NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 10 of 34

komawa tayi ta zauna duk da duk atsorace take agidan dan bata saba zama guri ita ka dai ba. Abdurrahim kamar yadda ya saba dawowa ya dawo gidan, har ga Allah ya manta da wata Na'ima sai da ya tun karo gidan ya tuna. Zaune take duk tata kure jikin ta, kallo d'aya za kai mata kagano atsorace take. Tanajin an bud'e k'ofa zumbur ta mike daga zaunan da take tana zare ido. Kallo d'aya Abdurrahim yayi mata ya dauke kan shi, kitchen yanufa dan haka d'abi'arshi take daga yadawo aiki bazaiyi komai ba har sai yasamar ma kanshi abinda zaici, dan shi bai iyacin abincin siye ba tsabar kyankyami irin nashi. Na'ima na nan zaune Abdurrahim ya fito ta ce "Bawan Allah dan Allah ina kasamoni tana mai maganane tana nuni da hannu kamar tana magana da kurma ,dan ita duk atunanin ta kurma ne. Wani banzan kallo Abdurrahim yayi mata ,tare da mamakin maganar da take mai da kurame. Banza yayi da ita ya shiga kitchen dan samarma kanshi abinda zai ci. Yana shiga kitchen d'in yaci karo da aman da Na'ima tayi mai aciki ,da ta rasa abin kwashewa tab'ar shi agun. Da sauri yadod'e hancinsa yadawo baya da sauri, kallanta yake rai abace ya ce" Kee, amma dai ke baki da hankali ko,kuma inajin asalinki talaka ce ke, dan su ke aikata rashin hankali irin wannan, kuma ke ko atalakar bagidajiyar talaka ce"Abdurrahim nuna Na'ima yayi da hannu yaci gaba da cewa, "wallahi nabaki minti d'aya ka cal ki goge min wan can k'azantar, sannan kuma ki zo ki bar min gidana yanzu-yanzun nan........ 🛥️ ABDURRAHIM🛥️ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.(RENEW) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚* Na Fadila Sani Bakori. Page 10 & 11 Wata uwar tsawa Abdurrahim yayi ma Na'ima ya ce"ba ki ji ne?, ki je ki goge min wannan k'azantar da ki kai min a kitchen, sannan kuma ki bar gidan nan yanzun nan." Na'ima ko tsabar al'ajabin maganar da Abdurrahim ya ke yi ce tasa takasa tashi, dan ita duk atunaninta Abdurrahim kurma ne. "Keeee!,wai ba ki ji ne"Abdurrahim ya sake nanatawa ganin Na'ima ta tsaya tana kallan shi. Da sauri Na'ima ta tashi ta shiga kitchen d'in amma still bata ga tsumman da zata goge aman ba, dawowa palon tayi tace cikin rawar muryar" Banga tsumma ba ne shi yasa tun d'azu ban goge ba"Banza Abdurrahim yayi da ita ya ciro wayar shi yayi Kira alheri. "Hello alheri ki zo yanzu please" bejira amsar ta ba ya kashe wayarshi. Cikin k'ank'anin lokaci alheri ta shigo gidan, kasan cewar tasan indai Abdurrahim yakirata ba lafiya ba, dan tasan baya kiranta hakanan kawai da wuya.Cikin damuwa dan ita duk atunanin ta ko be da lafiya ne, tak'arasa inda yake tsaye da waya yana dannawa. "Abdurrahim lafiya ka kirani ,gani nazo amma bakace min komai ba? " "Kitchen d'ina zaki d'anyi min mopping" Koda alheri ta shiga kitchen d'in taci karo da amai da sauri tayo baya dan adduniya ba abinda take kyama kamar amai, bata goge ba dan jikinta yabata ba aman Abdurrahim ba ne. Alheri kallan Abdurrahim ta yi da ta fito ta ce "Abdurrahim baka da lafiya ne naga amai a kitchen d'in ka? " " No, bani ba ne yarinyar nan ce. " Sai alokacin alheri ta tuno jiya Abdurrahim yakirata ta duba wata yarinya. Alheri kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Ita ce tai aman?" Kinga idan bazaki goge ba zaki iya tafiya. " Alheri juyawa tayi ta shiga d'akin da ta duba Na'ima jiya. Zaune ta iske ta ta tusa kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka. "Keee,tashi ki je ki goge k'azantar da ki kai ma muta ne" Na'ima d'agowa tayi tana kallan alheri,sannan ta ce " Dama babu tsumma ne shiyasa bangoge ba"Tom yanzu ansamu tsumman tashi ki je ki goge" "Na'ima yi tayi kamar bazata tashi ba dan idan akwai abinda tatsana bai wuce arika mata magana ba cikin isa. Na'ima tashi tayi tabi bayan alheri,suna shiga kitchen d'in alheri ta mik'a mata mopper d'in. Amsa Na'ima tayi tafara aikin gyra kitchen d'in. Cikin kankanin lokaci Na'ima ta goge shi tass dan bawai aman da tayi ba kawai ta goge sai da tabi lungu da sak'o ta goge, alheri duk tana tsaye tana kallanta, kiran da akai matane awaya yasa ta tafiya, Abdurrahim ta kalla tace zanje gida amma zan dawo" kai Abdurrahim ya girgiza mata alamun karta dawo, sanin halin shi da alheri tayi yasa bata wani jaba tatafi. Wacece alheri? . Alheri ainuhin sunanta kenan ,karatu ne ya kawo su zama London kasan cewar ita 'yar gata ce awajan babanta, primary da secondry d'inta duk a Nigeria ta yi su. Bayan ta gama secondary ne suka dawo London inda taci gaba da karatu, atak'aice dai yanzu haka tana aiki ne a wata private asibiti da ke k'asar. Alheri sun had'u da Abdurrahim ne sanadiyar ciwan ulcer ya kaishi kwanciya a asibitinsu, kasan cewar Abdurrahim baya son kwanciyar asibiti yasa ya naimi abashi wanda zai rik'a zuwa gida yana duba shi, shine fa doctor ya had'a Abdurrahim da Alheri, tom daga nan ne fa Alheri tazama likitan shi, ahankali-ahankali shakuwa tafara shiga tsakanin su,inda yakasan ce Abdurrahim bashi da aminin da
🏠