iwan mara,gashi shima bai da ciwo sai ulcer amma bai san tanasa ciwan mara ba.
Alheri cikin muryar bacci ta ce"A'a gaskiya ulcer ba ta sa ciwan mara sai dai ko in lokacin period d'inta ne ya yi" Period" Abdurrahim ya mai-mai ta." Eh menstruation ba"Shiru Abdurrahim yayi sannan ya ce " Tom me ye maganin shi? " Tom ka ga dai yanzu dare yayi, amma first aid d'in da zaka ba idan akwai suga kasamata a tea dayawa tasha zai rage mata kafin safiya.
Yadda alheri tace ma Abdurrahim haka yayi, kitchen ya je ya d'aura mata tea d'in sannan ya zuba ma ta suga mai yawa a tea d'in kamar yadda alheri tace, bayan ya gama had'a mata tea d'in ya kai ma Na'ima yace"Ga tea d'in tashi ki sha "Tofa anzo wajan dan Na'ima intana ciwo bata son cin abinci.
"Wayyo cikina ni bazan iya sha ba "Cewar Na'ima."ke Wallahi biki'isa ba daga taimako ki zo ki zamanmin wahala ked'in banza, ina barcina kin tadani natashi na kuma had'amiki tea ance zai miki magani dan kin maidani wani sakarai ki ce min ba za ki sha ba, tom wallahi bazan iya ba yazam dole ki b'ar min gida"
Duk b'ab'atun nan da Abdurrahim ke yi Na'ima najin shi sai dai ahalin da take ciki ta ciwanta take yi dan Allah ne ka d'ai yasan yadda take ji.
Abdurrahim jin Na'ima shiru bata amshi tea d'in ba zuk'unnawa yayi kusa da ita ya jawota da k'arfi dan har sai da tayi 'yar k'ara hannunta ya rik'o ya dank'a mata kofin ahannu ya ce" Da Allah malama amshi ki sha" Na'ima cikin cije baki ta amshi kofin tea d'in ta d'aga ta shanye duka.
Abdurrahim kallan Na'ima yayi ya ce"Ki tashi ki je ki kwanta"Dan shi ji yake duk ta zamar mai wani kaya.
Na'ima tashi ta yi tana rik'e ciki ta k'arasa kan babbar katifar ta mai kamar gado wadda wasu ke Kira da gado huta.
Ahankali-ahankali Na'ima ta ji ciwan marar nalafamata ahaka har barci b'arawo ya kwashe ta.
Can b'angaran Abdurrahim ko yana ganin Na'ima ta tafi ya koma ya kwanta, yana kwanciya barci ya kwashe shi.
Washe gari Na'ima kasa tashi tayi dan tana jin kunyar Abdurrahim yaga halin da take ciki, dan zanin gadon yab'aci sosai da jini, sai dai Alhamdullh ta ji sauk'i sai dai ciwan da kanta yake mata kad'an-kad'an marar ko Allah ya taimake ta kwana d'aya take mata tana ciwo dama.
Kasan cewar Abdurrahim hutu yake na dakatar da shi aiki da akayi hakan yasa be tashi da wuri .Lokacin da ya tashi ko da ya fito daga d'akin shi kallan inda Na'ima take kwance yayi na 'yan seconds Kafin ya juya ya shiga kitchen ya had'a ma kan shi abin kari, bayan ya kammala Karin ne, yaciro wayar shi ya ci gaba da chart da friend's d'in shi.
Na'ima ko tarasa yadda zatayi ta tashi sabo da rigar ta duk tab'aci da jini,dama kuma idan menstruation d'in mutum ya zo ya sha tea ko kunu da suga da yawa haka yake zubar jini sosai.
Na'ima da tarasa yadda zatayi komawa tayi taci gaba da kwanciyarta tana nan kwance Abdurrahim har ya dawo ya shiga d'akin shi yayi wanka ya fito, da alama fita zai yi da Na'ima ta tabbatar in bata cire kunya ba taima Abdurrahim magana ya tafi batasan ya zata yi ba.Naima kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Ina kwana"Lafiya,ya jikin naki?"Abdurrahim ya fad'a ba tare da ya kalle ta ba."Na ji sauk'i dan Allah ka taimakamin da pants da always"Abdurrahim be amsa ma Na'ima ba yaci gaba da tafiyar shi gidan alheri ya je ya bata ATM card na shi ya ce"Ga shi ki siyo min kayan mata na sawa da duk wani abu da mace ke amfani da shi"Alheri kallan Abdurrahim tayi ta ce"Nasan yarinyar nan zaka sai mawa ta gidanka ko? "Kai Abdurrahim ya d'aga mata alamun eh, tun da na ke da kai baka tab'a min kara ba ka sai min wani abu, haka da birthday d'ina baka ban ko mai ba duk ban damu ba amma gaskiya yanzu na damu.
Alheri kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Abdurrahim ya ka ke da yarinyar nan,ka fad'amin gaskiya?"Bansanta ba na ce miki" Tom shikenan, bakasanta ba ka ce ko? "Alheri ta ce.
Kai Abdurrahim ya d'aga mata alamun eh, shikenan bari inje in suyo mata ka jirani ina zuwa.
Alheri bacin ta suyoma Na'ima duk wani abu daya kamata, takama hanyar zuwa gidan Abdurrahim, dan ace warta sai ta tanbayi yarinyar taji ta bakinta akan alk'arta da Abdurrahim d'in.
Na'ima ko tana ganin Abdurrahim ya fita ta tashi ta cire rigar da ke jikin ta ta d'akko ta Abdurrahim da ta tab'a sawa tasa inda ita duk atunanin ta ya tafi aiki ne.
Na'ima zaune take tana shan sauran tea d'in da yarage dakyar ma take shan tea d'in sabo da ya huce.
Alheri ko da ya ke tana da key d'in gidan Abdurrahim yasa tana zuwa ta bud'e ta shiga zaune ta iske Na'ima tana shan tea abin ta. "Keee alheri ta kira sunanta da gurb'atacciyar hausar ta ta ce"Wayasaka kasa wannan rigar? " Shiru Na'ima ta yi dan ba ta san amsar da zata ba ta ba.
Alheri jin Na'ima tayi shiru ta kuma cewa"Kai na ce ubanwa ya saka kasa wannan rigar? " Na'ima da duk ta gama daburcewa sai cewa tayi"Shima ya ganni da ita rannan bai ce ko mai ba kuma d...... " Marin da alheri ta wankama Na'ima ne ya hanata k'asara abin da tayi niyyar