NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 17 of 34

halin yanzu yarinyar tausai take ba shi.Abdurrahim kallan Na'ima yayi ya ce "Sai dai me?" Na'ima cikin jin nauyi ta ce "Dan Allah in karage abinci ina jin yunwa"Meyasa bik,,,,," banko k'ofar da alheri tayi ne yahana Abdurrahim k'arasa abin da yayi niyya kallan shi alheri tayi sannan tace"Abdurrahim kana ganin abin da yarinyar nan tayi min jiya amma bazakazo dubani ba ko?" Ke da Allah malama nazo dubaki kin tafi yawanki" Shiru alheri tayi dan tabbas bad a gida take ba.Alheri kallan Na'ima tayi da ke tsaye da alamun magana suke da Abdurrahim ,alheri ta ce" Tom shikenan, amma jiya ai naji kace kakori yarinyar nan ya akai ta dawo?"Abdurrahim batare da ya kalli alheri ba ya ce" Sabo da bata da inda zata shiyasa ta dawo " Shiru alheri tayi sannan zuwa can ta ce " Yanzu kana nufin ta dawo nan dazama kenan? " Abdurrahim da yagaji da tambayoyin alheri banza yayi da ita . Alheri ko jin Abdurrahim yayi banza da ita ga kishin zaman shi da Na'ima da ke damunta sai cewa tayi"Shikenan ni ma yau-yau d'innan zan dawo nan gidan da zama, dan banyarda da zamanka da wannan yarinyar ba"Abdurrahim batare da yana mai ci gaba da danna wayar shi ya ce batare da ya kalli alheri ba" Amma dai kinsan ba ni da d'aki ko?"Sai muyi manage hakanan" cewar alheri. Abdurrahim shiru yayi yana tuna alherorin da alheri taimai ,hakan yasa yakasa hanata amma acikin zuciyar shi bayason zamanta gidan. Alheri ko bata saurari amsar Abdurrahim ba ta ce " Bari inje in kwaso abubuwan amfanina" Abdurrahim ko kai kawai ya iya d'agama alheri. Bayan fitar alheri ne Na'ima da ke nan tsaye har yanzu ta kalli Abdurraahim ta ce" Dan Allah in karage abinci ka taimakamin"dan zuwa lokacin Na'ima yunwa take ji sosai. Abdurrahim d'aga kai yayi ya kalleta ya ce "banrageba,amma ki je kitchen akwai komai sai ki had'a ko tea ne ma " Ai ban iya kunna abun da kuke girkin bane" Muje in gwada " Abdurrahim nuna ma Na'ima yayi yadda ake amfanin da duk kayan Wutan sannan yace mata duk lokacin da take da buk'atar abinci ta dafa duk abinda zata iyaci. godiya sosai Na'ima tayi mai amma bai tankamata ba yawuce abinsa. Kamar yadda alheri tace haka ko akayi dan duk wani Abu na amfaninta tadawo dashi gidan, d'akin dayazaman na Na'ima nan alheri takai kayanta ta jera, koda Na'ima taga haka gudun rigima kayan da Abdurrahim yabata Wanda alheri tasiyo kwaso kayan tayi daga d'akin duk da basu wani burgetaba dan duk k'ananun kaya ne sai dogayan ruguna guda uku sune ma masu dama-dama akayan,a falo Na'ima ta dawo da kayanta. Shiko Abdurrahim tun da yafita sai dare ya dawo gidan, dan juwan alheri gidan sai yaji abun duk ba dad'i. Ko da ya dawo a falon yaga Na'ima kwance, bece komai ba dan yasan alheri ce zatasata tadawo nan, ko inda alheri take be kallaba yawuce ciki abinsa, alheri tashi tayi tabi bayan shi har izuwa bedroom d'insa, kusa dashi ta zauna ta mai d'aura kanta akafad'ar shi ta ce"Abdurrahim kamar baka murna dawota kusa da kai ,Shine kazo koma ka kallan kai wucewarka ko? " Banlura da ke ba ne,amma meyasa kika kori yarinyar can ta koma falo bayan kuma ita kika iske awajan?"Alheri cikin jin haushin abin da Abdurrahim yace ta ce "Sabo da nafita iko da komai nagidan nan shiyasa , i swaer Abdurrahim indai kak'ara nunamin yarainyar nan kamar tafi matsayi awajanka ranar sai ta bar gidan nan ko kuma in b'atar da ita baki d'aya" Alheri na kawai nan ta tashi cijin jin zafi tabar wajan. Washegari ranar ne yakasan ce Abdurrahim zai koma wajan aiki, yanagama shirinsa yafito zai fita kenan ya iske alheri itama ta shirya zata fita, tare suka fita, Na'ima najin duk wani motsun su tashi ne kawai da batayi ba tana jin fitar su ta ta shi ta gyara gidan duk wani abu mai k'ura saida ta goge shi sannan ta d'ora makanta abin kari. Na'ima na nan zaune tana karyawa alheri ta shigo da kukan ta, ko inda Na'ima take bata kallaba tai gaba cikin mintina kad'an sai gata ta fito da jakar kayanta, kallanta Na'ima takeyi damamaki ba damar tambaya dan abun da take tunani Abdurrahim ne ya koreta agidan. Kamar yadda Abdurrahim yasaba dawowa haka yadawo, zaune ya iske Na'ima a falon yana zama wayar shi nayin ringing, da mamaki ya bi number da kallo ganin number k'anin shi ,cikin mamaki ya d'aga kiran damamki ya d'auka dan sunfi magana ta WhatsApp basu cika waya ba.Abdurrahim,da mamaki ya ce jin abin da mai Kiran wayar yace ya ce" Inzo in bud'e maka gida kuma" cikin rud'ewa da mamaki yayi maganar, kallan Na'ima yayi itama shi take kallo yace mata" k'aninane yazo yanzu yazanyi idan ya ganki kuma inajin zai dad'e betafi ba dan yadad'e yana son zuwa"Wani kiran ne yak'ara shigowa wayarshi da sauri ya tashi yafita Na'ma ta bi shi da kallo. "Kai broz ai na yi tunanin bazaka fito ba ne? " kai Abdurrahim ya d'an sosa alamun rashin gaskiya ya ce"Ina can inama k'anwarka fad'a batayi girki ba" k'anwata kuma?" Cewar Hafiz da mamaki.Abdurrahim cikin tabbatarwa ya ce "K'nwarka kuwa, ai nayi aure bada sanin ku ba,
🏠