n sanyi irin yadda kake so,Allah da gaske nake broz ina kamun k'afar k'anwarta dan karma arigani"Ita dai Na'ima murmushi ta yi dan taji dad'in yabata d'in da Hafiz ya yi gashi yana bata dariya.
Abdurrahim ko hararar shi yayi bai tanka mai ba.
Bayan Hafiz ya gama shanye tea d'insa ne, Abdurrahim yaja shi suka fita su kai sallah daga nan suka shiga gari duk da Abdurrahim bawani mai yawan dare bane basu suka dawo gidan ba sai 11:20 pm alokacin Na'ima ta dad'e da yin barci,rashin sanin inda zata kwanta yasa ta kwanta a falon inda gidan 2 bedroom ne .
Hafiz ko da suka shigo yaga Na'ima kwamce a falo ya ce " kai! Kai!! Kai!!! broz yau ka yi laifi fa? "Abdurrahim cikin rashim fahimtar Hafiz ya ce"Laifin me? "Hafiz Na'ima ya nuna ma Abdurrahim da ke kwance tana bacci abin ta dan daga ganin barcin kasan tayi nisan kiwo.
"Broz kalli inda amarya ta kwanta fa daga gani kai take jira ,ni karka jamin tabar ban abinci kafin in
wuce"Banza Abdurrahim yayi da shi dan shi dama baya iya ma surutun Hafiz, kallan shi Abdurrahim yayi ya ce"Inkagama zubar sai kazo innunama inda zaka kwanta"A'a broz kyau kafara kai Auntyta taci tukun" Kai Abdurrahim ya sosa ya ce"Kai bataso in ta yi barci atadata barta anan kawai in ta tashi ta shiga ta kwanta" Haba broz daga gani fa zaman jiran mu take gaskiya ya kamata katadata taga dawowarka dan k'ilama da fushinka tayi barci"Kai bana son shirme kazo mu je ka kwanta".
Hafiz da yake irin mutanan nan ne masu naci sai cewa yayi "Broz gaskiya bazataji dad'i ba ta tashi ta ganta a falo kwance zataka kamar danni ne ka juya mata baya kuma kaga laifina zata gani kasa tabar banu abinci"Hafiz ya k'arasa maganar da barkwancinsa.
Abdurrahim gaba ya yi yana mai cewa"Inkashirya kwanciya ka kashigo ka kwanta ni nayi nan inda kai naga alamar bakajin barci magana kake jin yi"Hafiz bin Andurrahim yayi yana dariyar maganar Abdurrahim d'in.
Inda Na'ima ke kwanciya Abdurrahim ya kai Hafiz ya kwanta.
Washegari Na'ima koda ta ta shi fuska kawai ta wanke kasan cewar ba sallah take ba, Kitchen ta shiga tana tunanin abin da zatayi ma bak'onsu, nan dai tayanke shawarar d'ora ruwan zafi ta had'a mai tea inda bawani abu su ke da shi ba sai ya siyo kamar yadda taji yace jiya.
Na'ima bayan ta kammala ne ta koma Falon ta gyara bayan ta gama gyara falonne ta koma kitchen d'in shima tana gyarawa,tana cikin aikin ne Abdurrahim ya leko ya ce"Sannu da aiki"Yauwa" Na'ima tace cikin girmamawa dan Na'ima akwai ladabi daganin mutumcin Wanda yake sama da ita.
Hafiz ko da yatashi sai da yayi wankanshi sanna yafito falon alokacin Na'ima na zaune tana shan tea, shi kuma uban gayyar yana zaune nesa da ita yana danna waya. "Good morning Auntyna " cewar Hafiz yana murmushi.
Na'im ma murmushin tayi mai sauti sannan ta ce"Barka da safiya, ka tashi lafiya, ya gajiyar tafiya?" Lafiya klau Auntyna, ina'iya zama?"Sosai ma kuwa"Na'ima ta ce tana mai murmushi. Zama Hafiz yayi d'an nesa da Na'ima.
Banyan sun gama karyawa ne dan har Abdurrahim sai da yasha tea d'in dan yalura da yarinyar batada k'azanta sannan ya ce" tom kai sai ka ta shi mu je asiyo abubuwan buk'ata na dafawa, na sanka sarkin jin yunwa ne kai" Dariya Hafiz yayi sannan ya tashi suka fita.
Na'ima na ganin fitarsu ta tashi ta shiga toilet d'in da ta saba shiga tayi wanka tasa d'aya daga cikin dogayan rigunan da Abdurrahim ya ba alheri ta siyo mata. Na'ima na gama shiryawa yayi daidai da da dawowarsu Hafiz.
Hafiz cikin tsokana yake Kiran Na'ima ya ce "Auntyn gashi angonki yace yau ki yi girkin da yafi na kullum dad'i"Na'ima fitowa tayi tana murmushi ta amshi cefanan da sukayi ta shiga kitchen d'in. Tare da Hafiz suka shi ga kitchen d'in hatta aikin tare sukayi tun Na'ima na d'arid'ari da Hafiz har tasaki jiki suna aikinsu tare suna hira dan tafahimci Hafiz mutum ne mai sauk'in kai bakamar yayan shi ba.
Abdurrahim ko dama suna dawowa cefanan ya tafi wajan aiki bashi ya dawo gidan ba sai dare.
Hafiz ko ganin yadda Abdurrahim ya dad'e ya ce"Auntna wai dama haka broz yake da d'ewa?" Shiru Na'ima tayi dan yaune yayi haka,sai zuwa can ta ce" Gaskiya yana dawowa da wuri k'ila wani abunne yarik'e"Hafiz numa Na'ima agogon hannunshi yayi ya ce kalla 9pm fa? " Shiru Na'ima tayi dan itama tafara tunanin ba lafiya ba dan aiya zamanta da Abdurrahim ta lura shi ba irin mazannan bane masu firar dare awaje.
Hafiz ko jin Na'ima tayi shiru ya ce "Aunty Amarya kin yi shiru?" Nima na fara tunanin k'ila ba lafiy,,,, " Turo k'ofar da akayi ne ya hanata k'arasa abin da tayi niyyar cewa.
Abdurrahim zama yayi kusa da Hafiz ya ce" kaji na dad'e ko? "Kai Hafiz ya d'aga mai alamun Eh.
" Kabari kawai wallahi bansan me ya faru ba yanzu ake yawan samun accidents d'in jirgin ruwa ba 'yan kwanan nan, kwanan nan fa ba afi wata d'aya ba akayi wani akarasa ran mutum da dama amma ikon Allah kaga yau aka sake yin wani" Wai gaskiya broz kuna aikin gan-ganci, ni me yajani in rasa abun da zanyi sai tukin jirgin ruwa wai!,sannunku