NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 7 of 34

ta kalli Na'ima ta ce, "Ki je gida ki shirya dan goba ne tafiyar"Kai Na'ima ta girgiza ta ce "A'a babuwani shiri da zanyima" Duk wani shiri da Na'ima za tayi tayi shi, fatan ganin gobe kawai take. Washe gari Na'ima zau ne a gaban Hajiya Rahila tagama duk wani shiri da za tayi. Hajiya Rahila kallan Na'ima ta yi ta ce, "Tom Na'ima Allah yakiyaye hanya Allah ya sauke ku lafaya, yanzu ga driver nan zai kai ki airport kaya ko mai da komai anriga angama shiryawa daga kun je sai tafowa, amma fa zaki sha sanyi yarinya, zakiyi kalar tafiyar da nake sha'awa Amma ni tsoro yahananiyi danni tsoran jirgin ruwa na ke" Murmushi Na'ima ta yi ta ce "Shekara d'aya da wata hud'u zamuyi ko hajiya?" Dariya sosai hajiya Rahila tayi, sannan ta ce "Yanzu ai a jirgin sama zaku, wajan dawowa ne dai zaku dawo a jirgin ruwa saboda kaya". Driver Hajiya Rahila ya kai Na'ima airport,suna isa ko babu da d'ewa jirginsu ya tashi. "Ikon Allah sai kallo wai yau ni ce a London"Na'ima al'ajabi duk ya isheta lokacinda ta take kwance kan kadon hotel d'in da zata kwana . Kwance take akan tafkekean gadon hotel d'in da Jamilu abokin tafiyar ta ya kamamusu. Juyi kawai take sanyin k'asar da tunanin halin da Mahaifiyarta ta ke ciki yahanata bacci. Washe gari koda Na'ima ta tashi kasa wanka tayi tsabar sanyin da take ji, Jamilu da kan shi ya kawo mata tea da wani farfesun nama. "Tashi ki k'arya dan yanzu zaku Kama hanya, Amma fa zakiyi doguwar tafiya ,dan Allah in tambaye ki mana?"Jamilu ya tambayi Na'ima. "Ina jinka"cewar Na'ima. "Dan Allah me yajawo miki wan nan wahalar haka?". Na'ima kallan Jamilu tayi da mamaki akan fuskarta ta ce "Wahala kuma tame fa?". "Ta tafiya a jirgin ruwa mana, waya fad'a maki su kaya dole sai an tsare su, ai daga anba direbobin shike nan, ba sai an had'a da mai tsaron kaya ba",Jamilu ya fad'a. "Tom nima sha'awar tafiyar ce kawai" Na'ima ta fad'a ma Jamilu haka ne kawai dan ta wuce maganar. Na'ima da Jamilu tsaye suna sallama dan yanzu jirgin su zai kama hanya. Jamilu kallan Na'ima yayi ya ce, "Tom shikenan Na'imatu Allah ya isomana dake lafiya, Allah ya karemana ke gaba da baya". "Ameen "ta amsa. Jamil bashi yabar gurin ba har sai da yaga jirgin su ya tashi sannan. Can b'angaran Mahaifiyar Na'ima kuwa bayan ta koma gida, tun tanasaran zuwan Na'ima har ta gaji, har ta fara tunanin k'ila hajiyar ce bata dawo ba sai gobe, tom Allah yasa dai goban ma tazo da wuri, kafin guyababbun Iyayanta su zo. Washe gari ma haka ya faru ba Na'ima ba dalilinta, Mahaifiyar Na'ima ganin har rana tayi Na'ima bata dawo ba abin sai ya fara bata tsoro, dan tasan tun da tacema Na'ima tadawo tom ba'abinda zai hanata da wowa. "Tom ko dai an sace tane" Haka Mahaifiyar Na'ima tai ta tik'a da warwara akan rashin dawowar Na'imar. Mahaifiyar Na'ima nanan kwance tana tunanin rashin dawowar Na'ima tajiyo sallamar su Ya'u ,cikin kid'ima Mahaifiyar Na'ima ta fito da tab'arma a hannunta tana k'ok'arin shimfid'amu su , Ya'u ne yad'aga mata hannu ya ce. "Dakata Mariya,bazama ya kawo mu ba, mun zo ne kibamu 'yarmu kuma matar d'an mu ko kuma wallahi Mariya hukuma zata rabamu da ke". "Wallahi! Wallhi!! Wallhi!!!" Sonawa narantse Ya'u?" Cewar Jimmai. "Sau uku, yaya jimmai". Kai Jimmai ta karkad'a ta ce, "Wannan shine gargad'i nak'arshe Mariya, ki fitomin da surukata in kuma bahakaba tom zaki san ruwa ba tsaran kwando bane Wallahi"Tana kai wa nan tai gaba. Ya'u kusa da Mahaifiyar Na'ima yadawo ya ce ahankali yadda Jimmai bazataji ba"Mariya ni zan tai makeki,inma baki son auran Na'imar ne, amma sai da sharad'in in kin aminta zaki auran?". Wani mugun kallo mahaifiyar Na'ima tayi mai ta ce "Ba aure atsakanina da kai amma ba abin mamaki bane dan ka fad'i haka inda nasan akwai k'arancin rashin sani atattare da kai". "Kamarya Mariya bangane ba,me kuma ya kawo rashin sani anan? " "Nufina bakasan haramun ba bakasan halaliiba". "Haba Mariya mai Ya kawo maganar haramun kuma da halali ana.... ". Maganar Jimmai da Ya'u yaji ce tasa ya canza abinda yayi niyar fad'a tahan yar cewa "kin ji dai abinda nace maki kinada damar samun mafita, in kinyarda in kuma kink'i tom ya rage naki"Yana kai wa nan yayi gaba abinsa. washe gari da sassafe mahaifiyar Na'ima ta nufi kaduna, sakamakon wani munmunan mafarki da tayi akan Na'ima. Gidan gwaggo Mahaifiyar Na'ima ta sauka. Cikin gwaggo sai da ya kad'a dan ganin mahaifiyar Na'ima da tayi, dan bata san abinda zata ce mata ba game da tafiyar da Na'ima tayi bada izinin taba, haka ma fa na d'aukar mata yarinya na kaita gidan aiki bada sanin taba,kuma koda tazo bata nunamata damuwa ba, ai ko yanzu da kunya in ce mata bata k'asar, tom inama zance mata taje. Haka gwaggo tai ta maganar zuci. Muryar mahaifiyar Na'ima ce ta dawo da gwaggo daga tunanin da ta lula. "Gwaggo ki yi hak'uri karkiga nadaimeki da sintiri ,wallahi abubuwane ne sun kacamemin gashi itama Na'imar da nace tayi hak'uri tazo a kaita d'aki
🏠