a suka d'unguma a motar hajiya Rahina suka nufi sabon yalwa gidan su Na'ima. Na'ima kuka ka wai take yi dan ita kanta batasan da idanun da zata kalli mahaifiyarta ba, Na'ima na cikin tunane-tuna nanta sai dai ta ji hajiya Rahina na cewa "mu je ko Na'ima, sannan ki goge hawayan nan na ki"
Mahaifiyar Na'ima na d'aura ma yaro manja da yake itace sana'arta yanzu tun jalin da mijin
hajiya Rahina ya bata ta saro manja da su kuma alhamdullilah sana'ar ta amsheta, dan tana ciniki sosai kuma da ita suke ci da sha da k'annan Na'ima.Mahaifiyar Na'ima da fara'arta ta shimfid'a ma su gwaggo tabarmar Na'ima ta kalla ta k'ara kallo ta ce"gwoggo wa na ke gani kamar Na'imata? "Ita ce Mariya ba gizo ta ke miki ba ita ce wallahi" Cewar gwaggo.
Na'ima rugume Mahaifiyarta tayi tana kuka, Allah sarki ita ma mahaifiyar Na'ima kukan ta ke, saida suka gaji suka yi shiru dan kansu ba wanda ya hanasu daga gwaggo har hajiya Rahina, ita mahaifiyar Na'ima sun san na murnar dawowar 'yarta ce, ita ko Na'ima sun san kan zancan kukan na ta.
Mahaifiyar Na'ima zaunar da Na'ima ta yi ita ma ta zauna tana mai cewa"Ku yi hak'uri hajiya ban baku ruwa ba mun tasaku gaba muna muku kuka" Murmushi hajiya Rahina ta yi ta ce"Wallahi hajiya banga laifinki ba"Mahaifiyar Na'ima tashi tayi tasamu yaro awaje ta ba shi kud'i ya siyo musu pure water. Bayan angaisane ansake gaisawa hajiya Rahina ta kalli mahaifiyar Na'ima ta ce"Maman Na'ima kin ga ikon Allah ko ya dawo mi ki da Na'ima alokacin da kin riga kin hak'ura da ita, haka ake so duk abin da yasamu bawa yayi hak'uri ya fawwala ma Allah, Allah na san bawansa mai yadda da k'adddara ko wata iri ce shi ne cikakkan musulmi. Kin ga da ki ka bar ma Allah ko mai duk da dai mun zaci Na'im ta mutu ne sai Allah yadawo da ita alokacin da ba muyi zato ba ,ashe Na'ima ba mutuwa ta yi ba duk da tace Wanda yatsince ta bai fad'a mata yadda akai ya tsinceta ba, tom Na'ima gatanan dai agabanki bata mutu ba, wani bawan Allah ne yatsinceta yakaita gidan shi yaci ga ba da riketa har izuwa lokacin da Allah yanufa ya biyamata kud'in jirgi ta dawo garemu.Maman Na'ima kin san duk indai namiji da mace suka kad'aita shaid'an ne yake zama cikon na ukun su, tom Cikin k'adddarorin da Allah ya rubuta mi ki ke da Na'ima gashi nan Allah nata nuna mi ki su d'aya bayan d'aya dan ko auran Na'ima da gali kin san k'adddara ne amma sai kuka nuna bazaku amshesa ba, tom haka Allah ke ikonsa da Na'ima ta nuna bazata amshi k'addarar auran gali ba sai Allah ya musanya mata da ciki yaga ita zata amshe ta Ko ko itama zata butulce mai ne.Maman Na'ima atak'aice dai ina so ince mi ki yarinyarki Na'ima na d'auke da ciki"Wata uwar k'ara Mahaifiyar Na'ima ta yi wadda saida ta rud'a su hajiya Rahina, balle kuma uwa uba Na'ima, dan ita take ta fasa kuka. Mahaifiyar Na'ima ta shi tayi ta shi ga d'akinta da gudu kamar sabuwar mahaukaciya ta d'akko tab'arya tayo kan Na'ima da ita da sauri hajiya Rahina su ka rirrik'e Mahaifiyar Na'ima.Mahaifiyar Na'ima kuma cikin b'acin rai ta ce "Hajiya ki sake ni ina jin kunyarki!"Ki yi hak'uri maman Na'ima na san da ciwo ,amma dan Allah ki yi duba da hankalinki kin san wacece Na'ima in ba k'addara ba kin san halin yarinyarki"
Ina Mahaifiyar Na'ima bata saurari maganar hajiya Rahina ba,sai dai
duk yadda mahaifiyar Na'ima ta so sub'arta ta bugu Na'ima abin yaci turo, ganin baza su saketa ba ya sa Mahaifiyar Na'ima cikin b'acin rai ta ce" Hajiya k'un k'i saki na ko? Tom shikenan gaku ga Na'ima nan dan Wallahi Na'ima sai saidai tasan inda zata zauna ba dai gidan nan ba, kuma in dai ni ce mahaifiyar Na'ima tom na cireta aciki 'ya'yana da nahaifa bani babu Na'ima,ki fita in bar ganinki wallahi kafin in mi ki baki, dama abin da ki ke son yi kenan shi yasa kika ce kar afad'a min zaki tafi ,Shikenan ki fitarnin agida na ce ko!, hajiya dan Allah ku fita baki d'aya ku fita bana son ganinku dukkanku abin da ku kai min Allah ya sa kamin kun had'a kai kun kai min yarinya ammata ciki dole za ku zo ku yi min dad'in baki ku fita dan Allah !!" Cikin wata irin razananniyar tsawa Mahaifiyar Na'ima tai maganar.
Allah sarki Na'ima ko ta had'a kai da gwiywa sai kuka take, Hajiya Rahina jawo hannun Na'ima tayi tasa ta mota ta shiga suka tafi. har suka je gida Na'ima batayi shiru ba.
Bayan sun shiga falon hajiya Rahina ne sun zazzauna, gwaggo ta ce"Hajiya yanzu ya za ai da Na'ima da cikin jikin ta? "Tom Na'ima dai sanadiyata wannan k'addarar ta fad'a mata ,dan haka za ta ciga ba da zama wajena, ciki kuma k'addararta ce dan haka zata raini abin ta"Wayyo ni dan Allah ku tai ma ka min azubar k'il in aka zubar ita ma mamana tayi hak'uri dan Allah ku tai ma ka min " Allah sarki da yake hajiya Rahina macece mai tsananin tausai jawo Na'ima tayi ajikinta ta ce"ki yi hak'uri Na'ima zubba ciki laifine babba, shi musulmi ana so duk k'adddarar da tasamai ya amsheta hannu bibbiyu ya gode ma Allah, sai ki ga Allah ya kawo mai mafita cikin sauk'i sabo da Wanda Allah ya nufa da alkairinsa shi ne yake jar