NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 7 of 42

san ko su waye ba a cikin Bahara shi ne Allah ya hada mu da wannan Jarumi ya kubutar damu, amma suna yawan zantawa za su kai mu wajen waziri Ja'afar don gabatar da ni ga Sarki Nasir Su ka hada ido da Jarumi Umar ta yi masa kallon tambaya, ya sunkuyar da kai kasa yana sauraren abin da mahaifinsa zai ce matsalarsa dama dan uwansa Abdullahi da ya tuna hakan su ka yi ido biyu da shi a dai-dai lokacin shi ma Abdullahi kallonsa yake irin kallon tuhuma. Hakimi ya ce "Duniya bata samu ba, sai da jini ya zuba, addinin musulunci bai kafu ba sai da jini ya zuba, sulhu baya yiwuwa sai an zubar da jini, taimakon ‘wata kasar da wata baya tabbata sai an kwantar da wasu, ki saka a ranki ke ‘ya ce a gare ni kika taho neman tallafi na, maza Shame'u zo a shiga da su ciki, koda duniya zata 3 tunkare ni, ba zan bari a tafi dake ba, Allah ya kawo ki ne gare mu domin ya san za mu iya ji da duk wata bakar guguwa da zata mamaye duniya.. Jarumi Umar ya jinjina lamarin yana wani murmushin jin dadin tarba da mahaifinsa ya yiwa su Gimbiya. Hakimi ya dubi Jarumi Umar ya ce “Abin da ka yi yayi dai-dai ɗana”. bature 18 Page Ba haka Abdallahi ya so ji ba,domin a zatonsa za a yi wa Jarumi Umar fada kamar yadda wasu lokutan yake debo ta da zafi azo a yi masa fada musamman fada da arnan daji. SHEMA'U ta zo cikin sauri ta talbe su, ta yi cikin fara’a da murmushi daya daga cikin kannen Jarumi Umar kenan. "Hakimi ya kara da cewa "Kowa ya zauna cikin shiri domin komai zai ya faruwa daganan zuwa gobe za mu iya yin baki" daga nan matasa da sauran wadanda babu su a zaman majalisar Hakimi duk suka koma bakin aik, dattawa da Hakimi suka ci gaba da tattauna a game da harkokin mulki na yau da gobe Jarumi Umar dubi abokansa su hudu da suka saka shi a tsakiya Daddar ya ce "Eh ba mu labari umi Umar dube shi duban tuhuma y ace “Labarin me ke nan?" "KUBAIT ya yi muurmushi tsolaya yace "Ka da ka yi mana rowa mana, na ga fa yadda kake kallon gimbiya, ita ma na ga yadda take kallon ka❞ Duk su hudu suka kwashe da dariya shi kuma ya hade rai "Wai me kuke nufi ne?" Kubait ya tsaya da dariya ya ce "Mafaraucin dabba ne yau yayo farautar mutum, shin akwai wadda ya isa ya kwace masa abin farautarsa”. Su duka suka kara kwashe da dariya Jarumi Umar ya kara hade rai "In kun gama nishadinku ku ne me ni, babu ni a cikin* wannan gayyar". SAKLAHUL ya ce "Ita fa ba kamar Jaruma bace, ko wani, dutse mai nauyin gaske da za a nuna mata mazantaka, idan ka tafi ma za ka dawo kana ba mu labarin, eh ita zuciya ba komai take iya jurewa ba, domin wani abin gubace sai an fesar ake samun sukuni”. 19 Page "Idan ku kun kuna da sararin da za ku na barin zuciyarku da duk wani abu da bai shafi tafarkin Allah da ma'aiki ba,ni ba ni da shi". “Tafarki da sunnar ma'aiki duk suna daga cikin abin da muke maka fatan kasancewa tare" MU"AZ yay i furucin duk suka kwashe da dariya har yayi nisa yana jin su. Wani tsaki ya kara yi a ransa ya ce “Shashashe, ko me suka ga ni har ya sa suke zargin na kamu da so". ** A nan take Waziri suka hau hanya don zuwa Kauyen ANnur wadda anan ne za su ji su tabbatar da inda su Gimbiya suke a hanyar ne Jarfis ya radawa Sarkal rada cikin hikima yadda babu wadda ya ji abin da ya sanar da shi ya ce “Lallai zabi wani a cikin mutanen mu, ka je ka labartawa Jagora Philiphis halin da a ke ciki domin ya san shirin da zai yi." "An gama ya shugaba na" Sarkal ya sulele a hankali ya je ya sanar da wani daga cikin dakarunsa sakon da Philiphs ya sanar da shi, ba tare da bata lokaci ba Mahayin ya sulele a dokinsa ya nufi wata hanya. Tun da suka fito daga babbar birni ba su kara yada zango ba sai a cikin kauyen Annur. A dai-dai lokacin da Hakimi zai shiga cikin gidansa sai ga tawagar Waziri nan cikin sauri sauri sun iso bakin fadar Hakimi". Koda Hakimi da sauran yan fadar da basu tafi ba suna niyar tafiya suka ga Waziri a halin sauri sai suka dakata domin za su iya tafiya Hakimi ya sa a kirawo su su dawo saboda ganin Waziri sau tari babu alkairi a ciki ziyararsa. Kowa dake wajen ya duka ya gaida Waziri amma banda Hakimi Abdullahi bin SHarjas, kamar yadda ya saba a kowane lokaci bature 9 20 Page matukar ba fadar wani ya je ba ba zai zube yayi maka gaisuwa irinta sarauta ba sai dai za ku gaisa kamar yadda shari'ar Allah ta ala ta tanadar. Waziri ba yau kadai ya san da wannan rashin girmamawa da Hakimi Annur yake yi masa, duk kuma yadda zai yi yayi domin a kwace hakimanci daga hannun Abdullahi bin Sharjas abawa dan uwansa SHAMSU BIN AUJAR amma sarki ya nemi dalili, ganin dalilin rashin girmamawa ba zai sa Sarki ya sa a sauke Hakima domin ko shi da kansa Hakimi baya masa gaisuwa da ta dace suna rayuwa ne tare kamar da da mahaifi, kuma Sarki bai taba jin wani abu a game da haka domin yana girmamawa Hakimi Abdullahi bin SHarjas. Bayan kowa ya nutsu Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya ce “Lafiya muka ganka da yammaci likis haka ya Waziri Birnin Bahara Allah ta Allah yasa dai lafiya".
🏠