i da yake Mahaifiyar Na'ima bata saba rigima ba, jikinta kota ina rawa yake.
Jimmai ko na zuwa ta shak'i wuyan Mahaifiyar Na'ima ta ce"Mariya wallahi ko zaki mutu ba zan sakeki ba sai kin fad'a min ina ki ka kai Na'ima?"
Wujijjiga Mahaifiyar Na'ima Jimmai take da duk k'arfin ta, masu hankali ne daga cikin wa inda suka zo d'aukar amaryar sukaga in sukabar jimmai zata yima mariya illa, in abun yazo da k'arar kwana ma ta kashe ta.
Dak'ar aka b'anb'are Jimmmai daga jikin Mariya, dan bada wasa ta shak'e taba.
"Dan Allah ku bar ni da ita."A'a yaya Jimmai ki b'arta, mu bata nan da kwana biyu mugani "cewar Binta.
Jimmai da kallan Mahaifiyar Na'ima tayi ta ce "Mariya kwana biyu na baki wallahi duk inda ki ka kai Na'ima ki kawota kafin nan da kwana biyu, in kuma bahaka Hmmmm".
'Yan d'aukar Amarya ko haka aka hak'ura aka koma ba amarya.
Allah sarki mahaifiyar Na'ima ranar kusan kwana tayi kuka saboda bak'in cikin abinda Jimmai taimata yaranta na tayata.
Aiko washe gari dawuri Mahaifiyar Na'ima ta shirya ta nufi kaduna. bata tsaya ko ina ba sai gidan gwaggon Hassan, lokacin ita kuma gwaggo tayi shirin zuwa gidan da take aiki.Gwaggon Hassan da mamaki take kallan Mahaifiyar Na'ima ta ce "Kai Mariya ke ce da wuri haka,Allah dai yasa lafiya,amma daga ganin zuwan nan nasan banawa bane, dan haka zo muje in kaiki gidan da Na'imar ke aiki" Aiki kuma gwaggo?" Nan dai kwaggo ta fahimtar da mahaifiyar Na'ima dalilin aikin nata dan ta taimakamusu ne.
mahaifiyar Na'ima bata wani damuwa ba saboda tasan gwaggo bazata kai Na'ima inda zata cutu b.
Koda su gwaggo suka isa gidan da Na'ima ke aiki, mai gadin gidan sukai ma magana yakakira masu Na'ima.
Na'ima ko kullum damuwarta k'ara k'aruwa take, gafargabar auran ta, tana cikin wannan tunanin ne, mai gadin gidan yazo yace meta tayi bak'i.
Na'ima Cikin fargabar kosu waye ke nai manta tafita. Koda ta hangi mamar ta cikin fad'uwar gaba ta k'arasa inda suke,dan daga ganin zuwan bana lafiya bane.
"Oyoyo mamana ,sannun ku da zuwa".Cewar Na'ima.Nan dai suka gama gaggaisawa,Sannan Mahaifiyar Na'ima ta kalli Na'ima ta ce"Na'ima sauri nake je ki d'auko kayanki mu tafi"Mama lafiya dai ko? "Mahaifiyar Na'ima kallan Na'ima tayi ta ce "Yi abinda nace sauri nake na baro k'annanki gida su kad'ai"Na'ima cikin rawar muraya ta ce " Tom mama amma hajiyar bata nan tafita sai dai in tadawo, kinga ni kadai ce a gidan ba zaiyuwu inbarmata gida ba ba kowa" Shiru Mahaifiyar Na'ima tayi ,sannan ta ce "Na'ima bazan iya jiran kiba, amma daga tadawo ki dawo gida yau yau d'in nan, dan jiya Iyayanki suka d'aura maki aure"
Na'ima bak'aramin jarimta tayi ba dan danne damuwarta dan kar mahaifiyarta tafahimci hakinda take, amma ainihin gaskiya ita kadai tasan halin da takeciki.Na'ima kallan Mahaifiyarta tayi ta ce
"Mama tom ya maganar da Baba yayi, kafin yabar duniya? "
"Na'ima ki yi abinda nace kinji, Iyayanki jiya bakalar cin mutuncin da basuyimin ba"Na'ima cikin damuwa ta ce
"Shikenan mama zan dawo yau d'in in tadawo, amma mama kina son auran ne yanzu?"
"Tom Na'ima ya zanyi?, amma maganar so ko bazan tab'a so auranki da gali ba"Shikenan mama sai nazo"
Na'ima koda tadawo gida , bak'in ciki yawa yayi mata, ga haushin abinda akai ma Mahaifiyarta ga takaicin auran da aka ce an d'aura mata da gali. Palon ta zauna tana ta kuka, har hajiya Rahina ta shi go amma bataji shigowar ta ba"
Hajiya Rahima kusada Na'ima ta zauna amma abin mamaki har yanzu Na'ima bata ji motsin hajiya a polon ba, kukan ta kawai takeyi a bunta.
"Ke! lafiyar ki? "Cewar hajiya Rahina.Sannan taci gaba da cewa
"Nalura da ke , tun da kika zo gidan nan baki da wani aiki sai tunani, tom idan bazaki iya aikin ba zan samu wata, inda abun naki k'arak'aruwa yake, yanzu abun ya zama sai kizo ki zauna ki tamin kuka, ina Tambayar ki kuma kin min shiru kin zuba min ido, tom wallahi bazan d'auka ba"
Na'ima shiru tayi tana sauraran hajiya, sannan ta ce"ki yi hak'uri dan Allah"
Zama hajiya Rahina tayi tana fuskantar Na'ima sannan ta ce"Me yasaki kuka yanzu nake son in sani? "
"Dama mama nace tazo yanzu tace wai duk abinda na keyi in dawo gida yau, tom ni kuma bana son komawa gidan"Saboda me?" Cewar hajiya Rahina. "Saboda 'yan'uwan babana sun min aure ni kuma bana son auran da su kai min,kuma Babana ma kafin ya mutu yace kar su auramin Yaya gali"
"meyasa bakya son galin? "
"Saboda babana yana gaf da mutuwa yace ko bayan ranshi be yarda ba in auri yaya gali"Na'ima hannun hajiya Rahina ta kama kamar za tai kuka ta ce "Hajiya dan girman Allah kitaimakan ki kaini, kasar nan danaji kina cewa za akawo miki kaya kuma zasu dad'e basu dawo ba, dan Allah hajiya hakane kawai zai sa in gujema auran Yaya gali da Babana ma baya so "Shiru Hajiya Rahina tayi ,sannan ta ce "Zan taimakeki amma sai naji cikakkyan tarihinki, naji dalilin dayasa mahaifinki be so ki auri d'an'uwanki?"
Shiru Na'ima tayi kamar mai tunani, sannan tafara magana kamar haka.
"Kakana Abdullahi ya