NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 34

n mijin ta shine tak'i zuwa, ni hattasani ma afargaba, na fara tunanin ko lafiya" "Lafiya"cewar gwaggo da batasan ma abinda ta ce ba. "Alhamdulillah ,dama wani mafarkine nayi akan Na'imar mai ban tsoro, shine nazo ingani ko lafiya, daga nan kuma k'afarta-k'afata". Wani irin kuka cikin gwaggo ya yi, cikin rashin sanin abinda zatace ma ta ta ce "Tom tashi mu je gidan da take aikin". B'angaran Na'ima kuwa al'ajabi duk ya isheta wai yau ita ce acikin jirgin ruwa. Su Na'ima ba su yi tafiya mai nisa ba,suka farajin Wani irin k'ara daga k'asan jirgin kamar ana balla Abu, cikin kid'ima captain d'in jirgin ya fara sanarwa jirgi yasamu matsala, kafin kace wani abu, jirgin yafara mangar-mangar. Na'ima kuka tafarayi ganin ruwa yafara tud'ad'owa cikin jirgin. Ahankali ahankali jirgin yafara k'asa ruwa yana k'ara shigowa cikin jirgin sosai kamar ana k'ara antayo shi......... 🛥️ ABDURRAHIM 🛥️ MATUK'IN JIRGIN RUW NE (RENEW) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚* Na Fadila Sani Bakori. Page 8 & 9 Banda salati da kuka ba'abinda Na'ima ke iya yi. Shugaban jirgin ruwan, (captain) ya bada rigar ruwa (life jacket) ya ce Aba duk matan dake jirgin su sa,sannan ya k'ara da cewa"mu na so dan Allah kowa ya kwantar da hankalin sa, ba abinda zai faru dan mun kai sanarwa (report) ababbar headquarter ta mu, za akawomana agaji yanzun nan" cewar captain d'in jirgin. Duk maganar da yake cikin speaker yake yinta, in bahaka ba ba kowa zai ji shi ba, dan jirgin nada girma sosai balefi. Bak'aramin razana mutanan dake cikin jirgin nan su kayiba, ganin jirgin nasu saura k'iris ya nutse, gashi har yanzu basuga alamun masu ceto ba. Shikan shi captain d'in jirgin yagama sadak'arwa. B'ak'aramin rud'ani captain d'in ya shigaba, ganin b'angaran matuk'an masu control d'in jirgin gabad'ayan shi ya nutse cikin ruwan . Gudu mutanan kusa da b'angaran da ya rufta suketayi suna dawowa b'angaran da yake da dama -dama. Allah sarki kusan baka ganin mutane sai kawu nan su kakegani. Bindiga carptin d'in ya sa ya harbi kan shi, dan ba zai jure ganin ruftawar jirgin gabad'aya ba. Rabin jirgin duk ya nutse, duk wata hayaniya da mutane ke yi duk sun baryi, banda mutun uku daga cikin matuk'an jirgin da su kai saura, duk dasu tsabar amanace irin ta su ta turawa, amma su sun iya ruwan da zasu iya taimakon kansu, tom amma su turawa sunada amana duk runtsi duk wuya sai dai amutu tare badai su gudu ba, dan duk sun iya ruwa sannan ga rigar ruwa amma sai sukak'isawa suka ba matan sukasa. Allah sarki su kansu mutum ukun da su kai saura sunriga sun gama galabaita suna ji suna gani haka suka sadaukar da rayuwar su, tsabar alk'awari irin nasu, Mutum d'aya ne da shima yagama galabaita, hannu yake ta d'agawa sakamakon k'arar jirgin da yake ji yana nufo su, dan ko ba afad'a ba yasan su akakawo ma agaji. Jin jirgin nata shawagi yasa ya lalibo usir d'insa yahura yasan k'arar zata ankarar da su dan yasan sakamakom ruwan da yasha kansu ne yahana masu kawo masu agajin sugan su.Tun k'arfin shi yahura usir din. D'aya daga cikin masu kawo agajin ne yajiyo k'arar husird'in, nuna ma sauran abokan tafiyar ya yi inda yajiyo k'arar . Da saurin su su ka k'araso in da su ke ji yo k'arar hura usir d'in. Shiko Azera da yajiyo alamun tahowar su cigaba da hura usir d'in yayi yana bubbuga hannun shi aruwan da d'an sauran k'arfin da yarage mai. ta ke suka gane inda al'amarin yafaru, suka k'arasa wajan. Cikin ikon Allah su kai ta fito da mutane daga cikin jirgin da had'arin yafaru, basuyi wani wahalar fito da mutanan ba, k'asan cewar yawancin matan duk asaman ruwa suke, saboda rigar ruwa da akabasu sukasa . Sun d'au dogon lokaci suna fito da mutane acikin ruwan, inda duk Wanda aka ciro asibiti ake wucewa da su. Ikon Allah duk iya sa idona danayi banga Na'ima ba cikin muta nan da aka ciro, har suka gama cirowa, ban ga alamu da sauran mutum ba, dan har na'urorin su saida suka haska basuga komai ba, sannan suka nufi da wa inda aka ciro asibiti. Tafe yake cikin d'an ma dai-dai cin jirjin sa. Matashi wanda kallo d'aya zakai mai ka tabbatar da kwanciyar hankalin ya wadatai, dan dagani ba sai an fad'aba kallo d'aya za kai mai kagane hakan, Sauri yake yak'osa yaje gida saboda uzirin da yake da shi agidan, wani tudu-tudu yake gani na tun karo shi da alama koma meye igiyar ruwa ce ta jawo shi. Tun kafin abun ya iso kusa da shi ya tabbatar da mutun ne, parking ya yi da jirgin nasa acikin ruwan, sannan yasa wata sanda dake cikin jirgin yarika jawo abun nan ahankali, sai dai tun kafin ya iso wajan shi ya tabbatar da mutum ne, dan yaga rigar ruwa ajikin mutum d'in ,shi ne dalilin da yasa bai nutseba acikin ruwan. Cikin jirgin sa ya sata sannan ya tub'e mata rigar ruwan da ke jikin ta. Al'ajabi ne ya isheshi ya ce " ikon Allah tom wannan kuma daga ina mutum cikin ruwa kuma mace" Tafiya yake yana sake- saken yadda
🏠