NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 27 of 34

yunwa take ji, garashin k'arfin jiki da ke damunta. Ko inda Abdurrahim yake Na'ima bata kalla ba kitchen ta shiga ta had'a tea tai zamanta kitchen d'in tasha,abin da ya ba Na'ima mamaki duk dad'e war da tayi a kitchen d'in haka ta dawo ta iske Abdurrahim yana ta kewaye falon da takardar scanning d'in ahannun shi inda ita Na'ima batasan ya kai ta asibiti ba inda har yakaita ya dawo da ita bata cikin hayyacinta. Kallan shi Na'ima ta yi ta gefan ido ta tana tunanin ta kardar da ya ke ta faman juyawa ko ta meye ,juwa ta yi zata tafi ," keeee! " Abdurrahim yakira ta, juyowa Na'ima tayi tana kallan shi dan raban da yayi mata irin wannan kiran harta manta. "Wai dagaske ne ki na da ciki?"Abdurrahim ya tambayi Na'ima yana mai k'ureta da ido. "Allah yarabani yin ciki dama fatan da ka ke min kenan? Tom Wallahi bazan tab'a yin ciki ba" cikin kuka Na'ima ta idasa maganar tana kaiwa nan ta juya zata shige bedroom d'inta , da sauri Abdurrahim ya rik'o hannunta ya ce" ke duba nan ki gani" yana nuna mata takardar scanning d'in , zaro ido Na'ima tayi tace"tom ai bani Na'imar ba, wannan bakaga Na'ima Abdurrahim akasa ba? Ni kuma Na'ima Yahaya sunana, kuma ni akan me ma zan yi wani ciki"Na'ima ta fad'i maganar tana turo baki ta ci gaba da cewa "San nan ni ban je asibiti ba" "Zauna "Abdurrahim yace mata. Zama Na'ima ta yi kamar yadda ya'umar ce ta. Shiru Abdurrahim yayi yana kallan Na'ima sannan ya ce"Kin san dai bana miki wasa ko? "Kai Na'ima ta d'aga mai alamun Eh, " Yauwa tom, jiya ba ki da lafiya kika fad'i anan gun ki ka suma na d'auke ki na kaiki asibiti tom shi ne bayan an dubaki suka ban takardar scanning d'in nan da kike gani" zin bur Na'ima tayi ta ta shi tace" Ni wallahi k'arya suke min banda wani ciki!"cikin kuka Na'ima ta fad'i maganar.Shiru Abdurrahim ya yi nad'an lokaci yana tunanin maganarta fa kamar gaskiya ce, yaza ai ace tana da ciki , kallan ta Abdurrahim yayi yace "dai na kuka ni ma da ma banyarda ba"Amsar takardar scanning d'in Abdurrahim ya yi daga hannun Na'ima ya yayyagata ya ce" tom ki dai na kuka kin ga ma na yayyaga takardar ko dan in tabbar masu da k'arya suk dan haka share hawayan kinga dai na yaga takardar ko?" Kai Na'ima ta d'aga mai, "yauwa tom yanzu ki je kiya sallah abinki kin ji?" "Tom "Na'ima tace, sannan ta ta shi ta shiga ciki. Na'ima cikin kwanciyar hankali taci gaba da gudanar da komai nata dan ita bata yarda tana da wani ciki ba kamar yadda shi ma Abdurrahim bai yarda ba. Yau kwana biyu kenan dayin maganar cikin Na'ima kuma cikin kwana biyun bawani zama gida Abdurrahim ya ke ba, lokacin da zai dawo Na'ima kuma ta yi bacci. Yau ta kama weekend Abdurrahim na gida tun safe yake falon dan so ya ke kawai yaga Na'ima , jin shirun ta yi yawa yasa Ya lek'ata yaga ko ta ta shi amma still akwance ya iddata, matsawa Abdurrahim yayi ya d'an bubbugi k'afarta, ido Na'ima ta bud'e tana kallan shi ya ce"Ya dai ? Na ji shiru baki tashi ba" "ban da lafiya ne"Na'ima tace mai." Me ke damunki?" Abdurrahim ya tambaye ta, "jikina ko'ina ke min ciwo, dan Allah yau she zaka k'asar ku d'in? Na k'osa in koma gida ina son ganin Mamana" Shiru Abdurrahim yayi sannan ya ce"tom tashi ki yi breakfast sai muyi maganar zuwa gidan", cikin sauri Na'ima ta sakko, kitchen ta shiga ta samarma kanta abin da zataci dan haka nan sai taji yau tagaji da tea d'in,haka yasa ta dafa taliya, saidai be fi loma uku taci ba ta ji amai nataso mata, da sauri ta ta shi ta k'arasa toilet sai da ta amayar da ita duka. Abdurrahim shiru yayi yana tunanin In ba zai mantaba ya tab'a jin mommyshi nafirar daga tasamu ciki duk abin da taci sai tayi aman shi. Bayan Na'ima ta fito daga toilet d'in ne Abdurrahim ya kalleta ya ce" Shirya mu je asibiti" Cikin k'ank'a nin lokaci Na'ima ta shirya. Wani baban asibiti Abdurrahim yakai Na'ima , yayi ma doctor bayanin abin da suke so, wata roba doctor yabashi yace taje tayi fitsari takawo mai. Abdurrahim inda yabar Na'ima yaje yakai mata rob'ar yanuna mata toilet yace taje tayi fitsari takawo mai, amsa Na'ima tayi taje tayi fitsarin takawoma Abdurrahim shi kuma yakaima doctor, wani d'an ma dai-dai cin d'akin dake cikin office d'in doctor yashiga yayi aune aunan da zai yi sannan ya kawo ma Abdurrahim wata takardar Wanda ke d'auke da bayanan abin da ke damun Na'ima,Cikin fargaba Abdurrahim ya bud'e takardar, sai dai abin da waccan takardar ta fad'a mai ita wannan ta fad'a mai. Abdurrahim cikin zuciyar shi yake mai-mai ta innalillahi'wa inna ilaihirraj'un! Abdurrahim ya dad'e zaune dafe da kai yana tunanin mafita, doctor ya tambaya za'a iya mata theater acire cikin, magani doctor yabashi yace inda cikin baiyi kwari ba yabata tasha zai zube, kud'i dayawa Abdurrahim yaba doctor yakoma inda yabar Na'ima wadda batasan me ke faruwa ba. Abdurrahim suna cikin mota suna tafiya ya kalli Na'ima ya ce" dama maganar da doctor nan gaskiya ne ashe?" Wata magana?" Na'ima ta tambaya. "Maganar ciki mana" "Wayyo nashi ga uku ! , Da gaske ka ke?"
🏠