Waziri ya waiga gefe da gefansa ko zai ci karo da wani alamu
na gimbiya, ganin bai hango komai ba ya sa ya dawo da hankalinsa
ga Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya ce Ko ka ji labarin batan Yarima
Salman ko 'yar uwarsa Suhaila bin Ababakari, ‘ya'yan marigayi
Sarki Ababakari?"
Kowa da ke wajen sai yayi shiru har sai da Waziri ya
tabbatarwa zuciyarsa akwai Gimbiya Suhaila bin Ababakari a
hannunsu, sannan ya kara da cewa "Ya kai Hakimi ka yi sani cewa
Wannan Gimbiya Suhaila bin Ababakari da wannan yaro Salman
lallai masu laifi ne kuma ababen nema ruwa a jallo, don haka
matukar suna nan ka gaggauta bani su domin na kaisu Masarautar
Shamnun domin gujewa afkawa yaki tsakanin kasashen musulunci"*
Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya yi murmushi ya kara taku
biyu zuwa gaban Waziri Ja'afar ya kare masa kallo sannan ya ce
"Yaushe Bahara ta fara tsoron ‘ya'yanta da fada da darashin adalci,
yaushe karamar kasa kamar Shamnun ta samu karfin gwiwar gwada
bature
21 Page
kwanjinta ga Bahara, har yaushe Bahara ta samu rashin kuzarin da za
a aiwatar da wani abu a wannan yankin da take da mallakinsa batare
da ita ce ta shugabantar da shi ba? Ya kai Waziri ina tare da Gimbiya
Suhaila bin Ababakari a karkashin tsarona, amma bana tare da
Yarima Salman, sannan ka sani babu mace a cikin rikicin rigimar
mulkin domin haka zaka iya tafiya neman yarima Salman ka kuma
gurfanar da shi a gaban Sarki Muhammad farsin, amma Gimbiya
tana tare da iko na".
Waziri ja'afar ya jinjina lamarin a zuciyarsa, domin ya san
taurin kai irin na Annur gabaki dayansu wasu irin jajurtattun mutane
ne marasa tsoro don haka dole ne ya sake sabon shiri don tunkarar
daukar gimbiya Suhaila bin Ababakari daga gare su……..
Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya katse masa numfashi da
cewa “Oh na manta, wai ma Sarki ne ya turo ka ko kuma zuwan kan
ka ne?"
Waziri yayi shiru,domin ya san cewar Sarki ba shi da sani a
cikin wannan lamarin duk yadda zasu yi su boye kada ya sani sun yi,
tabbas ya cika matsawa a cikin lamarin nan ya san cewar Hakimi zai
jewa da Sarki maganar wadda haka kuma barazana ce ga Yarima
Hilal don haka ya ce "A matsayina na mataimakin Sarki aka wakilta
ni domin daidaita lamarin birnin Shamnun, na kuma amince da
yadda Sarki, burina na hada kawunan Yarima Hilal da Salman".
Hakimi Abdullahi bin Sharjas yadube shi yace "Amma me ya
kawo kafurai suka tsare Gimbiya Suhaila bin Ababakari? Ko su ma
suna cikin masu nemarwa musulmai zaman lafiya?"
A rude Waziri Ja'afar "A'a bani da masani ya akan haka?”
Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya ce "Me yasa baka nemi ta
yadda aka samo gimbiya ba? An samo ta ne daga hannun kafurai
suna kokarin shigar da ita birnin Bahara shin wajen ka za sukai ta
dama ko kuma wajen Sarki?"
bature
(1)
Waziri ya kara shiga rudu amma sai ya daure yayi murmushi
gami da shafa gemu “Mene ne alakata da Kafurai da su kama
gimbiya su kawo min ita, babu mamaki sun kwace ta ne a hannun
mutanen da suka taho da ita, lallai mun godewa Allah da ta dawo
hannun na gari ba ta fada hannun yahudu da nasara ba, ya kai
Abdullahi bin Sharjas na barka lafiya ka kula da gimbiya Suhaila bin
Ababakari"
Koda fadin haka sai ya juya cikin sauri masu bi masa baya
suka bi shi da baya. Hakimi murmushi yayi kawai ya dubi jama'arsa
ya ce Za mu yanke shawarar abin da ya dace bayan Sallar Magriba
**
Sarki Muhammad farsi mutum ne mai son addini da ci gaban
al'ummar sa, yana da son addinin musulunci kuma yana bawa
addinin gudunmawa da gasken gaske, ta waje daya ya samu tawaya,
auratayya, ya hadu da mata mara sa kishin musulunci, da ci gaban sa,
wannan dalilin ya haifar da yaduwar masu taimaka masa a bangaren
sarauta suka zamo munafukai masu son duniya da abin da yake
cikinta, duk da tsatson su musulunci amma sulallan Zinare ya mayar
da su bayi, ba masu yiwa kasa hidima ba masu yiwa matan Sarki
Hidima game da bukatunsu, wannan dalilin yasa birnin ya zama ba
shi da wata kariya duk kokari da yake yaken da Kakaninsa suka yi
don gujewa fadawa tarkon Yahudu da Nasara soyayyar matar tasa ya
girbe dukkanin wannan nasara sun shiga tarkon Yahudu da nasara
dumu dumu, ana aiwatar da abubuwa da dama a cikin gidansa bai
sani ba, ana aiwatar da abubuwa a kasa bai sani ba, za a zartar da
hukunci bisa saka hannunsa batare da ya san an yi hakan ba.
Ba kowa ce Ummul aba 'isin wannan barnar ba face matarsa
ta kuma Siyamal Ihud, Siyama kyakkyawa ce ta kwatantawa,
bunkasa gidan Sarauta da haihuwar tanjamemen Saurayi wadda Sarki
yake matukar kauna kasancewarsa babban dansa Yarima YAZID
bature
22 Page
23 Page
bayan shi tana da 'ya'ya uku dukkansu mata, sai matarsa ta biyu mai
suna HAULE ibn Abbas 'yar babban wani shehin Malami ce a
wadda yayi mamaya a dukkanin daulolin na musulunci wadda ya
samar da litattafan addini, kwararre ne kuma wajen ba da magani don
haka Likita ne kuma Malami ne, aboki ne ga tsohon Sarki Wato
Junaid babban Muhammad farsi. ZULEHA ibn Abbas tana da yara
biyu mace da Namiji ta haihuwarta biyar