NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 20 of 34

" murmushi Abdurrahim yayi yace "Badamuwa ai tawani b'angaran aikin taimako ne, haka kwanaki fa na tsinci wata yarinya igiyar ruwa ta jawo acikin ruwa ,sai dai nayi parking cikin ruwa na d'akkota "Na'ima da sauri ta kalli Abdurrahim dan ta ji ajikinta bawata bace ita ce dagaji, aiko zata gwada tambayarshi taji itace" Hafiz cikin al'ajabi ya ce"Amma broz ta mutu?"A'a bata mutu ba"Abdurrahim ya kauda maganar da cewa" Kai nagaji sosai" Hafiz kallan shi yayi ya ce "Broz asama abinci ko?"No nak'oshi, sai da naci abinci na k'oshi sannan nadawo" Abdurrahim tashi yayi ya shiga ciki dan bak'ad'an ya gajiba, ya yi ma Hafiz saida safe ya shige ciki yabar Na'ima da Hafiz agun. Hafiz kallan Na'ima yayi yace"Auntna Allah bakyakulawa da broz sosai fa amma ki tsaya yanga wata ta kwace broz, duk da naga shima kamar irinki ne,ko dai dan kunganni ne?, amma idan har kina ganin kamar auran tausayi yayi dake yasa kikakasa bashi kulawa gaskiya shawara nake baki ki canza ki kula da mijinki da kyau kafin wata ta rigaki" Shiru Na'ima tayi tana sauraran Hafizs ji tai kamar ta fad'amai gaskiya ita ba matar Abdurrahim bace, amma tana jin tsoran kar Abdurrahim ya koreta gidan kuma batasan inda zata ba. Hafiz ko ganin Na'ima ta shiga tunani ya ce" yanzu dai duk ba wannan ba" ki ta shi ki je ki kula da mijinki" Na'ima cikin inda-inda ta ce "Gaskiya ni nan zan kwana" Haba Auntyna me ya sa ki ke yin haka ne mijinki ne fa!" Na'ima ba ta jin dad'i in taji yace wai Abdurrahim mijinta ne. Hafiz ko haka ya tasa Na'ima da naci da magiya sai da ya turata d'akin Abdurrahim. Na'ima ba dan taso ba sai dai ta rasa yadda zata zillema Hafiz haka ta hak'ura ta shiga d'akin da sand'a dan kar Abdurrahim yaji zuwanta,inda Allah ya taimaketa Abdurrahim yayi barci dan ya gaji sosai kamar yadda yace. Na'ima daddumar sallarshi ta d'akko ta shimfid'a ta kwanta ak'asa , sai dai kasa bacci tayi sabo da sanyin k'asan haka taita juye-juye ,asubar fari talallab'a kafin Abdurrahim ya tashi tai saurin barin d'akin. Yau satin Hafiz d'aya da zuwa kenan,shak'uwace sosai ta shiga tsakanin Hafiz da Na'ima kuma har yanzu Hafiz bai san Na'ima ba matar Abdurrahim bace, kullum Na'ima tare da Abdurrahim suke kwana d'aki d'aya sai dai Abdurrahim bai tab'a sanin Na'ima d'akin shi take kwana ba, sabo da ba ta shiga d'akin sai yayi barci haka zataitajan Hafiz da fira dan Abdurrahim yayi barci kafin ta shiga ,bata yadda ya tashi ya ganta zatayi sammakon barin d'akin. Dan Hafiz ba ya yadda ya kwanta sai yaga shigar Na'ima sannan. Yauma kamar kullmum Hafiz Ya ce" Auntna yau kije ki kwanta da wuri dannima barci nakeji" Na'ima k'in tashi tayi haka taita jan Hafiz da hira har sai ta ta tabbatar Abdurrahim yayi barci sannan tayima Hafiz sallama ta tashi ta shiga cikin sand'a kamar yadda ta saba, saidai me tana shiga taga Abdurrahim.............. Ayi hak'uri da wrong typing👏🏻 Masu naiman Abdurrahim matuk'in jirgin ruwa daga farko basu samu ba zasu iya magana ta numbar nan 08063830828 🛥️ABDURRAHIM🛥️ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE. 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚* Na Fadila Sani Bakori. Afuwa kwana biyu shiru🙏🏻🙏🏻 Page 20 & 21 Zaune Na'ima ta iske Abdurrahim yana daddan na wayarshi,bak'aramin shock ta ji ba gashi yaganta bare ta koma dan saida ya d'ago kai ya kalleta sannan ya yacigaba da danna wayar. Tsayuwa Na'ima tacigaba dayi abakin k'ofar dan takasa k'arasawa.Abdurrahim bai tankamataba cigaba da danna wayarshi yayi ita kuma da alama bata gaji da tsayuwar ba. "Lafiya? "Abdurrahim ya tambayi Na'ima. "dama Hafiz ne yadaman saidai in zo nan in kwanta" Inda ki ke kwana fa?" Shiru Na'ima tayi tana najarin abin da za ta ce ma Abdurrahim inda dai duk kwanan da ta ke yi d'akinshi bai sani ba. Na'ima cikin rashin sanin mafita ta ce "tom kullum haka yake min ai sai ya rako ni dole"Abdurrahim da bai gane maganar Na'ima ba ya ce "Ina ki ke kwana na ce? "A nan!" Na'ima taba Abdurrahim amsa kai tsaye. "Anan kuma?"Abdurrahim ya mai-mai ta, kai Na'ima ta d'aga mai ,Abdurrahim da mamaki ya bar abin da ya keyi ya tsaya yana kallan Na'ima ya ce "Wato sai nayi bacci ki ke lallab'owa ki shigomin d'aki ko? "Na'ima kanta ak'asa tana wasa da yatsun hannunta ta ce"Hafiz ne ke takuramin amma bada son raina ba" Banzan Abdurrahim ya yi da ita yagama danne-dannan wayarshi ya kwanta yana jiran yaga ina take kwanciya in ta shigo. Na'ima ko ci gaba da tsayuwa tayi sai da ta kintati lokacin da take tunanin Abdurrahim yayi bacci sannan ta lallab'a ta hau gadon ta d'akko addumar sallarshi ta shimfid'a ta kwanta ak'asa, saidai Na'ima batasan duk abin da take ba da ido d'aya👁️ Abdurrahim ke kallanta,Abdurrahim ko yana nan yana tunanin yadda zai b'illoma Hafiz akan haka har bacci kwashe shi. Kamar yadda Na'ima tasa ba tashi haka ta tashi ta shiga kitchen ta had'amasu abin kari suka karya kamar yadda suka saba. Bayan wata d'aya. Wata irin shak'uwa
🏠