wannan abarce take ma magana tai banza da ita, Alheri cikin d'aga muraya tace"kee ba da ke na ke ba, ina abincina na ce?"Na'ima gudun fitina dan ba k'arfin jikinta ta ke ji ba yasa tata shi zata bar ma alheri falon. Fusgota alheri tayi sannan ta turata tun k'arfinta zuwa hanyar kitchen d'in.Da yake Na'ima ba k'arfin jikinta ta ke ji ba yasa ta fad'i gun ta ciki,wata uwar k'ara Na'ima ta yi wadda sai da ta ba alheri tsoro, ko da alheri ta duba Na'ima sai taga kamar suma ta yi, sauri alheri tayi ta bar gidan.
Fitar alheri kamar da minti goma Abdurrahim ya shigo gidan, kwance ya ga Na'ima kamar ba rai cikin gigita Abdurrahim ya idasa gurinta yana jijjigata yana kiran sunan ta amma ina batasan yana yi ba tashi yayi da sauri ya shiga kitchen d'in ya d'ebo ruwa ya yayyafamata .Wata doguwar ajiyar zuciya Na'ima ta sa ki ta bud'e idonta tana kallan shi sai kuma tasa kuka, Abdurrahim jawota yayi yajikin shi ya rungumeta yana tambayar ta me ya sa meta, banza Na'ima tayi dashi ta ci gaba da kukan ta, ga kanta da ya ke wani irin jijjuyawa ma ta ga cikinta tana jin ya k'ulle ma ta. K'ok'arin tashi tayi daga jikin shi shi kuma yana k'ara riketa, ya ce"Lafiya wai me ya samekine haka?" Na'ima cikin sanyi ta ce " Ka sakan d'aki zani" Abdurrahim sakin Na'ima yayi yana kallanta, taku bai fi biyu ta yi ba ta yanke jiki ta fad'i agun, da sauri Abdurrahim ya matso ya d'auketa yayi motar shi da ita, a mota ya sata ya kaita wani k'aramin asibiti da ke kusa da su, aiko yana kai ta aka amseta, cikin k'ank'anin lokaci likitan ya gano abin da ke damun Na'ima. Likitan takardar scanning d'in ya ba Abdurrahim da magunguna yace "ko wana lokaci in ta farka zasu iya tafiya" Abdurrahim ko bai tsaya duba ta kardar scanning d'in da likitan ya bashi ba yace ma doctor zai d'auke ta tafarka agida sabo da yana sauri ne" likitan bai mu sa mai ba. Abdurrahim ko da suka shiga gida bedroom d'in shi yayi da Na'ima ya kwantar da ita, tsayawa yayi yana k'aremata kallo haske yaga ta yi mai sosai sai 'yar k'iba da ta d'an yi,Abdurrahim kwanciya yayi gefan Na'ima shima ya jawota jikin shi yana shafa kanta sosai yake jin Na'ima na burge shi ,haka Abdurrahim ya yi ta wasa da sassan jikin Na'ima ,haka ya tsinci kan shi cikin nishad'i,Abdurrahim matse Na'ima ya kuma yi sosai ajikin shi rigarta ya d'aga dan ba abin da ahalin yanzu yaji yana son gani kamar k'irjinta sosai shaid'an ke k'ara k'awata mai ita.
Ita ko Na'ima da bata san abin da ke faruwa ba k'ara shigema Abdurrahim tayi jin d'umin jikinshi sai yayi mata dad'i. Abdurrahim ko jin Na'ima nak'a shige mai ai sai yak'ara kaimi wajan abun da yakeyi mata, bakinsu ya had'e guri d'aya yana mata zazzafan kiss,haka Abdurrahim yayi yadda ya ke so da Na'ima . Bayan komai yalafane Na'ima ta fara jin yungurin amai tashi tayi dakyar tashiga toilet d'in shi tai ta kwara amai.
Alheri da dawowarta kenan gidan ta kardar scanning d'in da ta gani da magunguna ta k'arasa ta d'akko tana dubawa. "Ciki"Alheri tace da k'arfi, Abdurrahim ko dama Na'ima na shiga toilet d'in shi ya fita daga d'akin ya shiga nata toilet d'in da sauri yayi abin da zai yi dan so ya ke yayi ya kintsa jikinshi dan lokacin sallar magriba yayi, yana fitowa yazira jallabiyar shi yafita falon, alokacin kuma alheri ta d'auko takardar scanning d'in Na'ima tana gani, dai-dai lokacin da take cewa" ciki" Abdurrahim ya fito ya kuma ji abin da ta ce.
Abdurrahim Kallan rashin fahimta yayi ma alheri ya ce" Ciki kuma?Wa ke da cikin?" Yarinyar da ka ke tare da ita mana, yarinyar da ka ce wai taimakonta ka ke yi ita ke d'auke da cikin shege na tsawan wata d'aya ga shi nan likita ya rubuta muku baku gani bane...........
A yi hak'uri da wrong typing 🙏🏻🙏🏻🙏🏻
NI NA YI NAN DAN NAGA ABDURRAHIM YA TSORATA DA JIN LABARIN CIKIN NA'IMA🏃♀️🏃♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️
🛥️ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.
📚📚🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚📚🖊
Na
Fadila Sani Bakori
1)SO NE SILA
2)OGA HABIB
3)IN DA RAI
4)DAGA ALLAH KO D'AURA MA KAI
5)RAYUWAR HAIDAR
6) MENALLYN DADDY
7) ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE
Page 26 & 27
Cikin rud'ewa Abdurrahim ya fusge takardar hannun alheri yana karantawa, wata irin zufa Abdurrahim yaji tana keto mai kota ina, kallan alheri yayi ya ce" alheri ban yarda ba zo ki dubata dan Allah wannan ma ai shirman banza ne yaza ai ma ce wai tana da ciki akan me?" Wani irin kallo alheri ke ma Abdurrahim, Abdurrahim ko hannun alheri ya kamo ya ce"dan Allah mu je ki duba yarinyar nan danni ban yarda ba Wallahi ace wai tana da ciki" cikin masifa alheri ta fusge hannunta tace" bazan duba ta ba d'in!" tana kaiwa nan ta d'au wayarta tafita daga gidan gabad'aya.
Abdurrahim zagaye d'akin ya ke ta yi dan ya ka zama, ana cikin wannan yanayin ne sai ga Na'ima ta fito falon dan samar makanta abin da zata ci dan wata irin