abta, in ma yaran ne ko yarinyar in ki ka haifa ni nayi alk'awari zan rik'eta"
Nan dai hajiya Rahina tai ta lallashin Na'ima, dak'ar Na'ima tayi shiru sannan hajiya Rahina ta kawo ma Na'ima abinci, Na'ima k'in ci ta yi hajiya Rahina matsama Na'ima tayi akan dole taci abinci,Na'ima cikin kuka ta ce " bana iya cin komai sai tea " Tea d'in Hajiya Rahina ta had'o ma Na'ima mai kaurin gaske, nan dai suka yi sallama da gwaggo bayan taci abinci ta tafi.
Duk wata kulawa da ake ba mai ciki hajiya Rahina ta na ba Na'ima ita, game da mahaifiyar Na'ima ko hajiya Rahina tace ma Na'ima tambari sai ta haihu sunje su sa ke samunta dan har yanzu tana cikin takaicin cikin.
BAYAN WATA TAKWAS:
Cikin Na'ima har yafito dan a lissafin su koda yaushe Na'ima za ta iya haihuwa.
Yau Na'ima ta ta shi da wani irin ciwan mara, Allah yasa hajiya Rahina ta na gidan, amma kuma tana ta shirin zuwa airport d'auko d'anta da ya gama karatu dan yama kirata suna gaf da sauka, zata tafi kenan d'akko shi ta shiga tai ma Na'ima sallama ta isketa cikin halin da ta ke ciki.
Hajiya Rahina cikin rud'ewa ta shiga d'akin tana kamo Na'ima tana mata sannu,waya hajiya Rahina ta d'akko zata kira wata likita sai dai ganin yadda Na'ima ta zama lokaci guda yasa hajiya Rahina ta kasa kiran.
Cikin kin ikon Allah da taimakon hajiya Rahina Na'ima ta haihu,dai dai lokacin ne kuna yaron hajiya Rahina ya shigo gidan yana mamakin jin kukan jinjiri agidan nasu, har zai shiga d'akin da ya ke jin kukan sai kuma yafasa ya zauna falon ya na jiran fitowar mommyn shi.
Gajiya yayi da zama ya tashi ya shiga ciki ya watsa ruwa ya sakko k'asa samama kan shi abin da zai ci, karo su ka yi da hajiya Rahina da cup cike da tea ahannunta ,hajiya Rahina rik'e baki tayi ta ce"Kai-kai son afuwa Allah saura kad'an in manta da kai" mommy lafiya dai ko? Ina kuma ki ka samo b'aki ? Dan naji kukan jariri ina shigowa" "kai dai ka bari in mik'a mata tea d'in nan inzo in baka abinci da labari"Tom hajiyata afito lafiya"Hajiya Rahina tea ta ba Na'ima ta ce " yi ma za ki sha yanzu nan yarona ya dawo" murmushin K'arfin hali Na'ima ta yi dan bata jin dad'in jikinta gabad'aya.
Hajiya Rahina falon ta dawo ta ce"Ayyah my son fushi bai ma kyau ba,gara kayi murmushinka ya fi ma kyau" Haba mommy tun d'azu nazo ba ta ni ki ke ba ta wata can ki ke wadda ban san ina ki ka samota ba"Dariya hajiya Rahina ta yi ta ce"ina yarinyar nan dana ta b'a baka labari wadda aka je d'akko mun kaya da ita lokacin da Jirgin kayanmu yayi accident na ce maka ta mutu?" Eh na tuna mommy"Tom wallahi ashe ba ta mutu ba wanda ya tsince ta ne kuma yayi mata ciki kasan mutane, mahaifiyar yarinyar kuma tace bazata rike ta ba shi ne fa ni na ke rik'onta,,,," kukan babyn da Hajiya Rahina tajine ta ce"ka ji ko yarinyar na kuka ina zuwa na bar mai haihuwa ita kad'ai"Hajiya Rahina ko da ta shiga Na'ima na gefe d'aya rik'e da mara saimalele kuwa take babyn kuma sai kuka take, Hajiya Rahina batabi ta babyn ba ruwa mai sanyi tasamo ta yayyanka allbasa taba Na'ima tace taci zai mata sauk'in ciwan marar, ganin tarasa yadda zatayi dasu ga Na'ima sai malele kuwa take tak'i shan maganin ga kuma babyn itama sai kuka take, babyn hajiya Rahina ta d'auka ta fita da ita ta ce"son dan Allah jijjiga min yarinyar nan inji da uwarta" Amsar yarinyar yayi yana jijjigawa, ita kuma ta koma ta d'au maganin da kanta ta ba Na'ima abaki . Shi ko sai jijjiga yake ita ko baby ta dake sai kukanta ta ke.
Hajiya Rahina jin yarinyar tak'i shiru ganin ciwan Na'imar ya lafa ta ce "Son kawo min ita"
Da sallamar shi ya shi ga sai dai kasa idasa salkamar yayi yana nuna Na'ima itama Na'ima ba ta san san da ta ta shi ba daga kwancan da take tace "Hafizzzzz kai ne?"Wanda Na'ima ta Kira da Hafiz shi ma cikin mamaki ya nuna Na'ima ya ce "Aunty Amarya ke ce!?"
Hajiya Rahina kallan su ta ke yi ganin irin kallan da su kema juna na sani, gabantane yafad'i kardai ace Hafiz shi ya yi ma Na'ima ciki tunowar da tayi Hafiz ba a England ya ke karatu ba yasa hankalinta yad'an kwanta,ta kalli Hafiz ta ce "Hafiz kasan Na'ima ne dama?" Mommy matar brother Abdurrahim ce,,,,,,,,,
ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE daga nan free pages ya k'are 'yaruwa ki na buk'ar ci ga ba ? Dan samun ci gaban Abdurrahim matuk'in jirgin ruwa ne cikin sauki za ki transfer ta account d'in nan Account number 2111619333
Account name Fadila Sani
Bank name zenith Bank
za ki yi transfer 500 Kacal ko katin MTN number 08063830828
idan kuma biyu ki ke so ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE da MEENALLYN DADDY za ki transfer 900 only 👌🏻 ko katin MTN ta number nan 08063830828
Dan nai man k'arin bayani za ki iya magana da marubuciyar kai tsaye ta number nan 08063830828 .
Dan Allah idan ba siye za ki ba kar mu b'ata ma juna lokaci🙏🏻🙏🏻🙏🏻
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na