ga Motar nan ba ai na riga na gama zaman gidanka inda kai baka da amana ba zan tab'a komawa ba har abada".
Abdurrahim zamanshi yayi a Motar, ya da d'e yana kallan Na'ima ita kuma sai kau da kai take alamun bata son kallan da yake mata, cikin natsuwa Abdurrahim yafara magana kamar haka "Na ji ba za ki koma gidana ba yanzu ina zaki tom? "Ba bu ruwanka da inda zani" Cewar Na'ima.
Shiru Abdurrahim yayi sannan zuwa can ya ce" Shikenan za ki iya tafiya, sai dai ki sa ni nan ba Nigeria ba ce abin da ya fi abin da naimiki zai iya faruwa da ke, sannan za ki iya had'uwa da masu yan kar kai dan mu nan da ki ke gani akwai restaurant d'in farfesun naman mutane amma in kin ga za ki tafi tom badamuwa za ki iya tafiya"Shiru Na'ima tayi tana tunani sannan zuwa can tace"dan Allah ana yanka mutane da gaske anan? Ka fad'a min gaskiya"Kin ga ne je ki kawai, ni da ma taimakonki naso yi dan kar nukan garin nan da ki ke gani zasu iya cin ye ki ma kafin ki had'u da masu yanka muta nan"Abdurrahim na kai wa nan ya bud'e murfin mutar zai fita, da sauri Na'ima ta kamo hannun shi tace" dan Allah tom zan koma gidan naka wallahi ina tsoran kar nukan garin nan da masu yanka mutane dan Allah zan bika amma dan Allah ba za ka sake cin amanata ba?" Kai Abdurrahim ya d'aga ma Na'ima alamun Eh, "yauwa tom na gode,nama kusa yafema k'ila" Cewar Na'ima. "Tom na gode"
Ta re suka shiga falon gidan, kayan da Abdurrahim ya siya ma Na'ima ne ya d'akko ya aje mata a gabanta ya ce"Ga kaya nan na siyo mi ki ki ta sawa abin ki" Na'ima kallan kayan ta yi tace"Ni dai ba kaya nake so ba So nake ka taimaka ka mai da ni garinmu dan Allah"Na'ima ta ida maganar tana zubar da hawaye.
Shiru Abdurrahim ya yi na d'an lokaci sannan ya ce"Ki bari k'arshen watan nan ne zan je gida ba kin ce Kaduna ki ke ba? " Kai Na'ima ta d'aga ma Abdurrahim alamun Eh.Abdurrahim yaci gaba da cewa" tom ki bari sai mu wuce tare" A'a ni dai ina so in fara wuce wa" Cewar Na'ima, "Shikenan sai kin dawo in ki na da kud'in Jirgi" Abdurrahim na kaiwa nan ya tashi yayi shigewar shi ciki ya barta.
Na'ima ma tashi tayi ta shiga kitchen ta sa mar ma kanta abin da zata ci.
Yau Sati hud'u ke nan da faruwar abin da yafaru tsakanin Abdurrahim da Na'ima.Alhamdulillah ko hannun Na'ima Abdurrahim bai sake ta b'awa ba, sai dai zaman nasu ya canza salo, dan yanzu sukan sauna suyi hira bakamar da ba, hakan ya d'an rage ma Na'ima abin da ke damunta dan wani lotun in ta gaji da zaman gidan har addu'a take Abdurrahim ya shigo tasamu abokin hira.
Yanzu haka zaune suke suna hira duk da yawancin hirar Na'ima ke yin ta.
Na'ima kallan Abdurrahim ta yi tace"yauwa dan Allah me ya sa ka kori alheri a gidan nan? "Kallanta Abdurrahim ya yi ya ce"Na koreta kuma?". "Tom banaga ta zo tana kuka ba ta kwashe kayanta"Oh! Babanta ne yarasu" Ayyah shi yasa ta ta tafi..." Bugun k'ofar gidan da suka ji ana yi ne yasa su kai shiru ,Abdurrahim yana mamaki dan ba wanda su ka zai zo wajan shi, tashi yiyi ya je ya bud'e k'ofar cikin mamaki ya ke kallanta dan shi ya ma manta da ita, kallan shi alheri tayi tace" dama irin damuwar da ka ke cewa kayi dani kenan ko? Daddyna ya mutu amma so d'aya ka kira kai min ta'aziya me ya sa?"
Abdurrahim hannun alheri ya rik'o ya ce"Yi hakuri zo mu je ciki in fad'a mi ki dalilin rashin kiranki da banyi ba" Hannunta Abdurrahim ya kamo har Falon, haka nan Na'ima sai ta ji ba ta ji da d'in hannun alheri da Abdurrahim ya rik'e ba.
Alheri ko zama tayi tana wani cicin magani ganin Na'ima da tayi dan ta d'auka tsawan wannan lokacin ta wuce.
Abdurrahim ko kallan alheri yayi ya ce "kin gane ko abin da yasa ban kiraki ba na yarda Wayana ne tom shi ne fa narasa number ki"Shikenan ba damuwa"Cewar alheri.Alheri nuna Na'ima tayi tace" Abdurrahim wannan yarinyar tana nan kenan?"Kai Abdurrahim ya jinjina ma ta.Alheri ta ce"Ta'iya girki? "Shiru Abdurrahim yayi kamar ba zai bata amsa ba sai kuma yace"in ta'iya ya akai?" "Dama na gajine isowata kenan ta d'an dafamin ko indomie ce"Abdurrahim kallan Na'ima yayi ya ce "Na'ima je ki dafa mata indomie taci kin ji yanzu ta iso" Haka nan Na'ima sai ta ji ranta ya b'aci sa ta d'in da Abdurrahim yayi ta yi ma alheri girki .
Ba dan Na'ima ta so ba ta shiga kitchen ta soya ma ta indomie ta kawo mata.
Tun daga ranar yazamana Na'ima ita ke masu girki dukan su, tsakanin ta da alheri ko sai dai harara, amma magana ko gaisuwa bata had'asu, tsakanin Na'ima da Abdurrahim ko sun dawo kusan 'yar gidan jiya hakan yasa Na'ima sai ta ji duk haushin su ta ke ji gashi yawan cin 'yan kwanan nan bata jin k'arfin jikinta ga wani irin ciwan kai da ke damunta ga yawan fad'uwar gaba da ke da munta ,hakan yasa yau ko girkin ma ta kasa yi ta had'a tea ta sha tai kwanciyar ta .
Na'ima na nan kwance alheri ta shigo gidan wacce dawowarta kenan daga aiki, ko kallan ina Na'ima take alheri bata yi ba, wayarta ta d'akko tana danne-danne sai zuwa can tace" kee ina abincina?" Banza Na'ima ta yi da ita, alheri kallan Na'ima ta yi da mamaki wai