NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 4 of 34

ta hada kayan ta gobe zata fara aikin, kuma acan zata zauna, duk da Na'ima bata so zaman can ba bata nuna ma gwaggo ba godiya tayi mata sosai. Washe gari gwaggo tare da Na'ima su ka tafi gidan da take aiki, suna zuwa ko hajiya suwaiba tasa yaran aikinta yaraka Na'ima gidan hajiya Rahina wadda zata yima aiki, koda ya kaita a palon ya ce ta Zauna ta jira hajiyar kafin ta sakko tasan da zuwan ta" Na'ima ta dad'e sosai kafin hajiya Rahina ta sakko, amma abin mamaki hajiya tazo ta wuce ta ga ban Na'ima amma bata saniba "keeeee!" Hajiyar takira su nan Na'ima amma Na'ima ta shiga duniyar tunani bata jiba. Ciikin tsawa hajiya Rahina ta sake cewa "keee bakya ji ne?" Cikin furgici Na'ima ta tawo daga duniyar tunanin da ta fad'a ta ce "Wallahi banji bane yi hak'uri dan Allah ina kwana?" Shiru hajiya tayi tana kallan Na'ima nawani lokaci sannan ta ce" Lafiya ,yasu nan ki?, 'yar nan kaduna ce ke? " "Sunana Na'ima muna Zaune ne a sabon yalwa kusa da jaji" Kai hajiyar ta jinjina ,sannan ta ce "Kinnsan aikin da za ki min ? "A'a bansani ba" "Ok zaki rika min Shara da goge-goge sai wanke- wanke, zan rika baki dubu sha biyar duk wata yayi miki? " "Nagodee sosai yayi mommy " cewar Na'ima. Yau kwanan Na'ima uku da fara aiki kuma yau yake saura kwana uku d'au rin auran ta da gali kamar yadda yayyan babanta suka sa, hakan yasa hankalin Na'ima yata shi sosai duk Wanda yaga Na'ima ko be son taba kallo daya zai mata yagano cikin damuwa take. Can ko sabon yalwa fad'in damuwar da Mahaifiyar Na'ima take sai Allah ,ta yi bak'i taramai sosai kullum cikin zullumi take na zuwan 'yan'uwan Mijinta, yanzu haka Zau ne take akan dadduma ta idar da sallah, sallamar su binta ce tadawo da ita daga tunanin da ta ke ciki. Bak'aramin furgici mama ta shiga ba ganin su Ya'u, amma sai ta danne suka gaggaisa , bayan sun gama gaggaisawa ne, Binta ta ce "Tom Mariya ga kayan lefan Na'ima nan mun kawo" bud'e akwa tin Binta tayi tana nuna ma Mahaifiyar Na'ima kayan, atamfofi ne guda shida d'aya ce cotton amma sauran duk roba ne Sai ta kalmi d'aya hijab d'aya. Bayan Binta ta gama nuna ma Mahaifiyar Na'ima ne ta ce " Gashi nan Mariya ku yi hak'urin abunda babu in ta shi ga yayi mata kin san de yaran nan basana ace gare shi ba "Yayi ma k'okari" cewar ya'u. Binta ko taji gaba da cewa " Yaya Jimmai ta ce ace maku daga an d'aura aure za azo atafi da amarya kin san hanyar tamu Sai ahankali..." Mahaifiyar Na'ima dai ta kasa cewa komai,ganin haka Binta ta ce "Mariya baki ce komai ba?" Mahaifiyar Na'ima dai bata tankaba dan batasan me zatace ba. Ya'u Wanda mahaifin Na'ima ke bimawa ya ce "Rabu da ita Binta, ko tayi magana ko kar tayi mude mun bada sa k'on da akabamu akace mubada ku tashi mu tafi" Binta da bataga Na'ima kallan Mahaifiyar Na'imar ta yi ta ce "Mariya wai In Na'imar ne Banganta ba ?" Mahaifiyar Na'ima nan ma banza tayi da su. kwafa Ya'u yayi ya ce" ku mu je" Yau juma'a kuma yau yakama ranar d'aurin auran Na'ima da gali kamar yadda akasa, haka ko ta kasance anadawowa sallar juma'a aka d'aura auran Na'ima da gali, bayan gama d'aurin auran ne badadad'ewa ba masu d'akko amarya suka kamo hanya zuwa d'aukar Amarya. Mahaifiyar Na'ima na zaune cikin fargaba da tashin hankali dan yaune d'aurin auran Na'ima kamar yadda suka ce. Mahaifiyar Na'ima na nan zaune cikin fargabar yadda zasu kaya da Iyayan Na'ima masu d'aukar amarya suka shigo............ 🛥️ ABDURRAHIM🛥️ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE (RENEW) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚* Na Fadila Sani Bakori Page 4 & 5 Da bud'ar su su ka shigo gidan. Mahaifiyar Na'ima cikin fad'uwar gaba tafito daga d'aki. D'aya daga cikin masu d'aukar Amaryar ce ta ce "Tom Mariya yau dai Allah yayi Na'ima ta zama matar gali, afito mana da amarya sauri muke kin san hanyar tamu". Mahaifiyar Na'ima shiru tayi,sannan ta Binta ta ce"Binta d'an shigo daga ciki muyi magana."Binta binta tayi batare da tunanin komai ba tashiga. Bayan Binta ta shiga d'akin Mahaifiyar Na'ima ne, Mahaifiyar Na'ima ta kalli Binta ta ce" Binta banfa san inda Na'ima take ba" Wani uban ashar Binta tayi ta ce" wallahi Mariya tun daga ni sai ke ki fito da Na'ima kafin su yaya Ya'u suji maganar nan!" Wani banzan kallo Mahaifiyar Na'ima tayi ma Binta ta ce "Kowa zaki fad'amawa ki je ki fad'a mai Binta nace miki bansan inda Na'ima takeba". Tana kai wa nan tajuya tayi tafiyar ta. " Binta waya ta d'auka ta kira jimmai uwar ango ta fad'a mata abinda Mariya tace. Uwar ango wanda take amazaunin yayyar mahaifin Na'ima,cikin fushi ta ce "Binta ku jirani ganinan zuwa"Daya ke banisa tsakanin tudun malam da sabon yalwa hakan yasa cikin k'ank'anin lokaci jimmai ta iso." Tun kafin Jimmai ta k'arasa shigowa gidan take fad'in" ke Mariya duk inda kika kai Na'ima kiyi gaggawar d'akko ta kafin in shigo, dan wallahi in har na shigo banga Na'ima ba sai kin san dani ki ke, dan Yahaya ma bai isaba bare ke karan ka'da miya" Allah sark
🏠