NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 6 of 42

aike zai iya zuwa ya sanar damu cewar an kai ta masaukin da ka tanada don kai ta can". Waziri Ja'afar ya jinjina kai ya ce "Za mu ga ni, sauraro". kuma muna Har Jarfis ya bude baki zai yi Magana sai daya daga cikin yaron Kirzalu yayi sallama tare da cewa "Akwai bako daga Kiristoci ya kara so". Koda jin haka sai Waziri Ja'ffar ya dubi Jarfis ba tare da yace da shi komai ba. Jarfis y ace "Babu shakka 'yan sako sun iso don haka ya shigo ya gabatar da bayani a gaban Waziri Ja'afar". Jim kadan bako ya shigo cikin dakin yayi gaisu wa da Jarfis tun da Jarfis ya ga jikinsa duk rauni hannunsa na dama sai digar då jini yake sai ya zabura ya ce "Ya kai Sarkal, mene ne yake faruwa na ganka a haka ka tabbata kun iso da Gimbiya kun kaita inda aka Umarce ku?" Sarkal ya sunkuyar da kai kasa cikin nadama game da cewa "Ya shugabana ka dauki rayuwata domin ba ta da wani amfani a gare ka, mun yi rashin nasara gabatar da Gimbiya zuwa inda aka Umarce mu". bature 15 Page Har Jarfis ya zare takobi zai sare masa kai sai Waziri Ja'afar ya daka tsawa gami da cewa "Ni nake yanke hukunci a nan, saboda haka ni ne zan dauki mataki a kan ka da kuma dan sakon ka". Koda ya dakatar da Jarfis sai ya tako sannu a hankali zuwa ga Sarkal "Kisan ka ba shi da wani amfani a gare mu face bata kaifi takobi da bata waje, amfani daya ya rage maka a gare mu yanzu shi ne "A ina kuka yi shashancin sakaci da gimbiya?" Sarkal ya duka har kasa ya ce "Waziri nayi iya bakin kokari na na ganin na cika aikina kamar yadda na faro shi, amma na gaza a daidai madakatar Annur, inda wani Jarumi guda daya tal kamar shaidani ya baiyana a gare mu, duk ya bazar da yara na suna can cikin halin mutuwa ko rayuwa, dakyar na iya rarrafowa na kawo kai na nan domin na sanar da ku halin da ake ciki". Waziri ya jinjina kai game da cewa "Mutum daya kace kuma dai dai mararrabar Annur. To me ya hada ku da shi a wane dalili?”. Duk yadda ta faru Sarkal yay i bayani Waziri ya tafi nazari a ransa yana tunanin waye wannan mutum daya, ko ma waye zai kasance daga cikin jaruman Hakimi Abdullahi bin SHarjas. Koda gama wannan tunanin sai ya dubi Kirzalu y ace "Maza ka basu rawani da alkyabba mu isa Annur kafin faduwar rana, domin matukar ba mu tafi da Gimbiya ba Hakimi Abdullahi bin Sharjas zai yi wani abu maza ku shirya. ** Fadar Hakimi Abdullahi bin SHarjasl cike da jama'ar ana shirin bada umarni abi sahun Jarumi Jarumi Umar bayan da yayansa Abdullahi ya bi shi tare da dakaru goma. Ana wannan zaman ne sai ga Jarumi Abdallahi da mutum goma da ya tafi da su, gaba gare su ga Jarumi Umar nan da Gimbiya a bisa dawakai sun nufo kofar gidan Hakimi Abdullahi bin Sharjas. Kowa da ke wajen suka zuba wa bature 16 Page Jarumi Jarumi Umar da baki ido har suka iso bakin fada a inda Hakimi Abdullahi bin Sharjas ke zaune a bisa kujera ga dattawan gari suna zaune. Jarumi Umar Bin Abdullahi bin SHarjas ya karaso fuskarsa cike da annuri ya iso wajen mahaifinsa ya fadi yayi gaisuwa gami da yin gaisuwa ga dattijan majalisa suka amsa masa. Bayan Abdallah ya sauko daga dokinsa ya zo kusa da dan uwansa sai ya dubi Jarumi Umar ya ce "Ya mai girma Mun fita hanya don zuwa kaiwa Jarumi Umar dauki kamar yadda ka umarce mu,sai muka gan shi ya taho tare da wadan nan matan guda biyu, bai yi mana wani bayani ba, mu ka biyo bayansa har zuwa gida". Guri ya kara shiru mutane suka mayar da hankalinsu ga Gimbiya da abokiyar tafiyarta. Hakimin wato Abdullahi bin Sharjas Annur wato mahaifi ga Jarumi Umar ya kalle shi cikin alamun son Karin bayani Jarumi Umar ya gyara murya y ace “Ba wani abu da na sani dangane da su Baba, abin da nasani shi ne na kwace su daga Annabi hannun Kafirai ma'abota kaucewa daga koyarwa Muhammad farsi, sun so na bar su su ci gaba da tafiya a cewarsu zamowarsu a nan zai haifar mana da barazana gami da farmakin abokan gabarsu" Daga nan bai kara cewa komai ba. Hakimi ya dubi Gimbiya da suke tsaye suna neman izini. Ya jinjina kai ya ce ‘Yata matso kusa". Gimbiya na jin haka sai ta jinjina kai alamar amanna sannan ta taho ga tsoho Abdullahi bin Sharjas ta duka ta kai gaisuwa "Yata, wace ce ke, daga ina kike?" Gimbiya ta ce "Ranka ya dade Suna na SUHAILA BIN ABABAKARI, ni 'ya ce ga Sarki Abubakari wadda yake mulki a kasar Shamnun,an kamo ni ne a lokacin da nake kokarin tsarewa daga masarautar mu domin gujewa ballewar rikicin sarauta, wadda bature 17 Page tun daga mutuwar mahaifinmu magauta suke ta kokarin ganin sun hana kasar zaman lafiya, har yayan mu Yarima SALMAN ya gudu daga kasar saboda farautar rayuwarsa da ake yi, saboda da yawa a cikin kasar Yarima HALIL ne ya siye su don zama magajin mahaifin mu, yayana Yarima Salman ya turo min sako na gudu a cikin dare saboda matukar ya hau kan karagar mulki duk wasu ‘ya'yan mahaifiyarmu sai ya kashe su, mummunan kisa, wannan shi ne abin da ya baro ni daga kasar mu, sai kuma aka kamamu, aka kuma danka mu a hannun wadan nan kafuran za su danka mu wani hannu da ba mu
🏠