NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 34

a ce "tom ki kwanta ki yi bacci dan Allah kinga dare yayi kuma gobe da wuri zaki wuce"tom ba kace bazaka biyamin k'ud'in jirgi ba?" cewar Na'ima tana goge hawayan da ya zubo ma ta, Abdurrahim cikin jin tausayinta ya ce "wasa na ke mi ki zan biya mi ki" nan dai Abdurrahim ya lallashi Na'ima tare da tabbatar mata da in taje zai zo daga baya sannan yabarta ta kwanta. Washegari Abdurrahim da kan shi ya shiga kitchen ya had'a ma Na'ima tea ya soya mata kwai anufin shi duk dan kar taji yunwa dan shi tausai yanzu ta ke ba shi. Bayan Abdurrahim ya gama komai ne ya tada Na'ima. Bayan Na'ima tayi wanka ne tasa sabuwar rigar da Abdurrahim ya siyo mata wadda bata ta b'a sawa ba ,bayan ta gama shirin ta ne tafito falon, kallanta Abdurrahim yayi nad'an lokaci dan sai ya ga batatab'a mai kyau ba kamar yau ba. Bayan Na'ima ta gama shan tea d'in ne tabar mai kwan shi agun, kallanta Abdurrahim yayi yace"me ya sa baza ki ci k'wan ba? "Amai zai sani" "Okay"Abdurrahim yace. Abdurrahim dakan shi ya d'auki Na'ima ya kaita har airport. Abdurrahim hannun Na'ima ya ruk'o lokacin da zata sauka daga motar ya ce" Tsaya mu yi sallama mana,Na'ima dan Allah kar ki bari ki haifi cikin jikinki kin ji?"Abdurrahim ya fad'i maganar cikin sanyi ahankali, dan ji yake jikin shi duk yayi sanyi na rabuwar da zasu yi, sannan yaci gaba da cewa" kin ga gida zaki dan Allah in ki ka je kiyi k'okarin zubar dashi acan kinji?" Kai Na'ima ta d'aga ma Abdurrahim.Abdurrahim kuma cikin sanyi ya ce"kin yi min alkawari za ki zubar ?" Nan ma dai kai Na'ima ta k'ara d'aga mai," ki yi magana da bakinki sannan in yarda"cewar Abdurrahim. Na'ima cikin sanyi itama ta ce" na yi alkawari zan zubar insha Allah" ta fad'i maganar tana share hawayan da ke zubar mata. Wata leda Abdurrahim yamik'a ma Na'ima ya ce"gashi nan da akwai wata takarda aciki in kinje gida ki karanta kinji? "Amsa Na'ima tayi still tana goge hawayan da ke zubar mata. Abdurrahim kallanta yayi ya ce" me ya sa ki ke kuka? " "Ni ma bansan ina yin kukan ba" Hannunta Abdurrahim ya kamo ya ce" Allah ya k'addara saduwar mu" yana kaiwa nan yabud'e mata murfin motar ta fita. Abdurrahim na nan tsaye yana kallan Na'ima yaga ko zata waigo,amma Na'ima har ta shiga jirgin bata wai goba.Abdurrahim ta da motarshi yayi ya tafi. Jikin Abdurrahim asanyaye ya koma gida. Na'ima basu suka sauka gida ba sai cikin dare, direct Na'ima gidan hajiya Rahina ta nufa tad'au drop din mota,suna zuwa tai ta bubbuga gidan, mai gadin cikin tsoro ya matso kusa da get d'in ya ce"waye?" Baba ni ce" cewar Na'ima."ke ce wa?"Mai gadin ya tambaya. "Baba Na'ima ce" Ai Baba mai gadi najin haka ya matsa kusa da get d'in cikin wani sabon tsoran dan shi asanin shi ance Na'ima ta mutu a accident d'in da su kai na Jirgin ruwa har kayan hajiya suka hallaka, wayar hajiya Rahina Baba mai gadi yakira. Hajiya Rahina cikin bacci taji wayarta na ringing dubawa tayi taga number baba mai gadi, d'auka tayi tace"Baba lafiya? "Hajiya Wallahi ba lafiya ba, bubbuga k'ofar gida ake na tambayi waye ne akacemin wai Na'ima ce yarinyar ta akace ta mutu" Hajiya Rahina ma cikin kid'ima ta sakko tayo wajan mai gadin, tsaye tagan shi can nesa da get d'in, ita kuma Na'ima har yanzu bata bar bugawa ba tana cewa"Baba ni ce ban mutu ba Wallahi" Ai Hajiya Rahina najin haka tace"Baba bud'e Na'ima ce wallahi ga muryar ta nan wata biyar ai bazai sa inkasa gane muryar ta ba" bud'e get d'in mai gadin yayi, Na'ima ciki tashigo tana goge hawayan da batasan takamaimai na me ye ba, na murnar dawowarta mahaifarta ne Ko ko na bak'in cikin dawowa da cikin shege ne, Hajiya Rahina rungume Na'ima ta yi tana cewa "alhamdulillah dama Na'ima baki mutu ba ? Alhamdullilah!" abin da Hajiya Rahina ke cewa ke nan.Hajiya Rahina dakan ta ta rik'e kayan Na'ima suka shiga cikin gidan, d'akin da aka tanada dan bak'i Hajiya Rahina takai Na'ima,sannan ta kawo mata tuwan shinkafa. Na'ima ko yunwa take ji amma ta san ko da taci aman shi za ta yi dan haka ta kalli Hajiya Rahina tace"Mommy da dai akwai tea ne da shi na sha" dariya Hajiya Rahina ta yi tace "Allah sarki anyi doguwar tafiya ko ciki ya cin ku she"Shiru Na'ima tayi Hajiya Rahina kuma da kanta ta Had'o ma Na'ima tea d'in ta kawomata tai mata sai da safe dan ta huta washegari sa zanta. Bayan Na'ima ta gama shan tea d'in ta ne ta d'akko ta kardar da Abdurrahim yabata ta bud'e ta fara karantawa kamar haka, "Ki yi hak'uri Na'ima bazan iya zuwa gidan ku ba, hasalima address d'in da ki ban namanta shi, sannan ki taimaki kanki ki zub'ar da cikin da ke jikinki, ga kud'i nan ki yi hidimar zubar da cikin dasu. Bissalam. 🛥️ ABDURRAHIM🛥️ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE 📚📚🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚📚🖊 Na Fadila Sani Bakori. MARUBUCIYR 1)IN DA RAI 2) RAYUWAR HAIDAR 3) SO NE SILA 4) OGA HABIB 5) DAGA ALLAH KO D'AURA MA KAI. 6) ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE
🏠