tayima Na'ima, sannan ta ce mai zata tafi gida. " Ok, thanks" Abdurrahim ya ce ma alheri sannan yazaro kud'i dayawa yabata. Alheri kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Haba Abdurrahima ai kawuce haka aguna, kodai kana kokwanton matsayinka k aguna ne? " Kai Abdurrahim ya girgiza mata alamun a'a t"Tom nagoge" Abdurrahim ya ce mata ahankali cikin natsuwar shi da rashin son hayaniyarshi. Abdurrahim tun da yaba Na'ima awa d'aya bata farkaba kamar yadda alheri tace mai, tashi yayi ya shiga d'akin dake kusa da nata, yayi sallah ya shiga kitchen yayi makan shi abu mai saukin ci, sannan yakoma d'akin da ya kwantar da ita ya kuma dubawa ko ta tashi ,ganin bata tashi ba ya nufi d'akin shi. Cikin tsakiyar dare Na'ima ta farka, da wata irin k'ara mai rud'arwa, ihu take tana salati sai tangal tangal take ita kad'ai akan gadon. Abdurrahim jin k'arar mutum cikin furgici yafito dan shi harga Allah ya manta da wata yarinya agidansa. "Keee!,keee wata irin mahaukaciya ce" cewar Abdurrahim da kwatakwata baya son hayaniya. Na'ima ko da batason abinda takeyi ba dan har yanzu ba wai tadawo natsuwarta ba ne. Sannan jin tsawar da Abdurrahim yayi mata sai ya k'ara rud'ata. Wata uban k'aratasaki Wanda yasa Abdurrahim rufe kunnuwan sa da sauri, yana ja baya. Lura dayayi kamar ba ahayyacin ta ta ke ba yasa shi Saurin barin gurin. Dan shi mutum ne Wanda baya son hayaniya, kallo d'aya zakai mai kagano hakan. Ruwa mai sanyi Abdurrahim ya d'akko ya watsa mata.sannan Na'ima ta sauke ajiyar zuciya wadda ko ba afad'a ba kasan tadawo ahayyacin ta. Sannan ta jawa wani uban numfashi .Na'ima Abdurrahim ta k'ure da ido tana kallo, can kuma ta ce"Bawan Allah dan Allah inane nan? " Abdurrahim banza da ita yayi yajuya zai koma d'akin shi, tayi saurin sakkowa daga kan gadon ta ce dan Allah Bawan Allah ina nake?,ko na mutu ne" Harga Allah Na'ima take tambayar Abdurrahim duk da tambayar ta ta ta so ta sa shi dariya, cigaba yayi da tafiyar shi, itako tacigaba da tambayoyin ta. " Bawan Allah dan Allah ya akai nafita daga cikin ruwan nan?." Abdurrahim agogon hannun shi ya nuna mata, sannan ya kwantar da fuskar shi akan hannuna shi yanuna mata gadon da ya ajeta alamun taje ta kwanta .Duk da Hannu yake mata kwatancan, kamar dai yadda kurame ke yi. Ba yadda Na'ima ta iya haka takoma gadon ta kwanta da tunanin yadda za ta iya magana da kurma in gari ya waye. "Kai Allah dai kasa a Nigeria nake ma, shikenan yanzu inaji ina gani zan kwanta gidan wani kuma d'aki d'aya, tom ai kamar d'aki d'ayan ne inda daga yafito zai ganni aiko bazanyi bacci ba ma, dan ba'abinda natsana kamar wani yaga kwanciyata" Duk ita kadai ke maganarta cikin zuciya, ahaka dai bacci ya kwasheta ga wata bala in tattar yunwa da take ji. Washe gari Abdurrahim yagama duk abinda zaiyi amma bata farkaba. Alokacin da Na'ima tafarka lokacin shi kuma Abdurrahim yagama abinda zai yi har yafita aikin shi.Gidan ko rufe abin shi yayi kamar yadda yasaba in zai fita aiki. Da wata irin yunwa Na'ima ta farka dan cikin tama har gefe daya na rike mata, zama tacigaba dayi akan gadon tun tana tunanin fitowar Wanda tagani jiya har ta kasa jurewa ta tashi taje kusa da k'ofar d'akin shi,sai dai da alama yafita saboda tatura k'ofar taji arufe take. Kasa daurewa tayi ta fita daga d'akin ,kitchen ta shiga Allah ya tai maketa tasamu wani tea da yasha ya rage sai dai ya huce sai wainar kwai itama da alama yaci yarage ne,ta d'auka ta cinye tass sanna ta d'an ji sauk'in yunwar, sai dai me tana gama ci amai ya biyo baya aiko taita kwarashi agun. Rasa abinda zata kwashe aman tayi ta shiga tolait d'in d'akin nan ma bata ga wani alamun abunda Zata goge ba ko ta share,
🏠