nada mata biyu Jamila da kuma Habi, Habi ita ce matar kakana ta fari dan haka ita ta haifama kakana manyan 'ya'ya, gwaggo Jimmai itace babbar yarinyar kakana sai baba Ya'u sai baba Kabiru sai autar su Binta. An haifi gwaggo binta ba dad'ewa kakana ya auro mahaifiyar babana wato kakata, kakata tun da ta haifi babana bata sake haihuwa ba, kuma ta haifi babana badadewa Allah yayi ma kakana Abdullahi rasuwa, babana yataso cikin maraicin uba dan duk wani abu da yayye sukema k'annan su tom su baba Ya'u basama babana, amma fa in dai akazo maganar aiki tom akokacin zasu ce ai shine K'arami, da kakata ta lura wahala zata kassara d'anta d'aya tilo sai ta kai shi sabon yalwa almajiranci. Bakalar fad'an da su baba Rabi'u basu yiba amma kakata ta share, bayan tafiyar babana almajiranci badad'ewa kakata ta kwanta k'aramar jinya, wadda tazama sana diyar ajalin ta, babana yayi nisa da karatu alhamdulillah, saidai kash suna cikin karatu Allah yayi ma malamin nasu mutuwa shima sakamakon k'aramar jinyar dayayi, tom daga nan ne fa Babana ya koma aikin gona ana biyan shi, ahaka ahaka Allah yabud'a mai har ya tsaya da k'afarsa, cikin k'ank'anin lokaci ya sai fili yafara gini, yana cikin gini Allah yahad'a shi da mamana,kasan cewar itama 'yar'uwar babana ce ma'ana marainiya ce babana bai wani sha wuya ba aka bashi auran mamana. Tun da su baba Ya'u sukazo bikin sukaga abinda babana yayi na kud'i tom daga nan fa duk wani Wanda da muwar kudi ta tashi mai sai ya d'aurata akan babana, in ta kai cemiki har sai da sukaga sun karya shi sannan Suka b'arshi.
Masha Allah Allah ya azurta mahaifina da haihuwa dan mu biyar ya Haifa, ni sai k'anwata Aisha, sai Aminu da umar sai auta auwal. In ta k'aice miki tunda gali d'an gidan gwaggo jimmai ya fara nuna yana sona babana yahanani zuwa hidimar wajan su, dalili ko duk yarinyar da gali ya d'auka ido akanta sai ya lala tata.
Yaje gidan yari (prison) yafi ak'irga amma abin sai abinda yayi gaba, dan yanzu ma har sata yake"Numfasawa Na'ima tayi sannan ta ce ci gaba da ce wa "Wannan shine dalilin da ni da babana bama son aurena da yaya gali"
Nan Na'ima taitaba hajiya labarinta har izuwa auran ta da aka d'aura da gali kamar yadda mahaifiyarta tasanar da ita.
Hajiya Rahina kallan Na'ima ta yi ta ce "Na'ima naji labarinki kuma koni ban goyi bayan ki zaman aure da mutum kamar gali ba, dan haka zan kira gwaggonki in shaida mata in har ta yadda tom ba shakka dake za a, sai dai fa a jirgin ruwa zakuyi tafiyar,kuma tafiya ce ta wata shida kin yadda?"Eh Mommy na yadda "
Waya hajiya Rahila ta d'auka ta kira k'awarta hajiya suwaiba akan dan Allah ta turo mata da gwaggo mai ai kinta.
Driver hajiya suwaiba tasa ya kawo gwaggo har gidan hajiya Rahila.
Bayan sun gaisane. Hajiya Rahila ta kalli gwaggo ta ce" Gwaggo nasan zakiyi mama kin kiran ki da nayi, tom Na'ima ce tarok'eni wata alfarma atafi da ita Landon kinsan acan ake kawomin kaya"Nan dai hajiya tafad'ama gwaggo duk yadda su kai da Na'ima,ta d'aura da cewa"Gwaggo kin san HALIBIZ SHOPPING MELL tawace tom dama in dai shekara tazo tsakiya muna ai kawa akawomana kaya, kin san tafiyar ta jirgin ruwa ce, tom suna yin wata shida ahanya,tom kin aminta atafi da Na'ima ko ko?, amma fa ni badani za ai tafiyar ba.........
🛥️ ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.(RENEW)
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*
Na
Fadila Sani Bakori
Page 6 & 7
Hajiya Rahila kallan gwaggo tayi jin tayi shiru ta ce" Gwaggo bakice komai ba, kin yarda in tura Na'ima London d'akko kayan sabuwar shekara da zamuyi ? "Numfasawa gwaggo ta yi ta ce,
"Tom Hajiya bawai nayi shiru bane a'a wallahi kin san Na'ima ba yarinyata bace shine nake gani kibani nan da zuwa gobe inje in tambayi mahaifiyar Na'ima inta yarda tom."
Kafin Hajiya Rahila tai wata magana, Na'ima ta yi wuf ta ce.
"Ahalin yanzu mamana tana cikin k'uncin rayuwa, yayyan babana sun tasata gaba akan auran nan, tun da gwaggo kikaga mama tace sai dai in dawo gida akai ni d'akin yaya gali, tom wallahi bak'aramin furgita ta sukayi ba".
Na'ima kamar za tai kuka ta maida kallanta ga Hajiya Rahina ta ce,
"Hajiya kima girman Allah ki amshi tayin tafiyar nan tawa ko dan in cika burin mahaifina na rashin auran nan da har ya komama ga Allah baya son shi. "
Hajiya Rahina gwaggo ta kallah ta ce,
"Tom gwaggo kin ji abinda Na'ima tace,kin aminta ayi tafiyar nan da ita?"Tom, ni bawai nak'i tafiyar Na'ima bane, a'a wallahi kawai dai kin san yanzu muna wata irin rayuwa ne, sai ka yi Abu da niyar taimako nan gaba yazamarma matsala"
Kai hajiya Rahina ta jinjina ta ce"Hakane gaskiya,dannima bazan d'auki Na'ima ba bada amincewar kowa ba in kaita wannan kasa mai nisa kuma tafiya ce bata yau ko goba ba."
Gwaggo kallan Na'ima ta yi da ke Shirin fasa kuka ta ce,
"Badamuwa Hajiya amanar Na'ima ahannu na take dama, dan haka na amince Allah yasa jin shirun da zasuyi ya zamo silar rigujewar auran"
"Ameen ya Allah"cewar Hajiya Rahina,sannan