NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 9 of 42

ragowar duk an salwantar musu da rayuwarsu,idan ta haihu yaro baya cika shekara biyu yake mutuwa, wadan nan biyun ne Allah ya tseran mata da su wato Yarima Abbas da kuma gimbiya Jauhariya. Sai mata ta uku wato HAULE ita ma kamar SIYAMAN ce har ta fi Siya ma iya makirci da tuggu, matsalar ita bata taba haihuwa ba, don haka ta koma ta kama kafa da Siyama, saboda SIYAMA duk ta fi su dukiya, saboda danta ana ganin shi nemagajin Sarki duk wata dukiya da za a bayar kyauta ga gidan Sarauta idan ta wuce Sarki to shi ita ake bawa, ko a al'adance itace Shugaban gidan ta fuskar fifikon Sarki,ta fuskar siye duk wani wadda yake da ruwa da tsaki a cikin gidan biyayya take yi mata, haka duk wani da ke wajen gidan da yake da alhakin kawo ma'aikatan gidan Sarauta to shi ma bauta yake mata, saboda haka sai abin da ta ce a gidan ake yi. A lokacin tana zaune a kan hamshakiyar kujerar mulki ta cikin gidan Zuleha na gefanta a zaune barori da 'yan aikin gidan Sarki na zagaye da ita, wasu mata na can wata da'ira ana busa da gara garaya suna dan rausayawa, ta na zaune idon ta kyam akansu tana murmushi, wasu in sun shigo sai sun je sun yi mata kamar sujjada su kuma sumbaci kafafuwanta sannan su nemi wajen zama su zauna. A wannan Lokaci Hauletu na bangarenta ‘yar ta yar kimanin goma sha biyar na gefanta a zaune da barori waje da cikin daki suna masu jiran wata bukata a isar mata da shi, kaf cikin masu mata bature 241Page hidima Siyama ce ta kawo su, mace daya ce aminiya kuma 'yar uwa, wacce ita ce kadai amintacciya a wajenta wato HINDU. Da ita take duk wani sirrinta a gidan. Hauletu ta dubi 'yar ta "ZAHRA ta ce "Ki je daki ki kwanta za mu yi Magana da Hindu". Zahra ta dubi mahaifiyarta cikin girmamawa ta ce mike tsaye gami da jinjina wa "Na barki lafiya". Ita ma Haulet ta jinjina kai ta ce "Sai na shigo duba ki a turaka ki yi addu'a sosai ki kuma yi karatunki kafin ki kwanta". Zahra ta fara tafiya ta na zuwa bakin kofa wasu mata biyu masu yi mata hidima suka bi bayanta doguwar rig ace a jikinta an yi mata dinki da na kawa rigar jikinta har jan kasa take yi kamar Dawisu yana tafiya. Sai da ta fice aka mayar da kofa a ka rufe sannan Haulet ta dubi Hindu ta ce "Yake 'yar amana ta, me kika sani dangane da Kauyen Annur,shin kin taba zuwa ko kuma kina da labara, ko akwai wani da kika sani a kauyen". Da Hindu ta ji wannan batu sai ta yi shiru tana nazari cikin dan lokaci ta dago da kanta ta dubi uwargidanta cikin nuna kulawa sosai ta ce "Amincin Allah ya tabbata a gare ki, ‘yar malamai jikar malamai, jinin malamai matar hamshakin Sarkin duniya Muhammad farsi, ina da sani a game da kauyen Annur, har ma ina da alaka da Hakimi Abdullahi bin Sharjas, ya sanni farin sani, domin tawagarsa ce ta samo ni, ta kuma musuluntar dani, kafin ta kawo ni gidan Sarauta, saboda haka na koyi abubuwan da yawa a cikin kwanaki goma da nayi a gidansa kafin daga bisani a kawo mu nan". Haulet ta jinjina kai “Yayi kyau, na kuma godewa Allah da na samu haka daga gare ki, abin da yasa nay i tunanin tambayarki a game da birnin Kauyen Annur na taba ji kina maganar Kirkin matarsa Kubra, a lokacin da kike bawa Hindu labarin jarumtar bature 25 | Page kauyen, ban kuma ta shi bukatuwa da son sanin ba sai yanzu da wani dalili da ya ta so". Hindu ta yi sunkuyar da kai domin jin daga bakinn Haulet, jin shiru yasa ta ce "Ranki shi dade me kike nema daga gare ni, in sanar dake dangane daga Kauyen Annur”. Sarauniya Haulet ta yi shiru daga bisani ta ce "Wani abu ke dauremin kai yake kuma sani tunani game da rayuwar kauyen, gashi karamin kauye ne amma yadda kowane munafuki yake tsoron kauyen abin yana daure min kai, hatta Sarki akwai shakkar Annur a ransa akwai girmamawa ta musamman, a bangaren Sarauniya Zulehat kuwa bata da wani tashin hankalida ya wuce ta ji an am baci kauyen Annur, mahaifina in har ya zo wannan yankin to zai ce da ni zai je Kauyen Annur ban taba tambayarsa wani abu da ke faruwa a kauyen ba, sai yau na tashi da son jin labarin kauyen shi yasa kika ji na fara da tambayarki, shin me yasa duk mai mutumci yake girmama kauyen, me yasa duk munafuki yake shakkar Kauyen?" Hindu ta yi shiru tana dan murmushi tana tuna wasu abubuwa da suka faru a kauyen kafin ta dawo gidan Sarauta ta ce "Zama ne ya kama mu a gidan a lokacin muna matsayin bayi. A lokacin da muka isa Kauyen Annur a matsayinmu bayi mun taho cikin kaskanci da yunwa kishirwa da wahala, amma kallo daya Hakimi Abdullahi bin Sharjas yayi mana ya fuskanci damuwarmu a cikin Babbar Kasuwar Birnin nan. A lokacin ya kawo abinci da dabbobi daga kauyensa don siyarwa ya same mu a kasuwa a cikin wannan halin mu biyar ne. maganar farko da ya yiwa mafarautar mutane "Ku basu abinci da ruwa su sha, idan kuka kyautata musu za su yi daraja maimakon ku bar su suna cikin yunwa ga wahala". bature Daya daga cikin Dakarun ruwan sai ya ce "Ba z aka koya mana yadda muke sana'ar mu ba, idan sun yi maka ka siye su ka basu abincin da ruwa". Bai j
🏠