NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 2 of 34

" A'a yaya Jimmai kune barkanku da zuwa ,yaya Rabi'u ,yaya Ya'u ku zauna mana ga guri ya shimfid'a musu tab'armar kusa da shi ". Bayan sun Zauna ne anyi gaishe-gaishe jimmai tace" Ya'u Ka fad'ama Yahaya abun da muke tafe da shi. Wanda akakira da Ya'u kara gyara zama yayi sannan ya kalli Yahaya ya ce" Yahaya game da auran Na'ima ne tom mun yanke shawarar k'arshan watan nan za a d'aura auran Na'ima da gali kamar yadda muka sanar da kai akwanakin baya. Ba Na'ima ka d'aiba hatta malam Yahaya da mama idan ka kalle su zakaga tsantsar furgici a fuskar su. "Munji shiru Yahaya kai muke saurare "cewar Rabi'u. Numfasawa Malam Yahaya yayi sannan ya ce "Dama ni yaya Rabi'u wani hanzari ba gudu ba nace dama inda ita Na'imar tadage bata son gali mai zai hana abashi w........ "K'arya kake wallahi dama ba ra'ayinka kona Na'ima mukazo ji ba a'a mun zo ne muce muku ku shirya k'arshan watan nan zamu d'aurama Na'ima aure da gali" Mahaifin Na'ima numfasawa yayi sannan ya ce " Yaya Rabi'u ina gudun abun da nasani ne nan gaba shi yasa bawani abu ba ind...." Hannu Rabi'u ya d'aga mai yace " Ya'isa hakanan!,Yaya jimmai ku tashi mu tafi " Cikin hanzari Na'ima ta kama k'afar jimmai tace" Gwaggo dan Allah ki taimakan wallahi nayarda zan auri koma waye amma bana son yaya ga......" marinda Ya'u yawanka ma ta ne yasa takasa karasa abinda tayi niyya cikin wata kid'ima da rawar jiki ta kama kafar Rabi'u tace" Baba Rabi'u kataimakan karku aura min......."Wata in giza Rabi'u yayima Na'ima wadda mahaifiyar Na'ima batasan sanda taje da sauri zata rik'e taba amma ina sai datakai kasa cikin wahala da azaba Na'ima ta fasa wata uwar kara kafin kace me sai ga jini na zuba abakinta. "Aunty jimmai,Yaya Rabi'u, yaya Ya'u ku yi hak'uri bazan iya aurar da Na'ima ba agun Wanda bata so" cewar malam Yahaya mahaifin Na'ima. "K'arya kake aure dama bakai ka had'a ba Allah ne yahad'a dan haka kamar anyi angama ne" cewar yayar su jimmai tana kai wa nan ta ce "ku muje Rabi'u " . Allah sarki malam Yahaya daya rasa abunyi sai ya fa she da kuka cikin kid'ima Na'ima da sauran k'annanta suka karasa wajan babansu, Hassan ne ya zaunar da shi yace dan Allah kabar kuka baba yawuce. Na'ima kallan Mahaifinta ta yi da ke kuka ta ce" Baba dan Allah kabar kuka ni na yarda zan auri yaya gali" kai mahaifin Na'ima ya girgiza ya ce" A'a Na'ima bazaki auri gali ba" Mahaifin Na'ima ya fad'i maganar yana mai d'aukar butar dake kusa da shi yanufi hanyar bayi tari ne ya turnik'e shi ya fad'i gurin, da sauri Na'ima ta karaso gun tarik'eshi ganin yadda yake tarin ta ce" Baba dan Allah ka kwantar da hankalinka ni na yadda zan aure shi ". Mahaifin Na'ima Kiran sunan Na'ima yayi har yanzu cikin tarin yake ya ce "Na'ima indai ni ne mahaifinki tom bazaki auri gali ba" " Amma baba kaji yadda su gwaggo jimmai suka ce" Kai Manaifin Na'ima yake girgiza mata magana yake son yi amma tari yahanashi yi, mahaifiyar Na'ima ya yafito da hannu, da sauri tak'araso inda yake. Cikin rawar murya mahaifin Na'ima ya fara magana kamar haka " Ma.ri. ya ko bayan raina banyarda Na'ima ta auri ga.. li ba" cikin sar kewar harshe yake maganar, tarinda yaci k'arfin shine yasa basa jin abinda yake cewa sai kalmar shahadar shi sukaji, cikin gigita mama ke girgiza shi ganin baya nunfashi. Cikin kuka mahaifiyar Na'ima ke girgiza shi tana cewa" Malam dan Allah kar kai mana haka dan Allah katashi. " Kullunafsin za'ikatul maut rai ya riga yayi halinshi. Kukan su Na'ima ne ya shigo da mak'ocin su......... 🛥️🛥️ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE🛥️🛥️ (RENEW) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚* Na Fadila Sani Bakori Page 2 & 3 Allah sarki duk mai rai mamaci ne, haka akayi zana'idar malam Yahaya aka kai shi gidan shi na gaskiya. Ranar sadakar bakwai haka 'yan'uwan Malam Yahaya suka taru akai addu'ar bakwai. Bayan mutane sun tafi ne Yayyan marigayi suka nemi suna son magana da Mahaifiyar Na'ima da Na'ima, bayan sun nemi gune sun zauna suka sake yima mama gaisuwar rashin Mijinta,sannan wan mariyagin ya fara magana kamar haka "Mariya yau ne akai addu'ar bakwai na d'an'uwan mu Masha Allah, Allah ya jaddada rahamarsa agaresa" Yacigaba da cewa" Mariya nasan kin sanda maganar auran Na'ima da gali ko?" Mahaifiyar Na'ima dai bata ce mai ko mai ba. Yaci gaba da cewa "Tom kamar yadda mu ka tsaida k'arshen watan nan ne auran Na'ima da gali, tom yana nan yadda yake bazamu d'agaba, yanzu zamu d'auki buhun dawar shi uku da yayi saura mu saida kud'in mu had'a mu yi ma Na'ima kayan d'aki dasu, ina fatan haka ya yi mi ki? "Ya tambayi mahaifiyar Na'ima. Allah sarki Mahaifiyar Na'ima rasa abinda zata ce mai tayi, kai kawai tad'a ga mai. " Tom ai shike nan inda hakan yayi mata ku tashi mu tafi yace ma sauran abokan tafiyar nasa, " Yau saura kwana goma d'aurin auran Na'ima kamar yadda yayyan Mahaifinta su ka ce. Na'ima zaune kusa da Mahaifiyarta so ta ke tayi mata maganar auranta da gali ganin loka
🏠