NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 34

tom dole ce tasa haka dai yarinyar marainiya ce"Hafiz da tsatsanin mamaki ya kuma cewa "Aure kuma broz? "Eh aure ka ga na huta da surutun su mommy ko, sannan kuma nayi surprise d'inku" Hakane" cewar Hafiz dan shi yayarda da maganar yayan nashi. Itako Na'ima kafin su shigo tabar falon dan ta lura b'ako yayi kuma bayason yaganta shiyasa tayi shigewarta ciki bayan sun shigone Abdurrahim yace ma Hafiz yana zuwa , d'akin da Na'ima ta shiga ya shiga zaune ya isketa tayi ta gumi, kallanta Abdurrahim yayi nad'an lokaci haka nan sai yaji yanajin nauyin fad'amata abin da ya ko son fad'a,sannan dai ya daure ya ce" kee ya sunan ki? " Na'ima kallan Abdurrahim tayi sannan ta ce" Na'ima" Yauwa to nayi bak'o k'aninane yazo uwarmu d'aya ubanmu d'aya, tom akwai damuwa yaganmu tare kuma ke baki da inda zaki, ko kinada inda zaji?" kai Na'im ta girgiza mai alabun bata da shi.Abdurrahim yaci gaba da cewa " Tom nace mai ke matata ce, dan haka sai kirik'a behavioural kamar matata kingane ko........... Ayi hak'uri da wrong typing 👏 🛥️ ABDURRAHIM 🛥️ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE. 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚* Na Fadila sani Bakori Page 18 & 19 Shiru Na'ima tayi tsabar al'ajabin maganar Abdurrahim,Abdurrahim kuma jin Na'ima tayi shiru ya kuma cewa "Wai bi ki ji ba ne? Nace kirik'a behavioural kamar matata idan ba haka ba da akwai damuwa idan Hafiz yaje gida ya sanar ina zaune da mace kin ga dole zasuyi wani zargin da bahaka ba ne ".Kai Na'ima ta d'agama Abdurrahim alamun ta gane. Shiru Abdirrahim yayi sannan ya ce"Yauwa kin iya girki ko? Kinga munyi bak'o kuma yanada buk'atar abinci"Nan ma dai Na'ima kai ta d'aga ma Abdurrahim alamun Eh."Oh"Abdurrahim Yace ya ce " Kirik'a amsamin da bakinki mana" Tom"Na'im tace ahankali. "Yauwa tom yanzu bari in koma falon kar ya jini shiru" 'Hafiz mutanan England" cewar Abdurrahim da fitowar shi falon kenan. Hafiza da fara'arshi ya ce dan shi mai fara'a ne"Broz Allah maganar auran nan taka ta d'aure min kai, dama zaka iyayin aure ba da saninsu mommy ba? "Kabari kawai Hafiz yarinyar auran tausayi nayi da ita bawai so ba ne, yanzu haka sonake Idan nagama shirina in kaita mahaifarsu"Hafiz da mamaki ya kalli Abdurrahim ya ce "Mahaifarsu kuma? Tom auran fa? " Tom Hafiz ina tsoran karsu mommy su k'i aminta da auran ,gara idan nai musu bayani suka aminta sai inje garinsu in kaita nan wajansu" Shiru Hafiz yayi yana kallan Abdurrahim bai ce komai ba,Abdurrahim kuma yaci gaba da cewa"Nasan kanada surutu saura inji maganar auran nan bakin mommy dan nafi so in sanar da ita da kaina, kaji dai abin da nacema ko? "Insha Allah broz bazataji ba,inda baka son ta sani abakina" Nan dai kowa yayi shiru da tunanin da yake ,sai zuwa can Hafiz ya kalli Abdurrahim ya ce " Tom ita Auntyn ta wa bazata zo mu gaisaba ne? " Kai Abdurrahim ya sosa ya ce"Bari inje in fito da'ita" Na'ima na kwance tanajin motsin alamun shigowa tai sauri ta ta shi ko inda take Abdurrahim be kallaba ya ce" So ki ke ki ruguzamin plan ko? Tom rugujewar plan d'in nan dai-dai yake da barinki gidan nan duk inda zaki kije babu ruwana, yanzu in kiga dama ki zo ku gaisa"Abdurrahim na kai wa nan yafita abinsa. Bayan shi Na'ima tabi da k'ak'aro murmushin dole na tarbar bak'o tana zuwa falon ta ce"Snnu da zuwa"Tana fad'i maganar tana mai zuk'unnar da kai kamar wadda tayi k'arya asirinta yatonu. kallanta Hafiz yayi mai makon ya amsa gaisuwarta sai cewa"Wow broz your wife she is very very beautiful, gaskiya ka'iya zab'e" Sannan ya maida kallan shi ga Na'ima ya ce " Auntyna kin ganki kuwa? kamar ke kikayi kanki, dan Allah ki na da k'anwa ina rik'o" Da ya ke Hafiz irin mutanan nan ne masu b'arkwanci. Abdurrahim kallan Hafiz yayi yad'an harareshi dan shi atunaninshi jawo rainine hakan na kod'ata d'in da yayi. Sai zuwa can Abdurrahim ya ce dan katse Hafiz d'in "Tom malam idan kagama zub'ar sai katashi karakani inyoma cefane aimaka wani abun kaci"Kai broz nagaji fa, kawai taimin simple food ya'isa" kafad'a Abdurrahim ya d'aga irin ko ajikin shi, kallan Na'ima yayi yace" Tom kinji ki mai abu mai sauk'i kwai" Na'ima bata amsaba ta juya ta shiga kitchen d'in ,rasa abin da za tai mai tayi. Abdurrahim ko sanin hakan zata iya faruwa yasa yabiyo Na'ima kitchen d'in, tsaye yasa meta tayi tagumi daga gani tayi nisa aduniyar tunani, table d'in dake kusa da ita ya d'an buga, ya ce" Dafa mai ruwan zafi yasha tea sai ki soya mai k'wai kawai" Na'ima kai ta d'ama Abdurrahim,Abdurrahim harararta yayi ya ce "Ki natsu bawai kirik'a abu kina duk'ar da kai ba kamar wadda asirinta yatonu tayi gulma ba" kai Na'ima ta kuma d'aga mai alamun tom.Abdurrahim kuma juyawa ya yi yabar kitchen d'in. Cikin minti goma Na'ima ta gama had'a mai tea d'in ta soya mai kwai ta ta d'ora a plate ta kai mai. yauwa sannu da aiki Auntyna, murmushi Na'ima tayi mai ta ce"kai sai kace wani aiki mai yawa"Wow broz kai mai sa'ane voice d'in mai kwantacca
🏠