NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 13 of 34

ari in aure ki tom k'ila sai in nayi aure, kinga ni kuma yanzu bantashi yin aure ba ma. " Fuuuu alheri ta d'auki jakar ta tab'ar gidan tsabar b'acin ran maganar da Abdurrahim ya fad'amata. Na'ima ko bacin ta ta shi daga baccin wahalar ciwan da taji tana tashi yunwa ma tace gatanan,Na'ima tashi tayi ahankali ta nufi falon. Zaune ta iske Abdurrahim da waya yana chart da mommyn sa Na'ima ta shigo falon kallo d'aya za kai mata zaka fahimci halinda take ciki na yunwa. Na'ima kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Ummm dan Allah bakarage abinci ba"tana rike da ciki take maganar, kitchen ya nuna mata da hannu alamun taje can akwai. Na'ima ko da taje kitchen d'in bataga komai ba, dan haka dawowa falon tayi dak'ar take magana sakamakon rikewar da cikinta yayi ta ce" Dan Allah ka tai makamin yunwa na ke ji zan mutuuuu... "Na'ima ta fad'i maganar da k'arfi sakamakon aman da takeji yana tasomata. Kallan ta Abdurrahim yayi sai yaji ta bashi tausayi dan shima yasan yadda ulcer take rike ma mutum ciki. Abdurrahim tashi yayi yaje kitchen d'in ya had'o mata tea mai kauri, inda yabarta azuk'unne anan yasame ta. Abdurrahim mik'amata tea d'in yayi tana sha cikinta ya k'ulle Abdurrahim duk yana nan zaune yana kallan Na'ima da dake juyi tana faman rike cikinta tana cewa "Dan Allah ka taimamin Wayyo cikina da marata " Abin da Na'ima bata fahimta ba ba wai cikin ne kad'ai ke mata ciwo ba hadda mararta lokacin period d'in ta yayi sai ya had'e da ciwan cikin' duk watan nuniya haka Na'ima keshan wuya. Cigaba da malele kuwa tayi agun dan ko tea d'in ma kad'an tasha. Abdurrahim da yarasa yadda zai yi da Na'ima alheri yakira amma wa yatta akashe. Abdurrahim kallan Na'ima kawai yake yamarasa taimakon da zai bata,magungunanshi na ulcer ya kwaso mata ya bata ya ce" Ki tashi ki sha ga magani nan" Na'ima ko kallanshi batayi ba tsabar azabar da take ji,jin yadda mararta ke mata yasa tafara tunanin abin da ke damunta. "Ki tashi kisha maganin" Abdurrahim ya sake mai-mai ta mata. Na'ima da ta fahimci abin da ke damunta cikin cije baki ta ce "Bazan sha ba ba cikina kemin ciwo ba ai. "Tom me ke mi ki zuwo? "cewar Abdurrahim. Na'ima kamar zatai kuka ta ce "Ni dai ka taimakamin"Abdurrahim da ranshi ya fara b'acewa cikin d'aga murya ya ce"Ke da'allacan da me zan taimake ki ,indai bazaki magana ba Wallahi zan rabu da ke ?" Na'ima sotake tacema Abdurrahim ya siyo mata panties da always da kuma maganin ciwan mara amma kuma tana jin kunyar fad'a mai " Abdurrahim da yaga bata da niyar magana tashi yayi yabatta agun. Na'ima har dare tana gun zaune takasa tashi kuma har yanzu bata da niyyar tashi dan ciwan yanzu ne ma yake cinta sosai. Na'ima jin azaba tayi azaba dan gaba d'aya tama rasa wana yanayi take jin yadda marar kaba d'aya ta k'ulle mata tashi tayi ta nufi d'akin da Abdurrahim yake,tana zuwa ta fara bubbuga k'ofar tana nishin wahala tana cewa............ 🛥️ ABDURRAHIM 🛥️ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.(RENEW) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚* Na Fadila Sani Bakori. Page 14 & 15 Na'ima jin azaba ta yi azaba dan gaba d'aya tama rasa wana yanayi take jin yadda marar gaba d'aya ta k'ulle mata ,tashi ta yi ta nufi d'akin da Abdurrahim yake.Tana zuwa ta fara bubbuga k'ofar tana nishin wahala tana cewa"Wayyo cikina ka taimakamin zan mutu Wayyo Allah na, haka Na'ima tai ta maimaitawa tana cikiga ba da bubbuga k'ofar, abin ne yayi mata yawa gaciwan cikin ulcer, ga kuma na mara na period. Abdurrahim cikin barci ya jiyo bugun k'ofar da Na'ima ke yi, tashi yayi da sauri ya fito daga d'akin kasan cewar be san jikin k'ofar Na'ima take ba da k'arfi ya tura k'ofar ya nayin shi kamar arud'e ya fito.Wata irin k'ara N'aima tayi dan ba kad'an ba k'ofar ta buge mata kai ba, dafe kan ta yi tana jijjuya yashi, wajan da alheri tasamata bandage ya famamata turo k'ofar da yayi da k'arfi. Da sauri Abdurrahim ya k'arasa inda Na'ima ta ke hannu d'aya dafe da kan d'aya kuma dafe da marar.Abdurrahim ya d'an da d'e atsaye yana kallan Na'ima sannan ya ce"Ke wai me ke damunki ne?". Na'ima tsabar azabar da kanta da marar ta kemata yasa ko amsa bata iya ba Abdurrahim. zuk'unnawa ya yi kusa da ita ya d'an ruk'ota kad'an kamar mai kyamar tab'ata ya ce"Yanzu me ke mi ki ciwo?"Na'ima kanta ta nuna ma Abdurrahim da mararta da ta k'ulle mata. Hannu Abdurrahim ya kai wajan kan na ta, zafi rau ya ji kan."Sai me kuma?" ya sake tambayar ta. Na'ima mararta ta sake nuna mai. Abdurrahim kallanta yayi ya ce "cikinki ke ciwo?". kai Na'ima ta girgiza mai alamun a'a, shiru ya yi sannan ya tashi daga zuk'unnan da yake kusa da ita, waya ya d'akko ya kira alheri ,cikin barci alheri ta ji wayarta na ringing, kamar karta d'auka ganin Abdurrahim be tab'a kiranta ba kamar wannan lokacin yasa ta d'auka. Abdurrahim naji alheri ta d'aga ya ce" Hello Alheri ulcer dama tana sa ciwan mara ne? "dan shi duk a tunin shi ulcer ce tasata c
🏠