ci nata gabatowa amma tanajin ba kinta yayi nau yi bazata iya ba, can dai ta daure ta ce" Mama!" Kai mahaifiyar Na'ima ta d'ago tana kallan ta alamun inajinki.Na'ima kuwa cikin rawar baki ta fara magana kamar haka
"Dama mama ni bawai auran Yaya gali bane bana so, a'a wallahi na hak'ura kawai dai ina duba maganar da baba yayi ne yana gab da barin nuniya beyarda ko bayan ranshi in auri Yaya gali ba, amma naji kin yi shiru da maganar gashi lokaci sai tafiya yake" Tom Na'ima wallahi ba wai nayi shiru bane ,a'a rashin mafitane ya sani yin shirun dole, amma Na'ima ya kike gani zanyi ki fad'amin? ".
Mahaifiyar Na'ima kamar zatayi kuka tai maganar.
Na'ima shiru ta yi sannam ta ce "Mama ko gidan nan zamu saidane mu tashi mu koma inda basu sani ba?"
Da sauri mama ta d'ago kai tana kallan Na'ima,ta ce "Na'ima mu saida gidan nan mu koma ina da zama ga tarin k'annan ki? "
Na'ima za tayi magana ne sallamar Hassan ta hanata. Mama ko da murnarta ganin Hassana ta ce " Kai-kai sannu da zuwa maraba Hassan kai ne yau agarin, lallaikam ,Na'ima shimfid'a mai tabarma" Hassana ckin dariyar shi ya ce " Wallahi mama ni ne kin ganni sai yau, naso in zo ayi addu'ar bakwai dani amma Allah be nu faba" Bakomai Hassan "cewar mama.
Hassana kallan Na'ima yayi ya ce" k'anwata ya akaine naga ba akulani ba tun da nashigo?"
Mahaifiyar Na'ima ce taba Hassan amsa da cewa"Na'ima nacikin damuwa Hassan ko ince munacikin damuwa,naji dad'in dawowarka wallahi muna cikin damuwa sosai Hassan Nida Na'ima"Nan dai mahaifiyar Na'ima ta kwashe halin da suke ciki tafada ma Hassan kaf.
Hassan shiru yayi yana nazarin inda za'abulloma lamarin dan yasan halin 'yan'uwan mahaifin Na'ima kaf, bayan dogon nazarin da Hassana yayi ya kalli Mahaifiyar Na'ima ya ce
"Mama yanzu ke yadda za ki yi kina gani zasu aurar da yarinyar nan agun Wanda bata so, ba abinda zaki yi akai?"Tom Hassan ya zanyi?,
Kana gani shi kan shi mahaifin yarinyar nan nuna mai suke kamar sun fishi iko da ita, tom bare kuma ni da basu d'aukan bakin komai ba "
Hassana kallan Mahaifiyar Na'ima yayi ya ce "Idan kin yarda mama ni zan d'au Na'ima in kai ta gurin gwaggona ta Kaduna? "
Mahaifiyar Na'ima kallan Na'ima ta yi ,sannan ta maida kallanta ga Hassan batare da shakkuba dan ta yadda da Hassan sosai ta ce"Badamuwa Hassan nasan bazaka kai Na'ima gurin da kasan zata cutu ba, na yarda na amince ka kai ta, amma tunanina d'aya ne in suka zo me zan ce masu?, ina zan ce masu na kai Na'ima Hassan?"
"Tom mama ni dai yan zu sai in ga kamar wannan ita ka d'ai ce mafitar mu mafi sauki "
Shiru mama tayi nawani lokaci ta ce "shikenan Hassan Allah yasa haka shi ne abinda yafi alkairi"Da ameen suka amsa.
Wa she gari da wuri mama suka shirya tafiya kaduna kai Na'ima gurin gwaggon Hassan kamar yadda suka tsara, kasan cewar banisa tsakanin sabon yalwa da cikin garin kaduna yasa cikin awa (hour) daya suka k'arasa kaduna dan ma motar haya ce, Hassan yayi masu jagora har gidan gwaggonshi,kasan cewar Na'ima sun san juna da gwaggon cikin mutunci ta tar besu, bayan ta basu ruwa sun sha aka gaggaisa Hassan ya zayya ne ma gwaggo abinda yake tafe da su game da barin Na'ima da suke sonyi .
"Allah sarki mutuwa kenan me to nan asiri bako mai karkiji ko mai zan rike Na'ima har izuwa lokacin da yayi muku "
Godiya sosai mahaifiyar Na'ima ta yima gwaggon Hassan. "Haba ai anzama d'aya" cewar gwaggon Hassan d'in. Nan su kai sallahma suka tafi su ka bar Na'ima da gwaggon Hassan tare.
Haka mahaifiyar Na'ima suka dawo sabon yalwa cikin fargabar abinda zata cema yayyan mijinta duk sanda suka zo game da d'aurin auran Na'imar.
Yau kwanan Na'ima biyu kenan awajan gwaggon Hassan ,duk wani aiki kusan Na'ima ta d'auke ma gwaggo shi ,hakan yasa Na'ima ta shiga zuciyar gwaggo sosai. Yanzu haka Na'ima Zau ne ta ke tana wanke-wanke koda ta gama cigaba tayi da zama wajan wanke-wankan tayi tagumi hannu biyu, tunanin Mahaifiyarta duk ya da meta yadda zata k'arke da 'yan'uwan Mahaifinta in sunzo. Sannan asaninta basu da sauran abincin da fawa ko ya suke yi.
Gwaggon Hassan dafa kafad'ar Na'ima tayi ta ce" Cire tagumin nan dan Allah bashi da kyau kinji Na'ima" Tom gwaggo wallahi abun ne yayi min yawa ga tunanin koya mama zata k'arke da yayyan babana ga tunanin kome suke ci oho, wallahi gwaggo harma narasa wane tunani zanyi"Gwaggo shiru tayi sannan ta ce "Na'ima za ki iya aikin cikin gida irin Wanda nake zuwa?" Sosai ma kuwa gwaggo ai nama samu abinda zan rika tai makamasu da shi"
"Shikenan dama matar da nakema aiki tace in samarmata 'yar aiki k'awar ta na naima, inkina so sai in mata magana ki fara zuwa?" "Aiko inaso gwaggo nagodee "Cewar Na'ima cikin murnarta.
Ai ko gwaggo na zuwa gidan da take aiki ta fada ma hajiyar gidan tasamu 'yar aikin da tace ta samar mata, take hajiya ta kira k'awar ta awaya ta fad'a mata tasamu 'yar aikin.
Godiya k'awar hajiyar tayi ta ce "zata iya fara zuwa aiki gobe "
Aiko koda gwaggo ta dawo gida ta sanar da Na'ima