cewar Na'ima idonta har ya kawo ruwa.
Abdurrahim kai ya jinjina mata ya ce"da gaske ne mana ,amma ki kwantar da hankakinki Allah ya kawomana mafita ga magani nan likitan ya bamu yace daga kin sha cikin zai zube" Ai Na'ima ko jin shi bata yi ba kukan ta kawai take yi, banza Abdurrahim yayi da ita har suka isa gida, Abdurrahim da kan shi ya je kitchen ya d'akko mata ruwa yakawo mata yace"amsa ki sha daga kin sha likitan yace cikin zai zube"Na'ima ko kallan Abdurrahim ba tai ba bare yasa ran zata amshi maganin daga hannun shi, kukanta kawai take yi mai tattare da nadamar biyema shawarar zuciya da tayi, dan tasan da tanaimi izinin mamarta bazata bari ta zo k'asar ba bare abin da yafaru da ita har ya faru da ita.
Na'ima kukanta taci gaba da yi tana cewa"wayyo ni ya zanyi in koma gida? Wayyo dan Allah ka tai makamin!" Maganin Abdurrahim ya k'ara mik'a ma Na'ima ya ce" na ce mi ki ki amsa ki sha zaki rabu da cikin yanzu-yanzun nan daga kinsha"Wayyo ni wallahi bazan sha ba sanadiyar mutuwar Jamila kenan, ni kam inajin tsoro inje in mutu!" Abdurrahim kai ya girgiza ya ce " ok ,ashe ko zaki haifi cikin agidanku ,daga nan kuma sai ki naimo Wanda yayi maki cikin!"Abdurrahim na kai wa nan yabar mata gidan ma gabad'aya.
Inda Abdurrahim ya bar Na'ima nan yadawo yasameta, kamar ya wuce sai kuma ya fasa ya dawo, gefanta ya zauna ya ce" Yau she ki ke son komawa gida?" Shiru Na'ima tayi da kukan da take tana kallan Abdurrahim.Shi kuma jin tayi shiru ya kuma cewa" yau she ki ke son koma gida na ce!?" Ni dai ba zan koma da ciki ba gaskiya mamana saita kashe ni, sai dai in da Kaga kai ne kai min ta k'arfi in za ka zo muje ka fad'amata gaskiyar yadda akai in da kaga ni dai ba laifina ba ne" kallan baki da hankali Abdurrahim yayi mata, sannan yace" Ni aina fita hak'inki in da na kawomiki magani kin k'i sha,amma in ki na so in rakaki tom kisha maganin nan sannan"Ni dai gaskiya bazan sha ba wallahi inje in mutu" kafad'a Abdurrahim yamak'e alamun ko ajikin shi, sannan ya tashi ya ce "ki shir ya cikin satin nan zaki koma" yana kai wa nan ya juya yayi tafiyar shi.Na'ima ko cikin kuka ta ce" Ni Wallahi ba zan je gida ba da wannan cikin"Okay, zamu gani "cewar Abdurrahim.
Da daddare koda Abdurrahim ya kwanta kasa bacci yayi dan yana tunanin anya kuwa in ya bar Na'ima ta tafi da cikin nan nan gaba baza asamu matsala ba inda tabbas yasan cikin shi ne, kai gara dai ya matsa mata koda tsiyane ta sha maganin cikin ya zube zai fi samun kwanciyar hankali, nan dai yayanke makan shi shawarar koda tsiya da safe sai ta sha maganin.
washegari Abdurrahim zaune a falo ya gama breakfast yana zaman jiran Na'ima tata shi, yana nan zau ne sai gata ta fito." Ina kwana"Na'ima tace mai "lafiya" Abdurrahim yace. Kitchen Na'ima taje ta had'o makanta tea dan shi ne kawai abin da take iya sha bata amayar ba, in ba shi ba komai ta ci sai tayi aman shi .
Tea d'in Na'ima ta d'akko ta zo falon ,Abdurrahim rik'e da wayarshi yana daddannawa amma kallan Na'ima ya ke afakaice har ta gama shan tea d'in.
"Kin gama shan tea d'in?" Abdurrahim ya tambayi Na'ima, kai Na'ima ta d'aga mai alamun Eh. "Am sa ki sha"Abdurrahim yamik'a mata maganin, amsa tayi tace"Maganin me ye?"
"ki sha magani ne" cewae Abdurrahim.Na'ima juya maganin tayi a hannunta tana kallo ta ce " ni gaskiya bazan sha maganin da bansan ko maganin me ye ba" Abdurrahim cikin jin haushin maganarta ya ce"Maganin zubar da cikin jikinki ne kuma dole ki sha wallahi!" Ni wallahi bazan sha ba" cewar Na'ima tana turo baki, Abdurrahim tashi zaune yayi daga shin gid'an da ke ya ce cikin muryar daga ji kasan ba wasa,
"Sha maganin nan na ce!" Idon Na'ima ruwa yafara kawowa ta ce"Ni dai dan Allah bazan sha ba" fusgota Abdurrahim yayi tadawo kusa dashi, kuka Na'ima ta fasa dan taji zafin musgowar da yayi mata. Abdurrahim zare ma Na'ima ido yayi ya ce"sha na ce!" Na'ima k'ara rik'e maganin tayi da k'arfi tace ni dai wallhi bazan tab'a sha ba".
Abdurrahim rik'e Na'ima yayi ya b'anb'are maganin ahannunta da k'arfin tsiya,sannan ya bud'e bakinta da tsiya ya tura mata magnin ya d'akko ruwa ya tsiyaya mata irin yadda ake ma yara d'ure ya matse hancinta,,, ,,,,,,,,,,,,
AYI HAK'URI DA WRONG TYPING 🙏🏻
🛥️ ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE
📚📚🅙︎𝗮𝗿𝘂j𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚📚🖊
Na
Fadila Sani Bakori.
Page 28 29
Na'ima cikin fitar hayyaci jin yadda Abdurrahim ya matse mata hanci ta fusge kanta ta furzar da maganin daga bakinta. Abdurrahim kallan ta yayi cikin b'acin rai ya ce"ba za ki sha ba Sabo da kina son cikin ko?" Kai Na'ima ta girgiza mai tace cikin jin wahalar matsar da ya yi mata" Ni Allah tsoran sha na ke kuma ni bana son cikin" Abdurrahim tsabar takaici rasa abin da zaice ma Na'ima ya yi, kawai sai yayi banza da ita yafita gidan, Na'ima ko d'akinta ta koma tana kukan ta kai cin cikin, gashi harga Allah tana tsoran zubar