NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 11 of 34

ya wuce kamar alheri. abotarsu ya sa Abdurrahim ko da lafiyar shi lau zai iya kiran Alheri tai mai wani abun ita kuma daga ya girata zatabar duk uzirinta taje. Sai dai ita alheri anata b'angaran so mai tsanani takema Abdurrahim, dan akwai lokacin da ta taba fada mai tana son shi, shi ko ce mata yayi iyayan shi bazasu bari ya auri christian ba.Wannan kenan haka dai sukaci gaba da ta rayya har izuwa yau Abdurrahim yak'i ba Alheri damar nuna mai kalar son da take mai,dan shi bata ita yake ba. Wannan kenan. Na'ima nagama mopping d'in kitchen d'in tazo ta wuce tagaban Abdurrahim, ba abinda yafi da mun Na' ima kamar zan manta ba d'ankwali agidan dan daga ita sai doguwar rigar dake jikin ta, kanta ba d'ankwali, d'ankwalin yacire ne alokacin da Abdurrahim yake ciku-cikun cire mata rigar ruwan da tasa,ga gashinta atsefe yake. Na'ima na nan zaune a d'akin da take , Abdurrahim yazo ya wuce ta ya shiga dakin shi, yunwa takeji sosai dan har cikinta yafara k'ugin yunwa , tashi tayi taje kitchen d'in bata ga ko mai ba Wanda zata sa acikinta gashi har wani yunk'urin amai takeji saboda yunwa, idonta ne ya haska mata wata leda da sauri ta k'arasa gurin ledar tana bud'ewa taci karo da farfesun kaza sai zuba uban k'amshi yake, zama Na'ima tagyara taci gaba da cin namanta. Shiko Abdurrahim wanka ya shiga yi yazo yaci ferfesun shi , sannan ya kalli wasan kwallo dan shi ma abocin kallon kwallo ne sosai, sai dai duk wasan kwallon da zai kalla bai zuwa ko ina ya kalla sai agidansa dan shi kamar mace yake daga dare yayi shikenan shida fita kuma sai gobe, ko dan ba mai abokai ba ne ohoho, bashi da k'awar da tawuce alheri dan har mommyn shima tasan da ita. Da saurin shi yafito cin namanshi dankarya huce, amma wazai gani, Na'ima zaune tana tand'e hannu dan har tagama cinye farfesun. kallanta Abdurrahim yake da mamki nuni yayi mata da hannu alamun ta zo, bamusu Na'ima taje dan talura bashi da mutunci inda yau kwanan ta biyu amma bai tab'a bata abinci ba saidai Wanda tagayarage take d'auka taci, so takema tace mai tana son taje gida amma takasa mai maganar, garashin kayan canzawa duk da dai tunda tazo ba tai wanka ba ne, dan ma farin mutum ba acika gane k'azantarshi ba ajiki. Zuk'unnawa Na'ima tayi nesa da shi. Abdurrahim yadad'e yana mata kallan wulak'anci abinda yake saurin tafasa Na'ima kenan tatsani kallan raini.Abdurrahim ko sai da ya gama mata kalllan raini acewarta sannan yace ahankali dan bawanima jin abinda yakecewa tayi ba" Ke wata irin bagidajiya ce, bakida hankali ne?, Abincin da nasa akaimin shine zaki zauna ki cinye min?" Abdurrahim harya k'ari maganarsa Na'ima batace komai ba, bare kuma tace yayi hakuri. Abdurrahim takaici ya isai daga tai mako. kallanta ya kuma yi ya ce " bargunnan " Na'ima yau gaba d'aya ita kanta kyankyamin kanta takeji so take tai wanka amma bata san kayan da zata Saba, inda bata da kaya, haka take wuni kullum ba d'ankwali akanta gashi yau har kwananta hud'u agidan bawanka, kai inda dai mutum min nan bada wuri yake da wowa ba mai zai hana inyi wanka da ganan in wanke rigata, tom wana zani zan d'aura? Take tambayar kanta, yauwa basai in d'akko rigassa ba wadda nake rufawa in benan inzanyi sallah insa kafin rigata ta bushe, yauwa aiko haka zanyi bari in rufe gidan kar inje yadawo, duk da rufe ni ya keyi tom nima bari in rufe ta ciki. " Rufe gidan Na'ima tayi, sannan ta dawo ta cire rigarta ta wanke ta sa ta Abdurrahim,sannan ta shiga wanka, tana cikin wankanne tarika jin buka k'ofa da k'arfi, bak'aramin razana Na'ima ta yi ba , dan tasan ba kowa bane sai mai gidan, kai aiko bazan bud'e ba inda rigata bata bushe ba, kuma inyaganni da rigassa korata zaiyi kuma bansan kowa ba, haka d'inma Nagoge masa taimakona da ya yi, saidai fatan Allah ya kawo yadda zan bar kasar" Shiko Abdurrahim wasu takaddun kayan da zasu d'auka ya manta yazo sauka gashi jiran shi akeyi, tunyana tunanin ko bacci takeyi harya bara tunanin anya lafiya, cigaba da buga k'ofar yayi amma ba alamun za abude. " Na'ima ko kasa k'arasa wankanma tayi saidai ta watsa ruwan kawai, koda ta tab'a rigarta kamarma yanzu ta shanyata, jin bugun k'ofar yayi yawa Na'ima ta yanke shawarar taje tace mai ta wanke kayanta ne tayi wanka, gudin kar yaji shiru ya koreta in ta bud'e kuma. Shawarar zuciyara tabi, cikin tsoro da addu'ar da duk tazo bakinta tak'arasa jikin k'ofar.Sai dai ko da taje kusa da k'ofar kasa magana tayi tarasa abinda zatace , ringing d'in wayar shi da taji ne yasa ta saurara danjin abinda zaice, ji tai yana cewa"Kayi hauri nad'an samu matsala ne agidan amma yanzu zan kawo in aha Allah. " Na'ima ko jin haka ta ce"Uhmm dan Allah ka basu hak'uri n...." Abdurrahim bai bari tak'arasa abinda take son cewa ba ya ya ce, "Keee,bud'e k'ofar mana"Ka yi hak'uri bazai yuwaba ne shiyasa. " Abdurrahim mamaki yasa yama kasa cewa komai,ga bak'incikin fad'an da ogan shi zai mai.Shi da gidanshi daga taimakon magidajiyar yarinyar nan tana n
🏠